UBAYD MALEEK 1-END

UBAYD MALEEK Page 11 to 20

Washe gari ma yini tayi daki kwance abinci kawai ke fiddo da ita Palo har dare bataga jekadi ba sai washe gari da yamma tazo bayan ta tabbatarda NURUn ta huta daga wahalar shekaran jiyan kafin suka fara gudanarda aikin dake gabansu.

Sannu ahankali jekadi take koyarda ita komai na al’amuran rayuwar gidan sarautarsu ta delah,

Duk wani abu dayakamata NURUn ta sani Kuma ta iya Ana kan koya matashi Kuma tana ‘dan ganewa duk da hankalinta tashi yake idan Ana fada Mata wasu abubuwan ko koya Mata sbd batasan ta Yaya zata gudanar da rayuwarta ahakan ba,

Ta bangaren iyayenta kuwa tuni ta aika musu da dukkanin tarin dukiyar tukuicin data samu.

Ga kaleeb ta bangare daya kullum saita je takai Masa gaisuwa Wanda jekadi ce ta ‘dorata akan hakan bawai Dan al’ada bace kawai tanason Gina qauna me qarfi ne tsakanin NURUn da kaleeb sbd sanin irin tsananin qauna dake tsakanin Kaleb da UBAYD MALEEK.

Sannu ahankali tafara sabawa da rayuwar delah ga jekadi ma data Dan shaqu da ita sbd tana Mata kallon uwa kokuma tacema Kaka musamman sbd itama jekadin tsakani da Allah taji tana qaunar NURUn sbd nutsuwa da biyayyarta ga rashin son hayaniya sai hakan kesake saka Mata nutsuwa da shigar NURUn rayuwar UBAYD koba komai UBAYD Kamar ‘dane agareta sbd agabanta aka haifesa yagirma.

Tsawon watanta biyu a delah Amma haryanxu ko a zance bataji maganar waye aka bada ita gurinsaba,yaushe za’a kaita,Ina yake haryanxu shiru duk bataji komaiba Abu daya tasani shine jekadi ta fada Mata wata me kamawa za’a kaita wani guri.

Da farko hankalinta ya tashi Jin tafiya wani guri Amma sai jekadi tafara kwantar mata da hankali da cewar zasu dawo bawai zaman dindin bane itadai Sam hankalinta yakasa kwanciya ko bacci yanzu kasawa takeyi saitajin Kamar rabuwa zatai da gida har abada.

Ganin kwana biyu har wata rama ta sakota gaba da tunani da damuwa yasa jekadi takwai Kaleb zancen sai tunani ya shegesa yace anfasa Kiran zuwan UBAYD sbd idan yazoma kowa zai San shi keda negestatin Kuma Kamar yanda akasan MALEEK da ikonsa bazai taba karban negestati ba matuqar ba baya tareda matarsaba hakan zaisa afara tunanin sun rabu Wanda za’a iya amfani da wannan gurin muguwar manaqisar mulki akawo suka ga karban mulkinsa Wanda keleb bazai taba Bari hakan tafaru ba yafison koda za’a San ubayd da matarsa sun rabu zuwa lokacin sun samu wata Matar aure kawai za’a daura idanba hakaba da matsala babba Dan haka yasa aka matso da tafiyar NURUn tareda Bata damar izinin zuwa ganin iyayenta da daddaren yau.

Qatuwar baqar Mercedes Benz beymach ta ajiyeta gefen gidansu da qarfe goma sha biyu na dare Wanda shine lokacin barinsu fita delah tana kallon qofar gidansu jikinta yayi mugun sanyi taji idanuwanta sun ciko da hawaye ta ziro qafarta waje ahankali tareda fitowa.

Kai tsaye itace agaba jekadi na gefenta tana cewa”

Karkiyi kuka gaban iyayenki Zaki daga musu hankali Kuma laifine babba yin kuka was umarnin masarauta Dan haka ki kula.

Batace komaiba itadai burinta ta Isa cikin gidan taga ahalinta cikin sa’a kuwa har lokacin abal dinta da ammi na zaune tsakar gidan kan shimfida suna Shan iska sbd tsananin zafin da akeyi yau din meryam ma na kwance gefen ammi tayi bacci ammin na Mata fitar sauro.

Da budaddiyar murya jekadi ta rangado sallamar da har maqota anaji sbd asan da zuwan NEGESTATI ne.

Da ammin da abal lokaci daya suka miqe suna kallon qofar dasu NURUn ke shigowa wadda qamshinta tuni yafara cika tsakar gidan da hanzari ta qaraso ta fada jikin ammi tana riqo hannun abal duk alokaci daya tana sake hawayen farin cikin ganinsu batareda ta iya cewa komaiba.

Cikin tsananin farin ciki ammi ke Mata yare tana cewa”

Ya Allah NURU munyi kewarki matuqa.

