UBAYD MALEEK Page 11 to 20

Farhat data tashi nata baccin tana fitowa palon taga NURU tayi bacci kan kujera ta kalla kyakkyawar fuskarta datai fresh sbd samun hutu da gyara saita saki murmushi tareda qarasowa zata gyara Mata kwanciya ganin kaman zata fado tana Dora hannunta akanta taji dirin motocin dad dinta yadawo cikeda farin ciki ta miqe ta nufo qofa da sauri ko ta bude tareda rumgumesa cikin qasa qasa da murya tace”
Welcome dady.
Kallonta yayi cikin kulawa da mamakin meya samu muryanta take magana ahankali
Duk da qarancin shekarunta ta dade da sanin dad dinsu ba komai yake budewa Baki yayi magana ba da kallo ma kawai suna gane maganarsa Dan haka ta fahimci mamakinsa tasakeyin qasa da murya cikin rada tace”
Dady Lewa na Palo and she’s sleeping tagaji sosai da yawa koyaushe batada time din hutawa yanzu tasamu tayi bacci please dady kadamu tasheta.
Kallonta yayi suna qarasowa tsakiyar palon dan dama yasan tsawon shekarun Nan farhat Bata mgnar daya biyu saita lewa,my Lewa,my beauty kunnuwansa harsun gaji dajin sunan abakin farhat.
Dan juyi tayi daga kwancen ta sulmoyi zata fado da sauri farhat tayi kanta ta tareta Amma sbd NURUn tafita girma da nauyi saita kasa tareda saima danneta da NURUn tayi batasaniba sbd baccin yayi Mata nauyi sosai Dan tajima Bata baccin kirki Koda daddare.
Da sauri farhat ta kalli inda yake tsaye cak Yana kallon qanqanuwar yarinyar dabatafi AFIA shekaru da girman jiki da komaima.
Cikin wuya farhat tace”
Dady hannuna zai karye aunt NURU nada nauyi sosai.
Cikin wani irin taku da izzar data gama kame jininsa ya iso gurin batareda ya kalli NURUn ba ya Dan ranqwafo yakai dogayen hannuwansa masu siffar qarfi tareda tsananin taushi ya zura qarqashin bayan NURUn farhat tasamu damar janye hannunta tana yarfewa tayi dakinta da gudu tana cewa hannuna zai kumbura Bari nashafa ointment da sauri kada ya kumbura aunt NURU nada nauyi sosai.
Idanuwansa dake raunana kuzarin Wanda duk ya zubawa su ya waiwayo ya zubawa fuskar NURU wadda take wani glowing na zallar asalin kyawun da Allah yayi Mata.
Gangarowa yayi da kallonsa kadan zuwa jikinta a qirjinta ya dakatar da kallon tareda dauke fuska Yana zare hannuwansa daga qarqashinta yabar gurin sai ayau yasan babban shirmen da Kaleb ya tafka da jekadi kenan tsarar ‘yar cikinsa suka kawo Masa amatsayin negestati,
Ta Yaya suke tunanin wannan yarinyar tsarar afia zai iya hada shimfida da ita?Tama Yaya zata iya daukan nauyinsa ko ciki baya tunanin kwsmkesonta zai iya dauka bare haihuwa… unbelievable” yafada cikin zuciyarsa a ‘dan takaice sbd tunano ‘yarsa afia dake tsararta baya tunanin ko Nanda shekara biyar zai aurar da ita Dan ganin kaman tayi mugun qanqanta amma shi ba saurayiba ko ‘dan samari akawo Masa wannan.
##MAMUH#
Share this
[ad_2]