TUN KAFIN AURE Page 41 to 50 (The End)

Ruwa Hafsi ta diba a wata roba taje falo ta kwance dankwalin kanta ta jika shi tana goge masa jiki. Nafisa taje tana bude buden dakuna har taga kayan junaid. Riga kawai ta saka masa suka fice. Ihun Tilly suka ji tana kada ku barni da muzurun nan. Sai da drebansu ya sha wahala kafin ya iya kulle muzurun a kitchn dama ta taga ya shiga. Bakin Tilly duk jini don ta sha faratansa masu tsini suka tausaya mata ta shiga motar tare dasu. Asibitin kudi suka je inda aka yiwa junaid gwaje gwaje likita ya tabbatar babu abinda ke damunsa sai yawan tunani da bacin rai. Mummy da senator ma sun zo ana yiwa Tilly dressing din ciwukanta. Babu wanda ya kula ta a cikinsu suka wuce wurin Junaid.
Washegari sai wurin shadaya na safe Junaid ya farka. Koda ya bude idanu iyayensa ya gani da yan uwansa. Hajiyan dangi ma tazo daga kano. Yunkurin tashi yayi yaji hannu ya danne shi ta baya Juni ka kwanta jikinka ba kwari fa. Na shiga uku ce ta subutu daga bakinsa. Don har zuciyarsa saida ta kada don yanzu tilly tsoro take bashi. Yace me kike a nan ba na sake ki ba? Wani murmushi mummy tayi har kana ganin hakoranta, ita kuwa Tilly me kumburarriyar fuska tace dont mind him zafin ciwo ne yake damunsa. Imran da yake asibitin tun safe bayan ya kira wayar hamida ta dauka yace ke bana son iskanci…sai yayi saurin rufe bakinsa Allah na tuba. A gabana yayi mata saki uku wallahi kuma harda text ma shaida. Karya yake Mummy don Allah kada ku rabani da Juni. Nafisa tace idan ma joni ne ke da shi har abada. Kuma idan baki fita ba Allah security zan kira miki. Ta kalli su Hajiya tace ai a kwance muka ganta tana wani tsafi muzuru na lasheta kamar maye. Duk shi yaji mata ciwo. Tilly cikin kuka da daga murya tace wallahi karya ne bana tsafi. A jikin Juni nayi niyar shafa maganin shine na fadi ya goge a jikin mage. Subhanallahi dama asirce shi kike yi. Saurin rufe bakinta tayi jin baram baramar da tayi. Tana girgiza hannayenta da kanta tace ba haka nake nufi ba wallahi. Hamida ce ta bude kofa zata tura Tilly waje sai ga muzuru ya shigo ji kake yana meooowww da yaga Tilly. Bayansa nurses biyu ne da wani cikin masu gadi sun biyoshi da gudu. Jikin Tilly ya dafe yana zazzare idanu harda wani lafewa a kafadarta. Ita dai mutuwar tsaye tayi ko motsi ta kasa. Maigadin yace kuyi hakuri muna binsa yana gudu kamar yasan inda zashi ne. Imran dariya har kasa ta kaishi yace no ka barshi kawai ga matarsa nan ya nuna Tilly dake hawaye ba kakkautawa. Tausayi ta bawa hajiya tace don Allah a raba ta dashi. To dai jikin Tilly kamar me wasan kura da kyar aka rabasu don sai da aka yiwa muzurun allurar bacci ya fado. Tana ta godiya nan ta fada musu duk sharrin data kulla ita da Rosie ta roki gafarar su. Hafsi da ke can gefe akan kujera Tilly ta kalla tace kema sharrin dana yi miki babu ma cikin kawai so nayi ya sake ki.
Nan dai kowa yace ya yafe Nafisa tace ina kudin da kika karba wurin Junaid. Sai lokacin ma ta tuna cikin kankanuwar murya tace yana drawer a gida. Nafisa ta sha kunu to babu ke babu su don har atm din Alhajinmu ya sata yana baki kudi. Daga nan ki san inda dare yayi miki.
Hajiya tace to kuzo mu tafi gida don a kawo musu abinci. Hafsi ce kan gaba Hajiya tace ni bana son gulma zauna wurin mijinki kinji ko. Kamar tayi kuka duk suka fice. A bakin kofar ta tsaya taki juyuwa ma ta kalleshi. Kusan minti goma tayi a haka har kafaĆta ta fara sagewa shi kuwa Junaid dama kyaleta yayi don yaga iya gudun ruwanta. Yana kallonta ta sa nauyi a wannan kafar idan ta gaji ta canja. Murmushi tayi don ta fara bashi tausayi.
Batul Mamman????
TUN KAFIN AURE????45
Da kyar ya mika hannu ya dauko wayarsa don ya kira imran. Kansa ne yake juyawa saboda tsabar ciwo ga zazzabi da ya rufar masa lokaci guda. Missed call din Hafsi ya gani take yaji zuciyarsa tayi masa sanyi. Kiranta yayi amma har wayar ta kare ringing bata dauka ba.