Murmushin farin ciki kawai abal ke saki Yana kallonta ta cikin hasken farin wata Yana sake godewa Allah daya bashi ikon ganin ‘yarsa ‘daya tasamu gidan zamanta na rayuwa saura daya itama Yana fatan Allah yabasa ikon ganin yayi Mata aure ta tafi nata gidan.

Zama sukai tana tsakiyar iyayenta Meryam ma tuni NURUn ta tayarda ita sbd bazata iya tafiya basui mgn ba tana ganin NURUnta tafada jikinta da qarfi tana ihun murna Wanda ya tado da gimbiyar gidan wato padima ta fito cikin wani irin laushi tana jujjuya ido ta bude da kyau tana kallon mutanen idanuwanta suka sauka kan NURU tasake dubawa dakyau taga NURU ce da sauri ta qaraso tana cewa”

NURU????

Kece yanxu?

Dagowa NURUn tayi fuskarta daukeda murmushin kewar padiman ta taso suka rungume juna tana cewa”

Nayi kewar dukkaninku padima.

Zaman sukayi padiman nabinta da wani kallon kurulla da zallar mamaki tanson yin tunanin fahimatar wani abu kanta Yana toshewa da mamaki dakuma tausayi tausayin NURUn da rayuwarta ta lalace.

Shagala sukai sosai harsaida lokaci yaja jekadi tashigo da cewar zasu tafi Nan jikinsu duka yayi sanyi Amma hakanan suka bawa NURU qwarin gwiwa abal yabita da wasu irin adduoin Sanya albarka masu zafi wainda suka Sanya jikin kowa yin sanyi suna amsawa da Amin.

Har mota suka rakota tashiga padima sai kallon komai take cikin mamaki tana qaryata abinda idanuwanta ke gane Mata sbd tasan ba komai bane duk wannan akan irin rayuwar da ita zatayi a Nan gaba.

NURU kuwa Har suka Isa delah tunaninta bai daina zurfafaba gabaki daya yanzu kanta a toshe yake sai yanda akai da ita yanzu kenan.

Tana Isa sashenta daki ta wuce Kai tsaye ko tubewa bataiba ta kwanta tareda rintse ido.

Washe gari haka akai fita da ita zuwa gurin passport Wanda tun kafin su Isa aka tanadi komai babu Wanda yasamu damar ganin fuskarta sai Wanda ya dauka hotonta dagacan Kai tsaye delah suka dawo washe garima saida aka futa da ita zuwa wani gurin wanda acanma tasake tabbatarda mulki wani abune na daban sbd irin girman da ake Basu ko cikin ansan cewar bama daya daga cikin jinin sarautaceba ita din.

Ranarda ta cika kwana shida da zuwa gidansu ranar aka gama Shirin tafiyarta tsaf a washe gari itada jekadi jirginsu yabar Ethiopia zuwa qasar France.

***********

Breakfast sukeyi zaune su uku akan dining din Wanda suka kwana biyu Basu samu damar cin abinci tareda dad din nasuba sbd rashin zamansa a kwanakin sai yau,

Kallonsa AFIA tayi taga yanda yayi wani irin fresh fatarsa sai wani glowing takeyi tsabar hutu da arzikin dukiya duk da manyancinsa Amma Sam fatarsa taqi bayyana hakan idanma batai kuskure ba saitaga kamar bayan rabuwarsa da mum dinta wani nutsuwa yasamu.

Sake kallonsa tayi wannan karon suka hada ido ya zuba Mata manyan fararen idanuwansa cikin muryarsa me iko yace”

AFIA akwai wani abu ne?

Aje spoon din hannunta tayi ahankali tareda kallonsa gabaki daya cikin taushin murya da ‘yar sakuwa tace”

Dad please for how long zamuyita zama haka mum Sarah kwanakin Nan batajin Dadi qafafunta sunfara gazawa Ina tsoron zamu koma rayuwa mu kadai dagani sai farhat sauran maids din babu wani kusanci ko shaquwa tsakaninmu dasu.

Ciki wani irin Isa ya kurba ruwan Black coffee dake cikin farin teacup din hannunsa ya ajiye tareda daukan tissue yakai bakinsa ya goge ahankali ya ajiye tukuna ya dago ya kalleta yaji zancenta ya taba zuciyarsa tabbas suna buqatan abokin zama kada kadaici yayi musu illah gasu yara qananu,

Sam baida sha’awar maidasu zama gizah gurin mahaifiyarsa sbd kada giyar sarauta da mulki ya shigesu Dan kuwa tabbas zai shigesu sbd girma da irin bauta musun daza’aitayi zai gurbata tunaninsu sarauta zatai musu muguwar shiga bazai taba son hakanba Dan haka a yanzu dai baida wani zabi bayan karban negestatin Kaleb Amma bazai taba Bari Susan da hakanba sbd bai karbetaba bakuma zai taba karbantaba zaidai kawo musu itane amatsayin abokiyar debe kewa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button