TUN KAFIN AURE Page 21 to 30

******************
Ba wata kwalliyar kirki tayi ba don ma yayarta Hadiza ta matsa mata ne. A falon gidan Baffa yace su zauna yadda mutane zasu rinka wucewa. Hafsi murmushi tayi daya fadi haka lallai laifi Allah kadai ke yafewa duka amma mutane abu kadan sai yasa su tuna baya. Tun kafin ta daga labulen falon gabanta ke faduwa wanda ta rasa dalilin hakan. Da wannan muryartata mai kamar shagwaba tace Assalamu alaikum. kamar a dauke masa wutar jikinsa Junaid me cika idon yan bariki ya kasa amsa mata. Ido kawai ya bita dashi…..you are so beautiful,so pretty. Kin shigowa tayi ganin yadda ya rude saboda ganinta. Tsoronta daya kada ta shigo ya nemi taba ta. Karaso mana Hafsi ko….ya fada yana daga gira daya. Sunkuyar da kanta tayi kasa baka amsa min sallama ba ai. Dan bata fuska yayi ke da gidanku. Anyway wa alaikum salam. Tana zama ya tashi daga inda yake ya dawo kujerar kusa da ita. Wallahi kin hadu sosai ma kuwa. Can’t wait to have you. Gabanta taji ya fadi anya wanan ne Baffa ya aminci ta aura. sai ma a lokacin ta kare masa kallo. Don kyau dai yana da shi amma wani gashi ta gani ya danyi tsini daga tsakiyar kansa ga wani wando me fadi irin wanda black americans na ghetto suke sawa. Rigar jikinsa kuwa itama me fadin ce ta dan sauko masa. Nan take taji ta tsane shi bare da ta kalli wani kwantareren takalminsa. Yanzu fa sai ace duk kayan nan masu tsada ne ko ta fada a zuci.
Ganin yadda take kare masa kallo yasa yayi shiru shima yana dada kallonta. Can daya ji shirun yayi yawa yace yah nayi miki ko? Firgigit ta kalle shi bata fahimci zancen sosai ba kawai sai tace masa a’a. Ya zaro ido me kika ce? Kinsan yadda mata ke rububina kuwa? Ganin ya dauki wata hanyar sai ta katseshi da gaisuwa. Bayan yan mintuna tace zata shiga gida.
Batul Mamman????
TUN KAFIN AURE????20
Ke kada ki raina min hankali mana. Ya daga zuwana zaki ce wani zaki shiga gida. Ya kara kankance ido irin na ‘yan duniya ko kina son nayi miki irin abinda wanan matsiyacin yayi miki ne a wadannan pictures din? Gyara zama tayi tana kallonshi. Kaddai ace a hotunansu da Saif ya ganta. Tasan ance a hoto ya ganta amma bata da details din abinda ya faru. Da kyar tace wane hoton kake nufi ne. Wata babbar waya da bata taba gani ba ya dauko ya nuna mata hotunan. Gabanta ne ya fadi a tsorace ta mike wallahi ni ba yar iska bace idan ma abinda ya kawo ka kenan. It was my first and it will be my last in sha Allah. Tafi ya rinka yi tana magana eyye! eyye yarinyar ta iya turanci ashe. Kunya taji ta kamata shi kuwa ya cigaba da magana. Kar ki damu fa Juni has done worst amma tunda naga babanki yana pretending kamar ke saint ce ba komai shiyasa ma zan aure ki. Daga nan har muyi aure zanyi kokarin dena kula wasu matan sai ki dage ki koyi jan hankalina. Da wuya ake impressing din Juni. Yana gama magana ya tashi ya good night Hafsi Hafsi. Daga bakin kofa yayi blowing mata kiss. Sai da ya fita taja wani numfashi. Lallai akwai matsala ina ita ina wannan mai zubin ‘yan iskan.
