UBAYD MALEEK Page 11 to 20

Ahaka lokacin yaqara cigaba da ja sosai tuni sauyi yashigo rayuwarta ta sauyin jiki da lafiya tareda fara ilmantuwa Dan kuwa turanci yanzu kaman yaqi haka take gwamadawa suna dariya ita dasu musamman idan tanason bada labarin Abu to ko Yaya yazo watsoshi takeyi ganin hakan yasa AFIA yanke shawaran yiwa dad dinta maganar son asaka NURU makaranta Dan ita dake koya Mata yanzu karatunta yafara daukan zafi tana buqatan maida hankali.
Lokacinda tayiwa dad din maganar Kai tsaye yace tafadawa Omar babban amintaccen yaronsa.
Aikuwa tana yiwa Omar waya Babu Bata lokaci aka nemawa NURUn admission a wata school dake kusa datasu farhat inda zata fara daga farko.
Da farko taso zamewa zuwa makarantar sbd ganin kaman samun damar yayi yawa saida afia ta takura Mata tareda Bata qwarin gwiwan yin karatun tareda kwadaita Mata future me kyau na masu ilimi.
Ranar farko data fara zuwa daqyar ta iya bawa kanta qwarin fahimtar kalmar da ake fada Amma haka tadawo Bata wani fahimci komaiba shiyasa a salube tadawo driver na ajeta tana shigowa daki ta wuce ta zube kan gado kife tana sauke ajiyar zuciya tace”
Afia zakuyi hasaran kudi ne kawai banasaka ran kaina zai iya daukan karatu irin wannan.
Koda aka dauko farhat daga makaranta tana dawowa taga NURUn da gudu tayo kanta tana cewa”
My Lewa ‘yan makaranta.
Dariya kalman tabawa NURU ta jawota tana zare Mata school bag daga bayanta tana cewa”
Farhat lewanki kanta a toshe yake kidaina murna ma tun wuri.
Kumatun NURUn dakeda laushi suke burge farhat ko yaushe su farhat din ta matsa tana cewa”
Lewa bazatayi kyan banza ba zata zama me qoqari nasan wata Rana lewa zata zama abin mamaki.
Murmushi tayi tareda kissing goshin farhat din tana cewa”
Kinada yadda sosai haka akan zan iya?
Yes beauty Zaki iya daddy ma zai jinjina Miki sbd qoqarinki zai siya Miki duk abinda kikeso sbd daddy nason me kokari a school sosai.
Murmushi kawai tayi tareda Jan hannunta zuwa daki Dan tubewa ayi wanka.
Suna dining taba bawa farhat abinci Afia tadawo da sauri ta aje jaka ta qaraso tana cewa”
Fana ki kawo mun cheese cream zanci abinci dashi.
Cikin kulawa take kallonsu bayan ta shanye cup daya da juice tace”
NURU ya school da Dadi ko?””taqarasa cikin tsokana sbd Babu wani alamun school yayi Dadi atareda NURUn.
Kallon afian tayi tareda ‘Bata kyakkyawar fuskarta tace”
Kiyi dariyanki kawai afili.
Dariya afia tayi tana fara cin pasta salad tace”
Sorry babe Zaki sabane ahankali.
Suna gama cin abincin suka koma daki farhat na Taya NURU fahimtar karatun da akayo Mata afia na dariyansu har lokacin sallan la’asar yayi sukai sallah me karatun addinsu yazo Maheer asim suka fito zuwa libry inda acan yake musu karatun.
Sai dare bayan tagama komai ta kwanta tafara tunanin gobe ya zata Kaya Mata a makarantar Kuma da haka bacci ya dauketa asuba nayi ta farka tayi sallah ta tadasu sukai sallah itakuma tahau ayyukan data Saba tareda Shirin abincin farhat qarfe bakwai tayi wanka tazo tasake tadasu bacci sukai dakin farhat akai wanka ta shiryata cikin school wear itama tadawo daki tashirya qarfe takwas suka gama Shirin suka zauna cin abinci 8:10 driver yadaukesu yakai kowacce makarantarta ya ajiye.
Yauma kusan abin da wuya Amma dai sbd saka Rai sai Bata damuba Kamar jiyan data dawo gidama haka afia ta ajeta tana sake maimaita Mata karatun tun Bata ganewa har abin yafara warware Mata tana ganewa har a school dinma sbd kusan tafi kowa girma acikin makarantar Dan kaman primary ce afia kuwa kaman a secondary take ita.
