UBAYD MALEEK Page 11 to 20

Kallon afian yasake Yi tareda Dan sassauta fuskarsa batareda murmushin yafito dukaba yace”
Akwai abokiyar zama da debe kewa da Kaleb zai Aiko muku da ita ta musamman Dan haka karku damu damuwa ya qare ok??””yafada Yana shafa kan farhat dake kusa dashi tana cin pancakes da Zuma.
Cikin tsananin murna afia tace”
Dad daga delah ne za’a kawo Mana ita?
Gyada Mata Kai yayi cikin Jin dadin ganin farin ciki akan fuskarsu yace”
Yes my angels Dan haka kunada baquwa yanzu Dan haka no worries no sad face no complains.
Yes dady” farhat ta fada tana riqe hannunsa suka miqe tare suna barin dining din Dan yanzu haka yauma tafiya zaiyi zai Kwana biyu acan.
Har mota suka rakasa ya tafi dayake yau weekends ne ba school Yana wucewa suka dawo ciki cikin farin ciki sukaje suna fadawa mum Sarah sunada baquwa tananan zuwa.
Yana barin gida direct airport aka nufa dashi ya Jima Yana tunani kafin ya dauki wayarsa dake gefensa ajiye ya lalubo numbern jekadin kakarsa wadda yasan itace maganar negestati take gurinta Kira daya tana ganin me Kira ta daga cikin tsananin girmamawa hadda durqusawa duk da ba agabansa takeba tahau jero gaisuwa Yana sauraronta kafin ya dakatar da ita ta hanyar amsawa a gajerance cikin nauyin murya kai tsaye yace tanason bayani akan negestatin Nan tahau jero Masa asalin NURU da sunanta dakomai akanta cikin gajiya da zancen ya katse Kai tsaye yace”
Kada su afia su taba sanin waccece ita da matsayin datazo dashi.
Angama MALEEK ubayd sarki me kujerar delah gizah.
Yana kashe wayar ya kasheta gabaki daya tareda ajiyewa Yana daukar iPad karanta wani saqo.
Suna Isa airport ba Bata lokaci yashiga jet suka daga.
Sukuma a washe garin aranar jirginsu ya sauka qasar Kai tsaye babbar mota tazo daga gidan daukarsu daga ita sai jekadi ne Dan haka suna isowa makeken gidan na UBAYD MALEEK aptrmt dukkanin masu aiki suka fito suna musu barka da zuwa akai ciki dasu suna shigowa babban palon gidan dayasa NURU Shan jinin jikinta sukai kicibis dasu afia dasuka fito tarbonsu afia na ganin NURU ta tsaya cak tana kallonta cikin yanayi na Jin dadin wannan ai qawace ma aka kawo Mata tasaki fuska sosai tana cewa”
Jekadi wannan ce wadda zata tayamu zaman?
Da sauri cikin girmamawa jekadi tace”
Eh ranki ya dade itace.
Jin haka farhat ta riqo hannun NURU tana cewa”
AFIA tanada kyau sosai kaman Barbie Dina ko???
NURU bayan zare ido Babu abinda takeyi tana kallonsu hankalinta nakan gidan Wanda yasa taji tsoron duniyama gabaki daya na shigarta.
Dakin mum Sarah jekadi tasauka itakuma NURU dakin AFIA afian tajata tana sake tambayar sunanta duk Dadi ya isheta sbd take taji tanason NURUn.
##MAMUH*
HASKE WRITERS.
_ZAFAFA BIYAR_????????????
_SAFIYYAH HUGUMA_
_BILLYN ABDULL_
_MISS XOXO_
_HAFSAT RANO_
_MAMUH GEE_
_DUKA KUDIN WANNAN DADADAN BOOKS DIN SUNA KAN FARASHIN NERA 700. WATO KUDIN PAGES KENAN. DOCUMENTS IDAN AN KAMMALA SUMA KUDIN SU DABAN.._
Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????????
0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????????
*_08085405215_*
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????????
0903 234 5899
*_Mamuhgee 8_*
Zaune suke a dakin farhat kan kujera tana gyara Mata gashinta da aka gama wankewa farhat din na kwance jikinta tana Mata surutnda fiyeda rabi Bata gane komai saidai kawai ta murmusawa wata kalmar turancin Idan tajita banbarakwai itama farhat wani lokacin ganin turanci bawa NURU daria yasa idan suna tare turancin take Mata Kuma so take ta iya saboda tanason NURU taringa Bata labari Amma sbd rashin turancin sai ba dama.
