UBAYD MALEEK 1-END

UBAYD MALEEK Page 1 to 10

Wani mummunan tarine ya qware NURU idanuwanta suka firfito tafara tarin cikin azaba da tashin hankali tun tana shafa Mata baya hardai dole suka fito daidai fitowar amminsu Nan sukai kanta akaita Bata ruwa Ana fesa amata Amma sosai ta sarqu idanuwanta sunyi jajir sbd azaba cikin fada ammi tace”

Menene ya sarketa padima?

Ammi kawai zaune take saita fara tari shikenan ne kawai.

Fitowa abal yayi daukeda sabuwar madarar raqumi yabata yakuma fesa Mata take abin yafada Mata tafara fidda numfashi daqyar tana rufe idanuwanta cikin galabaituwa.

Padima ta tayata ta watsa ruwa takaita daki itama tadawo tayi wankan tazo tayi sallah saikuma takejin kunyar NURU din Amma Kuma tunda dai amfani takeson yi da ita dole zata fada Mata hakan.

Kwanciya dukkaninsu sukayi babu ko me dogon motsi sbd tunanin da kowa keyi musamman NURU dake cikin tashin hankalin jin masifar dazata samu ahalinsu.

Washe gari ma NURU ce taje wankan ruwan madaran haka zalika takasa sake tankawa padima maganar dasukai din sbd har lokacin shock din maganar Bata saketaba.

Padima ganin ankwana biyu NURU taki cewa komai gashi zuwa lokacin kowa ya shaida NURUn Bata cikin hayyacinta tana cikin tsananin tsoro da tashin hankali saidai anyi tambayar duniya taqi fada sai kuka.

Hankalin iyayensu yatashi sosai musamman da itama padima suka lura duk a firgice take ta bangare daya wankan haryanxu basuda masaniyar idan anzo NURU akewa sai gidan yakoma Kamar gidan da akai muguwar mutuwa sbd gabaki daya kowa baya cikin nutsuwa anyi anyi NURU tafada abindake damunta taqi fada sbd gabaki daya tsoro da firgicin abinda zaisamesu yasa ta kasa dawowa hayyacinta tsoron fadama takeji.

Yau dai padima da takaici da baqin ciki ya isheta sbd saura kwana goma sha biyu cikar wa’adin cikin tsakar dare ta tashi ta sake dauko wuqa yauma tadawo ta zauna tsakar dakin tareda fashewa da kuka yanda NURU zataji Dan dama tasan ba bacci takeba saigashi tana bude ido taga padiman ta daga wuqa zata sokawa kanta da gudu ta zaburo ta riqeta cikin tashin hankali tace”

Padima.

Qwace wuqar ta hau Yi padiman ta riqe cikin tsananin kuka take cewa”

Kibarni NURU gwara na mutu sai kowa ya huta matsalarmu da tsoronmu zai qare idan na kashe kaina shikenan Babu Wanda zaisan abinda nayi bare rayuwar abal da ammi tashiga hadari duk laifinane Dana Bari harnazo yanxu ban Kai qarshen matsalarba gashinan kema nasaki a damuwa bazan iya ganinki cikin damuwa da qunciba NURU sbd Ina tsananin sonki ‘yar uwata.

Cikin hawaye NURU tace”

Bazaki iya ganinaba cikin qunci kike tunanin Ni zan iya ganin kin kashe kanki.

Zamewa tayi ta zube qasa tana rusa wani sabon kuka tace”

NURU komai ya lalace a rayuwata

Mutuwata itace salama agareku sbd matsalar ta wuce yanda kike tunani NURU cikine Dani yanxu haka…

Neman zubewa NURU keyi padiman tayi saurin riqota tana cewa”

Kingani ko gashinan kina neman sumewa sbd jin wannan muguwar masifa gwara na mutu kowa ya huta NURU kibarni kawai….

Kokuwa suka hau Yi akan saita dauki wuqar NURU na riqeta cikin tashin hankali take gabaki daya hankalinta yakasa dauka wai padima harta San bawa wani kanta,mutuncin,qimarta hadda ciki.

Zubewa tayi qasa tareda rushewa da wani irin kuka Wanda yasa padiman itama zubewa tana sakin nata kukan.

Kwana sukayi kuka Koda gari ya waye kowacce fuskarta da idanuwanta sunyi suntum ai Nan hankalin abal da ammi yatashi musamman dasukai tambayar duniya kowacce tayi shiru har Saida abal din ya harzuka yace aqyalesu koma menene idan sunji uwar Bari sunzo dakansu sufada itadai ammi hankalinta bai kwantaba taringa lallabarsu Amma ba wata mgn saima Kamar zurfafa da NURU keyi da tunani.