Tun karatu nabata wahala sbd rashin sabo da nauyin da yake Mata hartazo tafara ganewa ta maida himma sosai tareda nacewa karatu saigashi yanzu batajin wahalarsa Sam ahaka har lokacin exams yayi cikin ikon Allah kuwa taci exams din suka Bata Daman wucewa makarantarsu afia Amma aji daya maimakon aji uku da afia take wato last year dinta wadda daga ita sai University.
Dan hutun dasuka samu yabata Daman waya da iyayenta a waya ta hanyar jekadi Wanda yasake faranta rayuwarta tareda sake kwantar Mata da hankali musamman dataji meryam da padima wadda yanzu ruwan soyayyarsu da amed yafara neman qafewa sbd wasu abubuwan.
A ‘yan kwanakin dad dinsu afia na gida Dan haka yanzu ta daina fitowa iyakacin hayaniyarsu a dakinsu ne kokuma a dakin farhat dasuke Zane zanen drowings sbd farhat na tsananin son Zane.
Wanka tafito bataga afia data Bari tana waya da mahaifiyar dad dinsuba ta nufi gaban mirror tana goge jikinta da ruwa ke gangarowa sbd tsantsin fatarta tana duba lokaci tasan suna can sama gurin dad dinsu ta shirya cikin doguwar riga straight designer ta _Alexender McQueen_ wadda taje straight ajikinta ta dauro wata hula Mara nauyi da Bata rufe kanta dukaba sbd tai Mata kadan ta fito ta nufi kicin Dan kamawasu Fana aikin abincin dare.
Sanin suna palon sama tareda dad dinsu yasa tabiyo ta babban Palo sbd hango kaman mum Sarah a palon.
Shigowa tayi gabaki daya palon hankalinta na kan hanyar shigowa da aka bude wani kyakkyawa yashigo sanye da suits farare tsayawa tayi cak tsakiyar palon tana dauke Kai daga kallonsa shikuwa cikin wani irin kyakkyawan murmushi yake kallonta cikeda mamakin wacece wanna agidan yabude Baki zaiyi magana sukaji taku abayansu cikin nutsuwa da Kamala
Da sauri ta juyo daidai Yana isowa daf saura kadan kirjinta ya daki nasa tayi saurin durqusawa qasa zuciyar ta harba da qarfi
Shikuwa kanta dake qasa ya kalla kadan da fararen idanuwansa kafin ya raba ya wuce Jin muryan farhat daga bayansu tana ihun ganin _IMRAN_ NURU na ganin hakan ta miqe da sauri tabar gurin numfashin na kasa daidaituwa dole daki Takoma Dan bazata iya zuwa kicin ahakaba zuciyarta na irin wannan harbawan sbd tsoro
Shikuwa Imran bayan NURUn yabi da kallo cikin basarwa da ya kamo farhat dake tsallan murnar ganinsa tana cewa”
Uncle Imran yaushe kadawo?
MALEEK ya kalla cikin shiga nutsuwa da wani irin kwaijininsa daya cika idanuwansa yace”
Barka da yamma MALEEK.
Zama yayi a kujeransa da Babu me zama Yana amsawa ahankali tareda miqa Masa hannu ya miqo Masa takardun dasukai maganar zai kawo Masa gida.
Karban file din yayi tareda dakatawa daga budewa ya saurara sbd Jin wani qamshi dake fita kadan kadan daga file dinne kokuwa daga jikinsa?
##MAMUH##
_ZAFAFA BIYAR_????????????
_Alkiblah–SAFIYYAH HUGUMA_
_Makauniyar qaddara–BILLYN ABDULL_
_Dalaal–MISS XOXO_
_Mabudin zuciya–HAFSAT RANO_
_Ubayd Maleek–MAMUH GEE_
_DUKA KUDIN WANNAN DADADAN BOOKS DIN SUNA KAN FARASHIN NERA 700. WATO KUDIN PAGES KENAN. DOCUMENTS IDAN AN KAMMALA SUMA KUDIN SU DABAN.._
Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????????
0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????????
*_08085405215_*
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????????
0903 234 5899
*_MG 10_*
File din hannunsa yasake rufewa ya dan kalli bayan file din tareda yamutsa fuska ahankali cikin yanayi na kamshin zai damesa ya bude Kai tsaye yayi signing inda zaiyi ya rufe tareda miqawa Imran din batareda yace komai ba cikin girmamawa Imran ya karba Yana sake Masa bayanin sauran paparworks din dasuke pending.