UBAYD MALEEK Page 1 to 10

Abu uku ne NURU takedashi duk nata kyawun takejin dama ita Allah yabawa duk ta hada,
Dirarriyar shape din NURU dayafi nata sosai sbd hips da Allah yabawa NURUn da qarin cikin NURUn dayafi nata shafewa sbd ita tafi NURU jiki sai gashin Nan na uku asalin yelloebrown fatar amhara da NURUn ta dauko Wanda yafi nata.
Wanka NURUn itama tayo taraka meryam itama tayo sukazo sukai sallah dukkaninsu atare kafin suka dungamo tsakar gida suka zauna cin abinci tareda iyayensu.
Kallon yanda sukecin abinci abal keyi Yana karantarsu Dan sake tantance wacce zai bada,
NURU yake kallo sosai Yana sake yaba sanyi da nutsuwarta saidai Sam bazai iya badataba sbd cutatuwa zatayi musamman idan yayi duba da baisan taqamaimai waye acikin delah za’a bawa ‘yarsaba.
Kallonsa ya maida kan padima wadda Kecin abincin a kiyaye batason Bata bakinta sosai Sarai yasan halinta da babban burin son abun duniya shiyasa zuciyarsa ke wasi wasi akanta Dan idan taje giyar daular arziki da mulki suka bugeta Yana tsoron ta zama wata mutum dabam sbd tsananin son duniyarta da jijida kanta yanada yawa kowa yasanda wannan.
Numfashi yasauke Wanda yasa ammi kallonsa sbd tasan tunaninsa tana lure dashi da yanda yake karantarsu,
Itadai tunda abune na dole baza’a taba guje masaba to a gaskiyance gwara abada padima sbd tunda sunada wata ‘yar bazata iya Bari abada NURU ba Dan baqaramar cutatuwa zatayiba,
Bazata iya rayuwa acikin sarautaba sam,
Tsaftatacciyar zuciyane da NURU zasu gurbato musu ita da rudin zalamar mulki da dukiya gwara padima tana zuciyar son abun duniya Dan haka zata iya gwagwarmaya acikinsu ta qwataci kanta dama ‘yayan negestati dazata haifa.
Suna kammalawa dukkaninsu suka hau fira da abal dinsu bayan NURU ta tattare gurin itada meryam suka dawo suka zauna.
_________________
*_No 554 U.MALEEK DELAH Aptmt_*
_Jericho brighton New York City,New York._
Mum””Yar budurwar yarinyar da Bata wuce sha Tara ba ta furta cikin nuna takaicinta da damuwarta a fili tana kallon takardun hannunta data dauka daga gaban madubin bedroom din uwar Tata.
Qarasowa tayi idanuwa na cikowa da hawaye har gaban dining din ta daga takardun dake hannunta tana cewa”
Mum menene wannan??
Cikin wata irin cikakkiyar izza data gama Kama jininta ta dago a natse Kamar Bata fahimci damuwa da tarin baqin cikin data gani atattare da babbar ‘yartaba wadda bazaka taba cewa ‘yartaceba sbd itama tsufa ko wani manyanci ba gama kamata yayiba sakamakon auren wuri na sarauta da akai musu da mijinta shiyasa ‘yartata tazamto Kamar wata qanwarta danma tafi Yar ‘kyawun jiki da itakuma ‘yar tafita kyawun fuska nesa ba kusaba sbd zallar Kamar mahaifinta data dauko.
Kallo daya tayiwa takardun kafin tamaida kallonta kan fuskar ‘yar cikin wani irin sautin zallar iko da mulki tace”
AFIA menene naki akan wainnan takardun dake hannunki?
Wannan tsakanin nida abal dinki ne so stay out of it okay?
Dire mata takardun tayi da qarfi gabanta idanuwanta na cikowa da hawayen baqin cikin halin mahaifiyarta tace”
Mum wannan decision din naki na nufin rabuwa da abal fa,kinsan abal mgn daya yakeyi Wanda idan yayi Babu Wanda ya isa canzawa
Mum are you willing to take that risk?
Idan bakya tunanin kanki da rabuwa dashi mum please kiyi tunanin mu ‘yayanki idanma Ni bakya tunanina kiyi tunanin farhat Mana,
Mum farhat bazata iya rayuwa Babu ‘dayankuba tsakanin ke da abal idan kikai signing wannan contact din Kika tafi Tokyo shikenan fa kinbar delah har abada bazasu karbekiba kokin dawo daga baya please think and think and think mum”” taqarasa mganar hawaye na gangaro mata tanajin Ina zata Sanya zance mum dinta ta aje wannan rayuwar dama tafi ta turawa zama abin tsoro.
