TUN KAFIN AURE Page 41 to 50 (The End)

Dakinsa ya shiga ya lalube duk wuraren ajiyarsa ya dauko kudi masu yawa. Yana zuwa wurin parking yaga convoy din Alhajinsu dole ya tsaya suka gaisa zai fita. Senator Rufai bai nuna damuwa ba yace Junaid kafin ka tafi ina son ganinka. Tsaki yayi wanda har uban yaji sautinsa. Tilly ta kira shi ya kai sau ashirin kada yaje taki binsa ko yau ta hana shi kusantar ta.
Duk yadda take kokarin boyewa kana ganin Hafsi kasan bata da nutsuwa da kwanciyar hankali. Son Junaid take sosai gashi tana missing din irin wasannin da suke na tsokana. Wataninta biyu a gidan Nafisa hakan ya zama wata uku rabonta da Junaid. Iyakar alkhairi tana samu wurin iyayen wanda bai damu da ita ba. Senator ya siyawa babanta mota ya canja musu gida. Duk sai da aka hada da ban baki Mal Aminu ya karba. Itama Hafsi dubu hamsin ta bawa Ummati saboda bikinta saura wata biyu.
Hafsi da Hamida suna zaune tana ta yiwa hamida tsiyar ciki Nafisa ta shigo falon da faraa. Big sis ta samu ne hamida ta tambaya. Kwarai kuwa yanzu Alhaji ya ce muje ayiwa Hafsi passport dukkanmu zamu umra. Farin ciki mara misaltuwa ya bayyana a fuskarta. tana ta godiya ga Allah. Ta samu damar zuwa yin addua sosai game da Junaid.
Batul Mamman????
TUN KAFIN AURE????40
Maaikan daya daga cikin bankunan da Junaid ke ajiya bisa umarnin senator Rufai suka gano masa atm machine din da yake amfani dasu wurin cire kudi. Duk a area daya ne hakan ya bashi tabbacin Junaid yana garin Abuja a sheraton hotel don shi yafi kusa da wurin atm din. Ba tare da ya sanar da iyalinsa ba ya tura ayi masa bincike a hotel din da ma wasu wuraren shakatawar dake kusa da wurin. Cikin ikon Allah bayan kamar awa biyu da tafiyar yan aikin aka kira Senator aka sanar dashi Junaid yana sheraton din harda room number aka bashi.
Damuwa da bakin ciki sunsa hafsi wata irin rama. Bata cin abinci sai abu mai ruwa ruwa. Kullum hakuri kawai suke bata. Karshe Nafisa tace gara ta tafi d ita gidanta saboda ta rage kadaici. Haka ta hada kaya suka tafi. A cän kano yaya hadiza ce kawai tasan abinda ke faruwa ita ma nafisa ce ta sanar da ita. Hadizan ce ta hana a fadawa iyayensu tace zata zo garin karshen wata idan maigidanta zaizo conference don haka kawai idan ta tafi baffa fada zaiyi yace Hafsi bata dade ba baya son yawo. A gidan nafisa ita da yaranta koda yaushe suna tare da Hafsi. Hatta abinci tare suke ci shiyasa bata da lokacin tunani da kuka sai ta shiga daki kwanciya.
Kwanaki biyu bayan an yi freezing account dinsa yaje atm ya dawo ya dubi Tilly dake rawa a tsakar daki. Naje atm fa duk machine din yayi rejecting dinsu. Ta rage sautin kidan tare da hade rai me kake nufi to? Ka duba a na wasu areas din mana. Ya zauna bakin gado naje wuri biyar fa. To ai sai kaje banki don yau dole sai ka biya ni. Hannunta ya kama ya zaunar da ita. Haba Tilly bafa call girl kike ba. Yanzu aurenki nake so banga dalilin biyanki ba duk kwana. Ki bari gobe naje na karbo keys din gidan sai mu koma can. Na gama gajiya da abincin hotel ga rashin abinyi. Hararsa tayi sai yaji gabansa ya fadi….Hafsi ce mai yawan yi masa irin wannan kallon. Ko sau daya baiyi mata waya ba gashi har yayi sati uku rabon da ya ganta. Tace kai malam dakata min, kudi fa sai ka bani ka tashi kaje banki kawai. Ya sauke murya kinga tym fa tilly gashi yau friday dole sai monday zan iya zuwa. Amma ina da cash a gida if you cant wait. Da yake akwai ta da hadama tace jeka ka dawo ina jira. Zan fita nima kafin ka dawo.
