UBAYD MALEEK Page 11 to 20

Tana shiga daki toilet ta wuce tana shigewa ta rufo.
Afia ma riqo hannunsa tayi tareda dorawa a goshinta tace”
Dehina metahi ya abal(barka/sannu da dawowa mahaifina)
Kallonta yayi da fararen idanuwansa masu maiqo aciki wani boyayyan annurin ganinta cikin nutsuwa data samu na bayyanuwa cikin ransa ya bude Baki cikin muryarsa me Dadi da sirkin mulki da iko na Koda yaushe yace”
Da akwai wani sirrin wannan boyayyan farin cikin danake gani akan fuskan AFIA UBAYD MALEEK ne?
Wani murmushin farin ciki tasaki suna yowa cikin Palo tace”
Sirrin na farin cikin dawowan abal din afia ne.
Daddy bana dawowankane ba kawai AFIA tasamu best friend yanzu tana surutu da NURU acikin gidan Nan Amma daddy nidai NURU tawace sbd tanada girma irin na AFIA ne suke friends.
Kallon bakin farhat din yayi Yana sauketa cikin palon yace”
Hmmm farhat inaga you are the talkative anan.
Masu aikin gidan ne suka jero mum Sarah ce agaba suka rurrusana suna Masa barka da dawowa cikin tsananin girmamawa batareda kowannensu ya dago Kai ba ya daga musu Kai kawai suka juya suka bar palon Wanda idan ba aiki suka shigoba Babu me shigowa sai mum Sarah.
Har sama farhat tabishi ita Kuma afia ta ja luggage dinsa tabishi dasu iyakacinsu Palo qaida Babu me shiga master bedroom dinsa sai matarsa lailah Dan haka kosu ‘yayansa Basu taba shigaba bare Susan Yaya yake.
Suna saukowa daki afia ta nufa inda tasamu NURU zaune tana kallon window inda take hangen library din karatun su AFIA sai datazo Nan takejin tabbas Ashe ilimin boko me yawa yanada amfani tunda gashi yanxu acikinsu Takoma tamkar wani kurman dabba da magana saidai a kwatanta Mata sbd duhun rashin ilimin bokon.
Dafata AFIA tayi tana cewa”
NURU Baki zo kinyiwa dad barka da dawowaba gashi harya shige se yafito cikin abinci Kuma.
Waiwayowa tayi ta kalli afian tareda dauke kai tace”
Darajana bekai naje gabansa harna tsaya na gaishesa.
Murmushi kawai afia tayi tana nufar mirror tace”
NURU kinason dakusar da darajanki anan gidan meyasa haryanxu kinkasa sakin jiki damu ki kulamu da qaunarmu yanda muke jinki?
Farhat na Miki kallon ‘yar uwa Kamar ta jini Amma koyaushe kina Mata abubuwan dakesata tuna akwai banbanci me girma a tsakaninku,
Nayi iya duk yanda zanyi Nima ba nuna Miki irin qaunar damuke Miki mundaukeki ‘yar uwa Amma Sam kinkasa sakewa Dani Nima meyasa?
Ko bakyajin dadin zama damu ne?
Rayuwanmu be Miki bane?
Tsoro NURU taji na shigarta na maganganun afia din ta juyo ta kalleta tana girgiza Kai tace”
Wlh ko daya Babu wannan sabo ne kawai matsalata inada wuyan sabawa da waje Amma wlh inajin farhat kaman meryam Babu wani abu dabaiminba anan hasalima wani irin girmane kukedashi aguna Wanda yasa bazan iya sakewaba sbd tamkar rashin girmamawa ne.
Ahankali Afia ta dawo takama hannunta tana cewa”
Karna sakejin wannan zoki rakani gurin karatu daganan zanfara koya Miki turanci.
Binta tayi zuwa libry dinsu dakeda wani irin girma da tsari da kyau ga littafai ko wani shagon Saida shagon littafan albarka.
Zama sukayi akan wasu kujeru masu kyau da taushi AFIA ta dauko wani littafi tana ajiyewa gaban NURU tace”
Kiyi kallon zanen dake cikin wannan littafin kafin nagama karanta wani abu cikin wannan littafin na hannuna idan nagama zanfara koya miki.
Karba tayi boyayyan murmushi na bayyana kan fuskarta Jin Wai tayi kallon Zane tsabar toshewar kanta kenan kaman wata yarinya kamansu meryam.
Budewa tafarayi tana kallo aikuwa zanen ne aciki na dabbobi da sunayensu irin su biri,doki,Kare,mage,zomo hardasu bera abin saiyaso Bata dariya ta murmusa harsaida haqoranta suka bayyana AFIA na lure da ita itama sai yanayin NURUn yasata boyayyar dariya.