Jan padima NURU keyi Kamar wata qaramar yarinya harsuka isa inda tacewa amed su hadu suna zuwa kuwa Yana gurin NURU ta jefesa da kallon qyanqyami da baqin ciki take zuciyarta ta gaurayu da tsanarsa saidai Babu yanda ta iya tunda dole cikin biyu daya za’ayi dole shine zataji idan zai auri ‘yar uwarta daya lalatawa rayuwa.

Wani abu ta hadiye me Kama da dutsi ta zuba Masa manyan fararen idanuwanta dasuka kusa gigitashi ya dauke Kai da sauri sbd wlh kallon cikin qwayar idanuwanta kawai na iya sumar dashi da duk wani ma’abocin begenta.

Ka yadda da Kaine kawai kasan padima amatsayin ‘ya mace?

Da sauri ya gyada Kai Yana satar kallon padiman dake Masa wani kallo.

Sake jeho Masa qata tambayar tayi da cewa”

Kasan cewa tanada juna biyu yanzu haka a jikinta Wanda yake nakane?

Nasani Kuma ashirye nake da aurenta kafinma kowa yasan da akwai cikin Amma Kuma sbd zata zama negestati wannan al’amari yazama mafi hadari ga rayuwarmu mu duka hadda ta iyayenmu,

Wlh inason padima sosai itama tana Sona NURU Amma yanzu tsautsayi daya gitta mukai wannan abin yasa yazama Kamar wata mummunar qaddararmu da iyayenmu da basujib Basu ganiba..

Rintse ido NURU tayi wani nauyi na ziyartar zuciyarta idanuwanta sukai jajir tace”

Idan harka aminta zaka aureta shikenan kaje kashirya kawai.

Juyawa tayi tabar gurin idanuwanta na sake rinewa da tashin hankali ta nufi gida ko gabanta Bata gani sosai ta fada dakinsu ammi dake zaune tsakar gida tana gyarawa meryam gashi tabita da kallo zata miqe tabita saiga padima tashigo itama tafada dakin.

Rungume NURU tayi cikin tsananin farin ciki ba kunya tahau yimata kukan godiya NURU da baqin cikin al’amarin ya danne Mata zuciya tace”

Padima menene ribar wannan masifar dakika saka kanki damu aciki?

Shin bakiyi tunanin abinda zai faru da iyayenmu ba lokacinda Zaki bawa wani kanki?

Shin bakiyi tunanin wace rayuwace makomar nida meryam ba idan hukunci yahau kanki keda iyayenmu?

Menene laifin su abal dabasujiba Basu ganiba idan anhukuntasu akan laifin da Kika aikata bayan dawainiyar dasukai akanmu suka bamu tarbiya.

Riqota padima tayi cikin marairaicewa tace”

NURU nayi nadama nayi Dana Dani Kuma tunda kin amince da rufa min asiri ki sauyeni ai matsalar ta wuce……

Ta wuce?

Ta wuce fa kikace padima?

Cikine fa ajikinki na namijinda ba mijinki kike cewa shikenan yawuce…..

Qarar sakin kofin silba sukaje daga bakin qofa take suka juya da sauri cikin firgici ganin ammi hadda abal tsaye yasa padima fara rawar jiki cikin tsananin tashin hankali NURU kuwa zamewa tayi ta zaune al’amarin na isarta Sam kanta baya iya daukan doguwar pressure.

*************

_Jericho new York_

Setin akwatinanta guda biyar cif aka jera Mata cikin mota guda qirar Mercedes Benz beymach 10/2607 2021 ta fito daga bedroom dinta sanye cikin wata doguwar turkian royalle satin gown red me kyau wadda ta fidda kyanta da kyan jikinta hannunta riqeda handbag din arkins irin qamshin datake fitarwa me yawa zaisa kasake tabbatarda ta aje auren tun daga cikin dakinta Dan Vail din rigarma rolling dinsa tayi iya wuyanta tafara saukowa cikin yanayinta na yanga da aji kamar ko yaushe.

AFIA dake zaune Palo riqeda hannun farhat daketa kuka kamar ranta zai futa tana ganin fitowar mum din tasu ta miqe tsaye itama idanuwanta na fara tsiyayar hawaye tafara girgizawa mum din tasu Kai tana cewa”

Please no mum,

Mum please please no.

Itama lailar tanason ‘yayanta tanason kasancewa dasu saidai tasan ko zatayi mushe ubayd maleek bazai barmata ‘yayansaba Dan haka tunda tasan zasu samu kyakkyawar rayuwa tareda dad dinsu bazata wani damuba ta qaraso ta rungumesu suka qanqameta suna kuka sosai suna roqonta sai Basu hkr takeyi tana cewa”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button