A kwance ta tarar da Rosie tayi amai har ta gaji. wani matsatsten wando tasa da karamar riga sai dan karamin mayafi shaidar ita musulma ce. Gidan duk yayi kura saboda sanyi ita kanta Rosie duk ta rame tayi baki. Abinka da hasken bleaching. Lafiya Rosie me zan gani haka tana magana tana toshe hanci. Cikin kuka tace Tilly da kina duniyar nan? Kwana nawa babu ke babu labarinki ko wayata ba kya dauka. Irin sakayyar da zaki min kenan? Na gama kashe kudi na tas a kanki duniya ta samu kin sani a shara. Tilly ta zauna can gefe. Yi hakuri bana son juni ya zargeni ne. Me ya sameki? Yunwa Tilly yunwa. Gashi na kasa girki saboda rashin kuzari. Tilly ta kalli cikin da ya fito sosai ko don rosie ta rame ne oho. Su shege manya ashe ana nan baa rabu ba. Ai na dauka tuni kin koma harka. Maganar ta sosa ran rosie sai ta dake dai. Me nema dole yayi hakuri. Wata yarinya mai sayar da plantain Tilly ta samu kusa dasu ta gyara gidan ita kuma tayi abinci. Bayan Rosie ta dan dawo hayyacinta Tilly tace na fa shiga problem kawata. Maganin nan kamar ya fara loosing effect dinsa. Kinga yau motsi kadan sai yace zashi gida to gudun kada naji a jikina na bari ya tafi. Idan akwai sauran sa ki bani. Cikin takaici ta kalli Tilly, lallai samun duniyar dan tsako. Dama nasan dole ce ta kawo ki wurina. To bani dashi ki koma halinki ya zaunar dake. Tilly ta mike aikin banza biyanki fa zanyi. Nan ta jefi rosie da kudi gashi nan dubu hamsin ne. Karyarki tilly har kin isa ki wulakanta ni. Har kin manta duk abinda nayi miki a rayuwa? Idan kika ci amanata Tilly nima zanci taki. Tilly ta ja tsaki da wannan kayan a gabanki…to naji duka sai nasan kina yi. Haka suka yi ta fada kafin da kansu su sauko don tilly bata da niyar barin gidan ba biyan bukata.
a firgice ya shigo gidan Mummy har tsoro taji. Junaid dama kana nan? Baka neman iyayenka da matarka. Ya gaisheta ta kau da kai lallai yaron nan bama ka da kunya. Yace mummy kiyi hakuri. Ina oldman? Baki ta bude oldman kuma Junaid? Hala abin ya naka ya dawo. To bari kaji in fada maka wannan iskancin bazan sake dauka ba. Yace kiyi hakuri mummy Alhaji nake nufi. Ina dayar to? Dama ita yake son tambaya amma ya kasa. Ban sani ba ta bashi amsa tare da mikewa ta haye sama. Tana hawa ta kira Bulus maigadi tace kada ya bari kowa ya fita sai Alhaji ya dawo.
Batul Mamman????
TUN KAFIN AURE????42
Sau uku tana katse wayar tare da yin tsaki. Ya kalleta fuskar nan babu fara’a. Ya rasa dalilin zamansa da ita don ko kadan baya sonta. Bashi da sukuni indai ba kusantarta yayi ba shiyasa take gara shi sosai. Parties kala kala yake dawowa ya tarar ta shirya a gidan samari da yan mata su taru su hole. Idan yayi magana kuwa ranar sai ya kusa kuka zata bashi hakkinsa. Yana dai zuwa gaida iyayensa idan ta gadama amma zancen Hafsi tace ko zuci yayi zata sani kuma tayi rantsuwa ranar sai dai hawayensa su kare bazata bashi kanta ba.