##MAMUH#
_ZAFAFA BIYAR_????????????
_Alkiblah–SAFIYYAH HUGUMA_
_Makauniyar qaddara–BILLYN ABDULL_
_Dalaal–MISS XOXO_
_Mabudin zuciya–HAFSAT RANO_
_Ubayd Maleek–MAMUH GEE_
_DUKA KUDIN WANNAN DADADAN BOOKS DIN SUNA KAN FARASHIN NERA 700. WATO KUDIN PAGES KENAN. DOCUMENTS IDAN AN KAMMALA SUMA KUDIN SU DABAN.._
Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????????
0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????????
*_08085405215_*
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????????
0903 234 5899
*_Mamuhgee 9_*
Sun Dade a can Saida afia taduba agogo taga lokacin fitowan dad dinsu yayi yasata aje karatun tana kallon NURU data dage tana kallon dabbobin duniya wainda wasu batama taba sanin akwaiba bare ganinsu sai take kallon abin cikeda mamaki da burgewa fuskarta ma ta nuna hakan
Afia ta dafa littafin tana cewa”
Ma’am Muje saikuma gobe mudawo ki Dora daga inda Kika tsaya.
Murmushi NURU tasake tana cewa”
Inason sanin sunayensu duka.
Karki damu ko farhat zata koya wannan yanxu dai muje inajin yunwa.
Fitowa sukayi NURU nasake wanyewa da qaton gidan sbd saiyau tun zuwanta ta fito ta zagaya cikinsa AFIA kuwa sai sake Mata bayanin komai takeyi tana nunnuna Mata.
Suna shigowa MALEEK UBAYD na gab da shigewa dining room tareda farhat dake gefensa cikin sauri AFIA tace”
Dad NURU na gaidasheka.
Jin haka yasa NURU saurin durqusawa muryarta na rawa tace”
Barka da fitowa cikin yarensu sbd a rikice take batasanma wane kalar yare shi yakejiba ko yake amfani dashi.
Batareda ya juyoba ko ya tsaya ya daga Kai tareda qarasa shigewa yana fiddo hannuwansa dake zube cikin alhijun qananan kayan dake jikinsa na _Stuart weitzman_ dark blue dasuka fiddo hasken fatarsa da asalinsa.
Miqewa NURU tayi kanta aqasa ta nufi hanyar qarmin Palo dazata Kai dakinsu ta shigewarta Dan tasan bama abune me yiyuwa cin abincinta dasu afia ayau.
Itama afian bayan wucewan NURU Bata damu da cewan tazo cin abinci ba sbd ba abune me yiyuwaba cin abinci a table daya da maleek ubayd idanba su ‘yayansaba to saidai matarsa ko iyayensa ko ‘yan uwansa akwai wainda baya yiyuwa cin abinci table daya dashi Dan haka ta wuce dining room din tareda kallon Fana tace idan tagama serving dinsu ta hada abinci a tray akaiwa NURU daki.
Sunci abinci sungama yakoma sama inda suka bisa suka zauna palonshi Dan Basu lokacinsa na magana Jin idan da akwai wani abin saidai duk Rabin zancensu na NURU ne Wanda yasashi mamakin irin shaquwan qanqanin lokaci dasukai da qaunan dasuke Mata Wanda yasashi Jin ai shikenan tunda sunsamu wadda suke so yanxu yasamu Daman kansa tunda inshallah hakan ya nuna ba damuwa yanxu ataredasu musamman AFIA dama ita farhat tuni Bata damu da tafiyan mum dinsuba sbd batasan me hakan ke nufi takamaimaiba.
Koda afia tashigo daki NURU na sallan la’asar itama toilet ta wuce Dan alwala.
Ahankali ahankali Afia tafara saka NURU sakewa dasu sosai tana dariya yanxu acikinsu,tana iya kwanciya akan akan gado daya da afia tareda farhat a tsakiyansu wadda itama shaquwanta da NURUn ya ninku fiyeda farko.
Duk wani aikin gidan ahankali tafara sabawa da saka hannunta musamman bangaren girki da sosai take tayasu Dan tana son iyawa hardai bangaren baking hakama gyaran dakinsu Dana farhat tuni ta karbe itakeyi sai hakan yasake janyo Mata qauna da masu aikin,
Duk wannan hidimar datakeyi a gidan bata sake hada hanya dako inuwar dadynsu ba bare ganinsa dama idan Yana Nan masu aiki basa wilgewa to dama ita tasan Babu wani banbanci matsayi tsakaninta da masu aiki shiyasa itama idan Yana gida tana daki ko library gurin karatun da afia ke koya Mata Wanda ba laifi tana Dan fahimta.