*********************
Fuska ba annuri ya shigar mata daki ba ko sallama. Junaidu abin ya motsa ne ka shigo min daki kai tsaye. Dafe kai yayi oh sorry Hajiyata raina ne a bace. Dan murmushi tayi tana nuna masa wurin zama. Zo nan dan Hajiya bani labarin yadda kuka yi da Hafsa. Kara zumburu baki yayi wai don rainin hankali baki ga yadda take min wani irin kallo ba. Hajiyan dangi dariya tayi ya bita da ido me kuma ya faru kike min dariya? Yo dannan banda abinka ji irin shigar da kayi kamar wani tsohon dan tasha. Duk kayan jikinka sunyi maka yawa. Lah Hajiya gayun kenan fa. Black americans hadaddu ai irin shigar nan suke irinsu ice cube, snoop dog, kanye west da….kafin ya kara magana ta daga masa hannu dakata haka. Yanzu don Allah zaka iya kawo min sunayen Annabawa ko Sahabbai goma? Ka rasa wanda zakayi koyi dashi sai makiyan musulunci? Kaji tsoron Allah Junaidu ka gyara rayuwarka. Yanzu dubi wani gashi a kanka kamar juji kuma nasan kana sane ka tara shi. Kana girma kana kara cin kasa. Bakin nan na Junaid kam yayi tsine saboda yadda yake zumburo shi..dan me zaayi masa fada. Sai dai kuma maganar ta dan shige shi. Ya mike zai fita daga dakin Hajiya kiyi hakuri da yardar Allah zaki ga na zama salihin mutum ko, yanzu ma ai kinsan Juni yayi sanyi. Filo ta jefe shi dashi ya gudu don yasan ta tsani Junin nan da ake kiransa.
*******************
To baiwar ciki ina nan ina ta nema miki mafita wurin Juni ke banda ci babu abinda kika iya. Tilly ta hadiye naman da ke bakinta da kyar kin dai sanni tun farkon haduwarmu ina da son abinci musamman idan akwai nama. Rosie ta bata fuska to naji mayya amshi ki karanta wannan. Dafe kirji Tilly tayi me zan gani haka? Aure zaiyi, ai wallahi uban kuturu yayi kadan. Ni fa banda kudinsa shima kansa ina so. Wata takardar Rosie ta mika mata tace to wanan kuma fa. Ci…ci…ci me? Mun shiga uku Rosie ya akayi kika bari ciki ya shige. Rosie ta dakatar da ita tsaya kiji ai cikin nan shine license dinki for now. Ke dai ki saurare ni da kyau kinsan tunda muke bamu taba yin babban kamu irin haka ba dole mu rike wuta.
****************
Nafisa da Hamida sai shirye shirye suke dan uwansu zaiyi aure. Kashe kudi suke kamar babu talauci a nigeria har sai da mommy tayi magana. An hada lefe na gani na fada a cikin gidan daga baya Senator ya yi musu gine mai kyau babu abinda bai saka ba yace a nan zasu zauna har sai yaga kamun ludayin zaman nasu don bai gama yarda da dan nasa ba.
A kano ma su maman Hafsi suna nasu shirin duk da sun san Senator Rufai da iyalinsa ba tsaransu bane amma dai suna gudun gori ace sikau suka kai yarsu.
Ranar karbar lefe tazo dai dai da sati daya kafin biki Hafsi bata sake ganin Junaid ba shima bai neme ta ba don yasan ta kusa shiga hannunsa wannan yatsine yatsinen da take masa dole ta ajiye a gefe.
Batul Mamman????
TUN KAFIN AURE???? 21
Yan uwa da abokan arziki sun cika gidan. Yan ganin kwal uwar daka ma suna nan zaune suga irin abinda zaa kawo wa Hafsi.
Akwatuna ne ake ta shigowa dasu gidan har goma sha takwas. Hajiyan Dangi ita ce tayi jagora ta nuna musu kayan. Akwati set biyu guda sha biyu na amarya ne komai na ciki me tsada ne harda set din gwal uku. Sai daya na baffa, na Mama, na ‘yan uwanta sai kuma wanda zaa bawa yan uwa da abokan arziki. Dukkansu shake suke da kaya. Ga kudin dinki dubu dari biyu. Wai a haka ma don kada su zake da yawa ne. Ranar bakunan mata sunyi magana har sun gaji kowa da abinda take fada. Mama dai dubu hamsin baffa ya bata na tukwici shima don su fita kunya ne. Wata yayarsa ta kira ta fadawa tare da dora nata dubu goma. Yayar da yake tana da dan rufin asiri ta kawo talatin itama Hadiza ta kawo goma suka cike dari. Hajiyan dangi mace mai kwarjini da kamala tace ko kwandala ba zasu karba ba yar da aka basu ma sun gode. Suna fita aka hau bude buden akwatuna ana kallon yadda ake wasa da kudi a kasar mu.
*******************
Hafsi tasha gyaran jiki sai sheki take ga lalle wanda mai lallen ma Hamida ce ta turo ta har gidansu. Ummati tace Allah Yasa kuyi zaman lafiya naga kamar basu da raina mutane. Haka akayi kamu a wani makeken filin senator wuri ya dauki mutane. Idan kaga Hafsi kamar wata yar tsana saboda mai kwalliyar ma tafiyayya ce. Tayi kyau har ta gaji. Su ummati ma da kannenta baa barsu a baya ba. Itama Batul Mamman sai wani shishshige musu take taga kudi.