Spoon din boiled veggies da aka soya da kwai takai bakinta tareda shanye sauran black lemon tea dinta ta zari tissue ta goge bakinta kadan ta miqe tsaye sai alokacin ta fuskanci afia din dakyau ta kalleta cikin wani irin iko tace”
AFIA tuntuni nasan cewa zanbar delah duk ranarda na karbi contract din santrigo Tokyo na jirane dama sbd ki qara girma kiyi wayonda Zaki kula da farhat idan natafi hakama idan nadawo nasan Zaki tsaya tsayin daka su karbeni,
Santrigo Tokyo babban burinane Dana girma dashi na rayu dashi Dan haka aure bazai hanani cika burinaba ayanzu Dana samu dama,
Idan kinason duk wannan kar ayi azauna lfy kije kiyi convincing dad dinki yabarni naje Tokyo nayi aikina Dan bazan bar aikina Dana dauko shekaru fiyeda goma sha ba inayi akan tsantsar ikonsa da izzarsa ba.
Wani numfashin mamakin mum dinta tasake tana mata kallon mum kinyi nisa ta sake sauke wani numfashin tareda gyara tsayuwa ta kalleta cikin sanyin murya tace”
Mum kinfi kowa sanin mijinda Allah yabaki idan duk dukiyar Tokyo zakije abaki bazaki samu abinda yakai Wanda kike samu agunsaba,
Duk abinda Zaki samu a duniya bazaki samu abinda yakai _*UBAYD MALEEK DELAH*_ ba,
Mum Ina sake Baki shawarar kizauna adaki kiyi tunanin abinda kike Shirin aikatawa,
Zaki rasa mijinki,’yayanki biyu,dukiya,suna da matsayinki na Matar _MALEEK_ na GIZAH Wanda nake ji Miki tsoron rasawa har abada.
Ke mahaifiyatace bazanso ki rasa duka wainnan sbd abal shine abu na qarshe da mace zatai baqin cikin rasa samunsa a rayuwa.
Wani QAYATACCEN murmushi LAILAH tasaki tareda dafa kafadar ‘yarta tace”
AFIA ke yarinyace
Kinason dad dinki fiyeda komai shiyasa kike ganin dukkanin hakan Amma abinda Baki saniba shine dad dinki mutum ne da duk duniya Babu me juyasa sai kakansa Wanda Shima halinsune yazo daya,
Inaga zaifi ki nutsu ki maida hankali kan karatunki ki Kuma kula da farhat Dan zata shiga damuwa sbd bananan Kuma dad dinku is a very busy man.
Kasa cewa komai tayi tabi bayan mum din Tata da kallon damuwa da baqin ciki harta haye sama.
Masu aikin gidan ne kusan su biyar sukazo suka fara tattara kayan dining din suna gaidata cikin tsananin girmamawa duk da dukkaninsu sun girmeta wasuma sun haifeta Amma sbd matsayinta na babbar ‘yar maleek suke Bata mugun girma.
Ko kallonsu bataiba sbd halinda zuciyarta take ciki gabaki daya a jagule take bazataso auren iyayenta ya rabu ba akan iko,izza da isar dad dinta dakuma taurin Kai da burin duniya na mum dintaba,
Farhat kawai take dubawa sbd yarinyace sosai akanta sbd ita yanzu takeda 8years a duniya bazata iya ganin iyayenta sun rabu ba saidai abu daya tasani shine rabuwa kamarma sunyine Dan Babu abinda zai sauya taurin Kai irin na mum
Dad din Kuma aishi kankat ne Dan yafita zama riqaqqe saidai tana jin tausayinsa sbd mutum ne shi me tsananin qyanqyami na komaima
Suna rabuwa da mum za’a fara kawo Masa ‘yayan manyan masarautu kokuma ma za’a iya kawo Masa negestati Wanda tasan tsananin qyanqyaminsane ya hanasa qara aure aure kamar sauran ‘yan delah musamman shi dayake ubayd maleek na GIZAH,
Hakan nema yasa ya kebe kansa anan new York da iyalinsa Yana gudanarda rayuwarsa a qaidance yanda yake sonsa ba tarkacen hayaniyar masarauta duk da yasan dole wata Rana zai koma can da zama.
Bedroom dinta ta nufi ta fada kan gado tareda rintse idanuwanta hawayen ciki suka gangaro ta share da qarfi cikin takaici tace”
Bazanyi kukaba mum tunda haka Kika zabar Mana shikenan zamu runguma mu rayu Kamar marayu duk da munada uwa Amma ta zabi duniya akanmu.