TUN KAFIN AURE Page 21 to 30

Ranar dinner wasu kaya da mama ta kure basira ta dinka Hafsi ta saka. Ummati tana zuge mata zip din rigar Hamida ta shigo da wata riga da skirt na lace ne ko material gashi nan dai abin mai daukar ido golden brown. Tunda aka fara biki ta likewa su ummati sun zama kamar kawaye. Kayan hade suke da takalma da head and veil. Hafsi ta bata rai ni fa wanan zan saka mama ce ta dinka min. Hamida ta marairaice haba matar yaya anko yake son kuyi da kansa ya bayar aka dinka miki. Suka shiga ban baki ita da Ummati amma sam Hafsi taki yarda har zancen yakai kunnen mama. Nan tayi musu sulhu gobe idan zaa kaiki sai kisa nawan zan ga mai hanaki amma yau dai ki saka na angonki. Maman ummati tayi dariya to yar shagwabar Mama gobe dai zanzo da bokitin share hawaye.
Taro yayi taro wuri ya cika da mutanen da suka amsa sunansu a naija. Yan mata anyi dinkunan rashin mutumci suna tafiya kamar sanduna babu lullubi. Matan aure sai hura hanci wai kar a raina su. A mota aka tsayar da hafsi har Junaid ya iso. Ko da ya fito da shaddarsa golden brown bata gane shi ba. Duk da yasa hula ta kula yayi aski, ya gyara fuska gaba daya ya canja. Shima kallonta kawai yake har ya karaso. A kunnenta ya rada mata ni kada ki cinye ne da kallo, it has been three weeks, kin kara kyau kema. Cak ta tsaya saboda yadda yayi kusa da ita. Ana fara musu alamar su shigo cikin hall din taji yana kokarin kama mata hannu. Kokarin fizgewa tayi shi kuwa ya matse hannun ga zobba a hannun har ta fara jin zafi. A hankali tace kaci bashi wallahi. Ya sassauta rikon suka shiga.
Dinner tayi kyau kuma ko liki baayi ba wannan kuma dokar Hajiyan dangi ce. Tilly da aminiyarta Rosie ma sun sami shiga a wurin daukar hoto Junaid ya gansu. Tsoro ne ya kamashi ya hau adduar kada tayi masa wani haukan a wurin don bai ma tsaya tunanin yadda suka sami katin shiga ba. Bayan sun dau hoto ta bashi wani envelop congrats Juni boy. Hafsi ta dan kalle ta Tilly tace amarya mun dai rigaki lasar zumar muna fata tayi miki dadi yadda….junaid ne ya katse ta get out…ba musu ta kama kawarta suka fita don idanunsa sunyi jazur tasan halinsa sarai. Babu wanda ya kula sai Hafsi kowa na shaanisa.
Dreba ne a gaba sai Ummati baya kuma Junaid da Hafsi don ya nace shi zai mayar da ita gida. Tayi kokarin daurewa ta kasa can kasa kasa tace wace wannan matar ne. Dama ransa ya gama baci gashi yana son dena shaye shaye babu ko taba a aljihunsa ya harareta idan zaki bude baki kiyi magana ki bude sai wani kasa kasa kike da murya kamar wata mumina. Ummati ta juyu don taji me yace…zare mata ido yayi ke bana son gulma me kike kallo. Ba shiri ta juyar da kanta. Tooooh wannan ne mijin da Hafsi zata zauna dashi. Hafsi dai shiru tayi tana kallon fuskarsa. Sai tayi da gaske akan wannan mutumin. Abu daya ta sani dai da yana cikin farin ciki kafin yaga wannan matar. Babu ko sallama suna zuwa gida suka fita yace da dreba yaja motar su tafi.
Daki ya shiga hankalinsa a tashe yana tarrabin abinda ke cikin takardar da Tilly ta bashi.
Juni boy
Nasan kana cikin farin cikin auren da zakayi gobe nima ina taya ka murna. Sai dai ina me tabbatar maka gobe zanzo Abuja a tawagar amarya. Ga wedding gift nan.
Luv Tilly
Bude daya takardar yayi gumi ya karyo masa ganin reult ne dake tabbatar da Tilly na da ciki har wata uku.
Batul Mamman????
TUN KAFIN AURE???? 22
Ko kayan jikinsa bai canja ba ya fita zuwa hotel din da abokinsa Imran yayi masauki. A waje ya tsaya yayi masa waya. Sai a karo na uku ya dauka ya sanar dashi yana wurin parking ya fito.