Tsaki tayi ganin me kiran ta wurga ta kan gado tare da tayar da sallah. Husna ce ta shigo dakin jin waya tana ringing ta dauka ta fita Maama ga wayar Mama Hafsa tana ringing. Nafisa ta ajiye remote din hannunta ta kalli Husna. Yanzu wa yace ki dauko mata waya? Maama sallah take yi. Kinga an sake kira ma. Nafisa ta karba ganin sunan Junaid tayi saurin dauka. Tana jin muryarsa ta mike tsaye Junaidu kana ina? Jikinta har rawa yake yace sis kece? Sautin kukansa taji yace i need you please. Kizo gidana yanzu. Kwalawa Hafsi kira tayi ki fito muje gidan Junaid Hafsi ina jin akwai matsala don maganar da yake ma ya dena. Hafsi najin haka itama kukan ta fara suka dunguma waje driver ya kaisu unguwar maitama inda gidan Junaid yake. A hanya ta kira mummy ta fada mata itama duk ta rude don tasan ko ba a fada ba dan nata yana cikin matsala.
A falo suka tarar dashi yana ta rawar sanyi ga gumi ya gama wanke shi har rigarsa ta jike. Nafisa tace da drebansu yazo ya dauko musu shi asa shi a mota. Hafsi tace bari a rage masa kaya jikinsa yayi zafi sosai. Ina ne kitchen ma, duk ta rude tayi nan tayi can. Nafisa ta nuna mata da hannu tana dago kan Junaid.
Wata irin faduwar gaba taji lokacin da taga Tilly kwance muzuru yana bin jikinta yana lashewa. Ko motsin kirki ta kasa yi don duk inda ta motsa sai ya yakushi wurin. Yanzu ma cinyarta muzurun ke lasa. Auzubillahi minash shaidanir rajim. Abinda ya fito daga bakinta kenan. Tilly cikin kankanuwar murya tace taimake ni…muzuru ne ya dare kan fuskarta yana lasar mata baki saboda ta motsa bakin.
Batul Mamman????
TUN KAFIN AURE????47
Dole ta ajiye fushin ta koma kan kujera ta zauna. Tana zama ya soma dariya ai na zata kinyi short service ne shiyasa kika dogare a tsaye kamar soja. Dan turo baki tayi tana harararsa… shafa kansa yayi yace God how i missed that. Hafsi don Allah dan dawo nan ki zauna. Kujerar gaban gadon ta kalla daya nuna ta kawar da kai gefe sai hawaye. Kamar tana kara masa ciwo da kukanta ya taso a hankali ya dawo kusa da ita akan wata doguwar kujera. Janyota yayi ya rungume ba tare da yayi magana ba sai saukar hawayensa taji a wuyanta. Tayi saurin dago kanta kukanta ya kara tsananta. Fuskokinsu ya hada suna kallon juna yana shaqar daddadan kamshin jikinta. Ki yafe min Hafsa, ki yafe…bakinsa ta rufe da hannunta daya wanda yasha lalle mai kyau tace Allah Ya yafe mana baki daya. Hannun nata ya zare ya cigaba da magana. Nasan na zalunci kaina da irin rayuwar danayi adopting tun kafin nayi aure. Na janyo ma kaina da duk wanda ya rabeni bacin rai da bakin ciki. A yau nayi dana sanin duk wani shaye shaye da bin mata dana yi, rashin kyautatawa iyaye da keta dokokin Allah. Kuka Junaid yake sosai da sauti Hafsi ta kara rungume shi sosai tana share masa hawaye. Kasan lesson din dana dauka a rayuwarmu? Ya girgiza kai tace Allah Yana bawa bayinsa chance din tuba da dama don baa makara da tuba sai an mutu. Kaddarar aurenka tasa nayi abinda ban taba tunanin yi ba kaima kuma kabar abinda kake yi. Ni bazan dauki fushi da kai ba don idan Allah Ya yafewa bayinSa baya rike su ko Ya cigaba da kamasu dashi. Ni da kai duk da sauran musulmi duk muna bukatar inganta imaninmu mu tsayar da zukatanmu wuri guda a hanyar neman lahira. Kudi ba hauka bane face wani nau’i na jarabawa daga Allah. Sai dai munyi rashin saa da yawa cikinmu musammam ‘ya’yan musulmi idan muka ganmu ko iyayenmu a madafan iko a kasar nan sai muyi ta barna da dukiyar da ba tamu ba. Yace hakane kuma gashi da sanin iyayenmu muke yi. Zanyiwa Alhaji magana kinga duk abinda nayi a da bai taba hanani kudi ba. Nagode da Allah Ya hadani dake Allah Ya yi miki albarka tace amin. Dago fuskarta yayi yana kokarin kissing dinta ta sake sunkuyar da kai. Au bayan duk kin gama zance ni shine zaki wani sunkuyar da kai kasa. Dama fa na gano ki tun dazu abinda kike jira kenan shiyasa kike ta wani shige min jiki. Hararar nan mai burge shi tayi masa ta tashi da sauri. Kada ka manta ni amarya ce samuna sai anyi da gaske. Yanzu ma don baka da lafiya ne. Yayi mata murmushi me kashe zuciya Hafsi Hafsi tawa Allah Ya barmu tare.