UBAYD MALEEK Page 11 to 20

Duk ranarda wannan zancen yafita ta hanyata na bada kaina acire fansar cin amanar danayi.
Jinjina Mata Kai yayi ta miqe tafice tana sake basa gaisuwa.
*************
Zaune suke jigum jigum fuskokinsu cikeda damuwa da baqin ciki Babu me iya mgn se sautin kukan padima dake fita ahankali ahankali tana roqon abal da ummi dasu yafe Mata tsautsayi ne.
Cikin nauyin zuciya abal ya dago ya kalleta da idanuwansa dasukai jajir kafin ya kalli ummin da ita shita kalla da idanuwanta dake cikowa da hawaye tana maidawa sbd batason zubarwada padima hawaye kada Allah ya kamata da laifin sakasu zubda hawaye abin yamata yawa,
Fahimtar abinda abal ke nufi da kallon dayai Mata yasa ta bude Baki daqyar cikin nauyin nurya data toshe da baqin ciki tace”
Padima mune iyayenki da bazamu taba zabar Miki abinda zai cutatar dake Dan haka kiji tsoron Allah kifada gskiar abinda yake faruwa,
Nice na haifeku duk ku duka Kuma nasan halin kowannenku fiyeda ku kanku tun ranarda akai maganar badake delah zuciyarki Bata amintaba Kuma shine dalilin dayasa Kika Hana kanki sukuni koba haka ba???
Tsit tayi tana Dan share hawayenta cikin jin tsoron anfara ganota takasa dago Kai ta kalli kowa cikin tsananin fushi da baqin ciki abal yace”
Hakane koba haka ba?
A kidime cikin tsoro tace”
Eh Hakane.
Dukkaninsu wani sabon baqin cikine ya turniqesu musamman NURU da hawayenta suka fara gangarowa.
A qyamace ummi tasake jefa Mata kallon baqin ciki tace”
Sbd baqyason abadake delah shiyasa jika bawa wani kanki yayi Miki ciki sbd ki nuna bamu isa dakeba duniyar dakikeso ita Kika saka gaba….
Da sauri ta girgiza Kai tana fashewa da kuka tace”
Ummi kuyi hakuri wlh banda ciki Amma..Amma…Amma tsoron hukuncin kasheku danima idan naje delah aka….aka..aka gano…yasa nace inada ciki sbd NURU ta yarda taje ta yanda Babu abinda zaisamu kowa wlh ummi sharrin shedan ne Kuma….
Wani wawan gigitaccen Mari abal ya sauke Mata guda biyu Wanda yasata zubewa kwance tana hadiye sauran maganar cikin tsananin tashin hankali sbd yaune karo na farko da aka taba lafiyar jikinta.
Kasa mgn ummi tayi sai hawaye sbd sunkasa riquwa yanxu Kam,
Cikin baqin ciki abal yace”
Sbd son ranki Kika siyarda mutuncinki,
Kika ringa wasa da amfani da qaunarda ‘yar uwarki ke Miki harkina qarya da zance me girma na cewar kinada ciki Dan kawai bakyaso.
Kinyiwa kanki padima,
Kinyiwa rayuwarki,
Ban Miki bakiba Amma wannan abinda kikai shine babban kuskure mafi girma dazakiyi danasani akansa Amma tunda ke Kika zaba hakan ‘yar uwarki zataje delah kekuma idan kingama tsare tsaren burikan naki amed din yafito zanmuku aure dashi Allah yabawa kowa alkhairinda yake fata.
Miqewa yayi Rai bace ya fice yabar gidan ummi ma qala batace Mata ba ta miqewarta meryam na riqeda hannunta.
Ba kunya padima ta tashi zaune tana share hawaye duk fushinda za’ayi tasan kowa zai sauko itadai tunda buqata tabiya angama me wahalar.
Kallon NURU tayi zatai mgn NURUn ta miqe batareda ta kalletaba zuciyarta na Mata zafi da radadin abinda padima tai Mata baqin ciki goma da ashirin ga tafiya delah ga abinda padima tayi ita rayuwartama ta ruguje gabaki dayanta sbd shikenan ta tabbata batada rabon zama acikin igiyoyin aure idan taje delah tariga tazama negestati idan ba Allah ne yayi Mata raboba tasamu damar shiga inuwar aure.
Gabaki daya gidan rikicewa yayi Babu me farin ciki bare walwala tundaga ranar sai padima data bushe ido tasakewarta da walwalarta da komai tunda buqatarta tabiya kowama yayita baqin cikinsa duk zasu dawo daidai idan komai yasake wucewa.