Suna hada ido Imi yace yace ya mutumin you sounded worried fa. Me ya faru ne? Envelop din Junaid ya mika masa. Imi ya rinka dariya bayan ya karanta harda hawaye a idonsa. Can ya daki kafadar junaid…haba mutumina kada ka bada ni mana. Yanzu har akwai wata chick da zata ce kayi mata ciki ka yarda? Matan nan fa sun fi mu tsoron faruwar hakan tunda su ke da wahala. Wani abin kawai take so. Fuskar Junaid babu sauran kwanciyar hankali uhm uhm Imi aure fa zanyi kuma Allah Ya sani ina son yarinyar ina kuma son gyara rayuwata. Kaima Allah Ya baka tagari. Kayya yaro gigin soyayya ke dibanka bari romon ya kare zaka neme ni ne. Bayan ina kallo dazu amaryar taka ta murguda maka baki. Kansa ya shafa yana dariya da irin tsokanar fada ne yaga tana kulashi shiyasa yake mata haka a fili yace Kai kam kamar ana kada maka gangar shaidanu..ya ina cewa zan shiryu kana min mugun baki. To yi hakuri na Hafsa Imi ya fada yana dariya…yanzu dai ka manta da wannan yarinyar kada ma ka sata a rai. Idan ta sake nemanka kaci ubanta da kyau wallahi zata kyaleka. Kada ma ka fara bata kudi don sai tayi blackmailing dinka. Nan suka yi ta shawara sai wurin ukun dare Junaid ya koma gida.
******************
Bacci sam yaki zuwa idanun Hafsi sai tunani take kala kala. Wannan Junaid din dabiunsa na bata tsoro( wai ma don ya rage!) Gashi haka hankalinta bai kwanta da matar da ta bashi envelop ba. Maganar Tilly duk ta tsaya mata a rai wai sun rigata lasar zumar…..ehew abin kyankyami ma zancen ta fada a fili tana yamutsa fuska. Anya ba yan is…sai tayi shiru zargi babu kyau don haka mafitar ta daya shine ta mike ta dauro alwala ta tayar da sallah. Haka tayi ta nafila har asuba tana addua sannan ta yi bacci.
Sai wuraren goma na safe ta farka. Shima Hadiza ce ta tasheta da dundu…to kasa ana shirin fita daurin aure kina kwance kina bacci hankali kwance. Mutssika idanu tayi ta mike…ina ummati ta tafi Yaya? Debo miki ruwan zafi kiyi wanka. Kinsan dai baffa yace karfe biyu zaa bar kano so kiyi da jiki kafin a dawo daga daurin aure. Ta kalli agogon wayarta…Allah sarki nan da mintuna arbain da bakwai kin zama matar aure. Cikinta taji yace kulululu da gaske abin yazo. Kuka tasa wa Hadiza inama basuyi wadannan hotunan ba tun kafin aure da yanzu Saif ta aura. Ummati ta ajiye bokitin hannunta ki gode Allah baa daura dashi ba don yadda aka ce Junaid yayi bayan yaga hotonki da kila a gidan auren zai biyo ki ko ma ya kashe auren. Hadiza tace kyale ta ummati ai tasan wani baya auren matar da ba tasa ba.
Kayan da mama ta dinka da aka hanata sawa daren jiya su tasa ai kuwa tayi kyau sosai. Katon mayafi ta yafa ga kamshi ko ta ina.
Taro yayi taro don manyan mutane na kusa da nesa sunzo bikin dan manya. Junaid yasha cream shadda harda babbar riga da brown din takalmi da hula maroka suna ta sanaar su. Daga karshe dai Liman ya daura auren Junaid Rufai Bukar da Hafsa Aminu Garba.
Mijin Hadiza ne ya bugu ya sanar da ita an daura auren kan sadaki dubu dari gida ya cika da guda da hayaniya. Wata ‘yar makarantarsu tace gaskiya Hafsa Aminu kinyi saa muma Allah Yasa mu a danshinku. Yan Amin kuwa suka amsa.
Ansha koke koke lokacin dasu Hajiyan dangi suka zo daukar amarya. Mama kasa daurewa tayi ta kulle kanta a daki. Baffa ma yana mata nasiha yana sharar kwalla. Bai taba tunanin zata yi auren nesa ba, aure ma irin na gidan Senator Rufai Bukar. Motoci har wajen layinsu Hafsi. Cikin motocin kuwa harda wadda Rosie da Tilly suka dauko haya suka bi ayarin kai amarya. Don karfin hali har mutane uku suka dauka aka dauki hanyar abuja.
Batul Mamman????