Afia ce tashigo tana neman NURU ta qaraso ciki tana kallonsu tace”
Zamu fitan shine Kika jawo aikin gyarawa farhat gashi,
Ki aje idan mundawo a qarasa inason mu biya wani gurin ne daga can.
Riqe hannun NURU farhat tayi tana marairaice fuska tace”
Lewa zanbiku.
Kallonta NURU tayi tareda sakin murmushi tana daure Mata gashin guri daya tace”
Ki tambayi AFIA idan zataje dake to Nima Kinga rakiya zanyi.
Kallon afian sukai duk su dukan atare da sigar roka tayi saurin girgiza Kai tana cewa”
No.
Please AFIA zanje.
Girgiza Kai tayi tana kallonta cikin kulawa tace”
Farhat zamuyi yamma acan sanyi zai sauka kinsan Kuma bakyason sanyi da yawa so ki zauna gida muje mudawo.
NURU Jin tayi kaman tace zata zauna da farhat din ta janyota tana shafa gaban gashinta tace”
Zamu dawo da wuri Inshallah kinji kadaki Bata fuska.
Daki NURU Takoma ta sanya doguwar rigar datafi ta jikinta budewa da daura gyalen rigar akanta sbd su daura sukeyi suka fito afia na sanye da dogon jean da riga me tsayi har qasa saidai gefenta a tsake yake inda ake ganin dogon jean din.
Har jikin mota farhat ta rakosu tana riqeda hannun NURU har suka shiga mota suka fice.
Sai dare suka dawo lokacin farhat harta fara bacci jikin mum Sarah tana jinsu tataso da gudu ta fada jikin afia tareda riqo hannun NURU dake gajiye sbd yawon dasukai na gurare neman wasu text book na afian Kuma sukaje saloon akaiwa afian gyaran qafa itama hadda ita kanta.
Direct daki suka nufa afia tafara shiga bayi alwala kafin tafito itama tashiga tayo wanka tareda alwala tazo kusan atare sukai sallah suna gamawa afia tafara wucewa cin abinci kafin NURUn tabiyota abaya tareda farhat dataketa tambayan Ina da Ina sukaje.
Kamar ko yaushe ita tafara gamawa Amma sbd afia Bata gamaba Bata miqe ba Dan ganin kamar rashin girmamawa ne wa afian datake kamar shugabarta na matsayi.
Saida afia tagama suka miqe dukkaninsu sukai daki afia dakinta ta wuce ita Kuma NURU farhat ta raka dakinta ta sauyo Kayan bacci takaita tayo brush suka dawo dakinsu ta kwantar da ita gefen afia kan gado kafin itama tadawo kujera ta kwanta tana rufe idanuwanta sbd afia tuni tafara bacci Dan agajiye suke.
Washe gari dad dinsu zai dawo Dan haka gidan a natse yake anata gyara da girkin ire iren abincin da akasan su yakeci Dan shi mutum ne da bai cika cin abinci me maiqo ba ma’ana soyayyan Abu bai damesaba kodai dafaffe ko Wanda aka gasa.
Cikin farin ciki farhat take da dawowan dadynta hakama afian Dan haka da wuri tadawo school yau sbd tasan tareda dad din zasuci lunch Dan baya tafiyan dare yawanci da wuri yake dawowa idan yayi tafiya musamman irin wannan daya Dade.
Qarfe biyu da rabi da mintuna hudu jirginsa ya sauka suna zaune a babban Palo suna kallon wani film da NURU afia ce ke fassara Mata me suke cewa tana gyada Kai ahankali sbd kallonma kaman na dolene takeyi afiance ta sakata zaman dole Amma ita tafi Jin dadin zaman daki.
Sunajin diran motan isowanshi da sauri suka miqe farhat da gudu tayi kansa tana Kiran sunansa tana Isa yayi sama da ita Yana sake Mata wani irin murmushin daya kusa sumar da NURU data Dan waiwayo setin qofar idanuwanta suka sauka kanshi da sauri ta dauke kanta daga gurin tana sauke Kai tayi saurin miqewa tana barin palon tsoro na mamaye zuciyarta Dan tabbas laifine yiwa jinin sarautar delah kallon quri bareshi dayake maleek guda na delah gizah Dan haka hanyar daki ta Kama har qafafunta na Dan hardewa sbd tsoron kallon datai Masa Wanda takasa gane laifin ne ya tsoratata kokuwa.