NURU ta sauya sosai gabaki daya yanxu batada walwala kullum cikin damuwa da tunani take idanuwanta harsum bushe da kukan tayi tayi tagaji harta daina saidai ido.
Ranarda jekadiyar Kaleb tazo duba NURUn tayi Mata kallo harna qurulla take tagama tabbatarda NURUn itace mafi cancantuwa Nan take takaiwa Kaleb rahoto yabada umarnin afara gyaranta tun agidansu kafin kwanakin daukota su cika.
Al’amari yadawo sabo sbd irin zarya da matakan tsaro da bayin da aka kawo aka zuba a gidan yasa al’amarin yafara bawa kowa tsoro da mamaki itadai padima ko ajikinta matsuwartama ayi ayi agama NURUn ta tafi sbd tsoron karma wani abu ya gitta aqara dawoda abun kanta.
Hankalin iyayensu yafara tashine sbd tunanin wannan tsananta tsaron da matakan dasukai yawa da wuya idanba gizah za’a Kai NURU ba sbd sai ‘da mafi kusanci da sarauta akewa irin wannan taka tsantsan din Amma dai Babu iko ko hurumin tambaya.
Cikin kwana goma sha daya dukkanin Wanda yayiwa NURU kallo daya baya sakewa a qaidance idan ba hakaba hukunci zai hau kansa sbd wani irin sauyi me yawa datayi,
Fatarta ta sauya fiyeda tsammani,
Haskenta ya ninku komai nata santsi yake musamman gashinta dako dankwali baya zama sbd tsantsi ga sutura ta alfarma da aka kawo daga Kaleb Kai tsaye a sirrance.
Ayau tun safiyar jiya take kuka har idanuwanta basa iya gani sosai sbd yaune ranar tarewarta/ma’ana tafiyarta,
Ammi da abal kwana sukai Bata nasihu da rarrashinta ita ammin ma Kamar yanda NURUn ke kuka hake takeyi Daren farko lafiyayyun motaci biyar sukazo daukeda dukiya da abinci tareda sitiru na alfarma wa iyayen negestatin kafin aka dauketa a sirrance tareda mahaifinta yakarata yakaita har gaban Kaleb Wanda yasake narkawa abal din dukiyar tukaici rakiya aka nufi wani kebantattcen sashe na musamman daya gama hada jin dadin duniya da NURUn tareda sabbin masu kula da ita su shida cif cif ha’di da jekadiyar Kaleb Wanda ke sake yaba zabinsu na NURUn.
##MAMUH#
*Last free page*
_ZAFAFA BIYAR_????????????
_SAFIYYAH HUGUMA_
_BILLYN ABDULL_
_MISS XOXO_
_HAFSAT RANO_
_MAMUH GEE_
_DUKA KUDIN WANNAN DADADAN BOOKS DIN SUNA KAN FARASHIN NERA 700. WATO KUDIN PAGES KENAN. DOCUMENTS IDAN AN KAMMALA SUMA KUDIN SU DABAN.._
Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????????
0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????????
*_08085405215_*
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????????
0903 234 5899
*_Mamuhgee 7_*
NURU Tasha kuka sosai tayi kewar Yan uwanta da iyayenta wanka tayi sbd ta gaji sosai tana zaune saiga wata hamshakiyar Mata Nan ta shigo dakin kallo daya tayi Mata tasan kudi yazauna Mata ????????mmn Anwar kenan ta zauna a kusa da NURU tace Mata sannu yata ykk ya bakunta????mmn Anwar taja fasali
Juyar dakai tayi daga kallon makeken dakin baccin ma’ana bedroom dinda take Wanda ita kaf rayuwarta da tunaninta dama irin labare labaren da padima ke fada Mata akan akwai daula da jin dadin rayuwa tareda qyale qyalin rayuwa Bata taba ayyano tunanin ganinsu Kamar hakaba abin ya shallake tunaninta musamman da tun jiyan sanyin AC ke shigarta a hankali Saida ‘dayar me aikinta data shigo dubata cikin dare taga yanda ta qudundune ta bude Mata qaton duvet me tsananin laushi da Sanya nutsuwa ta lulluba Mata batamasan lokacinda tasake shigewa cikinsaba tana gyara kwanciya sbd sanyin yayi Mata yawa ga tsoron baqunta na kwanciya daki ita daya.
Jin akaro na biyu ansake kwankwasa Mata qofa Ana sake sanar da ita anagama shirya Mata abinci yasa ta tashi zaune tareda miqewa ta nufi qofar qafafunta na rawa murya na rawa cikin sanyi tace”