UBAYD MALEEK 1-END

UBAYD MALEEK Page 21 to 30

Mirror dinsa tamaida ido akai girmansa yasata juyowa gaba daya tana kallon kanta aciki ta yanda take firgice.

Komai na dakin fari ne shima Kuma komai tsaf tsaf yake ba wata qura sbd ba gurin shigowarta kamar dai akwai mutum aciki kullum.

Qamshinsa ne dai wadda tafara haddacewa sbd tsoro shine yake tashi takowane lungu da saqo na dakin.

Cikin sauri da gaggawa tahau aikin daya shigo da ita take ta gyare komai tsaf tareda wanke toilet ta goge ta kunna AC da turaren daki dake fita ahankali sbd Bata budeshi duka ba kadan ta bude ta yanda kamshin zaifi bada nutsuwa sbd kadan kadan yake fita Kuma saiya Jima kafin ya feso kadan din.

Gadonsa ne kawai batayi gangancin ko tabawa ba sbd sanin hukuncin laifin hakan Dan ko yau da a delah ne ko gizah Allah ne kawai yasani idan zataga safiyar gobe sbd mugun babban laifine ganin makwancin asalin jinin DELAH bare MALEEK guda matuqar ba negestatinsu ba ko matayensu Suma sbd sune abokanan kwanciyar tasu Dan haka kallo daya tayiwa gefen gadon Bata kumaba harta gama ta fice dakin zuciyarta na sake shiga rudu.

Tana fitowa palon tahau tattare kayan biscuits da drink dinda takeci tayi kicin dasu tasake tattara palon ta gyara hakama cikin take tahau gyaransa takuma Dora Masa abincin daren dazaici.

Sanin kalolin abincin dayakeci yasata hada Masa gasashen flat bread da boiled veggies aciki sai ruwan lemon tea masu zafi da qamshin lemon leafs da ginger takawo dining ta jera ta bar palon gabaki daya ta shige daki ta rufo Dan batasaka ran zata sake dogon motsiba a gidan har gari ya waye yatafi.

Yakai mintuna talatin Yana wayar dayake Yi kafin ya kammala tareda kashe wayar gabaki daya ya nufi hanyar master bedroom dinsa dinsa yashige Kai tsaye tareda rufowa.

Wayar hannunsa ya ajiye gaban mirror ya nufi closet dinsa ya rage kayan jikinsa duka ya daura brown towel a qugunsa lafiyayyan fatarsa da hutu da kulawa yagama bayyana atareda ita Kamar ta sabon saurayi me sabon jini ajika.

Babban toilet dinsa daya kusa girman dakuna biyu yashige.

Bayan fitowarsa yayi duk abinda zaiyi ya Sanya fararen kayan bacci masu Dan kauri na _roughbay_ da socks din sanyi a qafafuwansa yazuro slippers yafito dining tea din kawai yasha sai rolled flat bread din guda daya yasha ruwa kadan ya koma daki yayi brush ya kwanta tareda Jan duvet cover take qura ta Dan tashi sbd Bata taba komaiba na gadon bare kakkabewa da sauya su bedcovers.

Muguwar shaqa yayiwa kurar wadda zai iya cewa tun Yana yaro rabonsa da shaqar Kura irin hakan sbd mummunan attack din datake basa take yafara tari ahankali ahankali Yana rufe hancinsa da bakinsa ya yaye bargon gaba daya Wanda yasa qurar sake tashi take tarinsa yafara qarfi idanuwansa na fara sauyawa ya sauko da qyar numfashinsa na sauyawa da sassarqewa ya isa gaban mirror ya lalubo wayarsa ya kunna zuwa lokacin yafara samun attack Dan kuwa numfashi yafara dauke Masa Kiran Mr Omar ya Danna daqyar ya iya furta”

My inhaler…..

Yana fadar hakan ya saki wayar Yana durqushewa agurin cikin tsananin azabar toshewar numfashi da wani irin zufan wahala daya jiqasa cikin qanqanin lokaci.

Mr Omar najin muryar MALEEK da abinda yafada yasan attack ne zai samu a rikice yabude inda ake aje inhalers dinsa cikin duka motocin dayake hawa ya ciro jikinsa har wani rawa yakeyi da gudu ya nufo ciki tsabar sauri da rikicewa ko lift kasa tsayawa shiga yayi ta staircase yabiyo Yana hada stairs uku uku gurin hayewa.

Danna doorbell yake ba kakkautawa Wanda yasa NURU dake waya da Imran akewa ba shiri ta fito sbd gudun ‘karar ta damu MALEEK.

Kayan bacci ne ajikinta qaramin guntun wando da rigarsa Mara hannu Dan haka saita sanyo doguwar kimono akai ta riqe gaban ta fito da sauri ta bude tana cewa”

Please stop ringing the bell Ina zuwa.

Tana budewa taga mr Omar ciki mamaki take kallonsa kafin tayi mgn ya dunguro Mata inhaler din cikin gaggawa yace”

MALEEK yasamu attack na asthma kiyi sauri ki Kai Masa idan yayi nisa ki shaqa Masa please go go go fast.

Karba tayi ta juya arude sbd ita duk Mr Omar dinne ya rudata ta yanda yake maganar dukkanin jikinsa na wani irin rawa ga tsoron shiga dakin na MALEEK Yana ciki Amma haka ta Isa arikice ta bude tashige qofar na rufewa shima Mr Omar Jan qofar yayi yakoma gefen qofar shiga palon ya dasa sabon zama.

Tana shiga yana qoqarin zubewa kwance batasan lokacinda ta qarasa da sauri ba cikin tsoro da rudewa ta tarosa dayake batada kauri sosai da qarfinda zata iya taresa musamman da jikinsa yariga yasaki sai takasa suka zube kan gadonsa gabaki daya.

##MAMUH#

_ZAFAFA BIYAR_????????????

_Alkiblah–SAFIYYAH HUGUMA_

_Makauniyar qaddara–BILLYN ABDULL_

_Dalaal–MISS XOXO_

_Mabudin zuciya–HAFSAT RANO_

_Ubayd Maleek–MAMUH GEE_

_DUKA KUDIN WANNAN DADADAN BOOKS DIN SUNA KAN FARASHIN NERA 700. WATO KUDIN PAGES KENAN. DOCUMENTS IDAN AN KAMMALA SUMA KUDIN SU DABAN.._

Ɗaya___300

Biyu____400

Uku_____450

Huɗu____500

Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????????

0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????????

*_08085405215_*

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????????

  0903 234 5899

*_Mamuhgee 14_*

Kokuwar tashi takeyi daga kan gadon dukkanin jikinta rawa yake sosai sbd tsananin tsoro da tashin hankali tareda ma firgici duk ta gama rudewa Amma sbd jikinsa yasaki gabaki daya ko kadan takasa motsashi daga jikinta sai numfashinsa dake qoqarin barin qirjinsa da sauri ta lalubo inhaler din dake hannunta ta dago kansa daga qirjinta dake harbawa ta Dora cikin bakinsa ta Danna harso biyu zuwa uku taga kaman Yana responding saita sake daddannawa tana shafa bayansa ahankali kaman yanda takewa farhat tana dan hura Masa iskan bakinta a fuska har lokacin jikinta rawa yake sosai sbd fadar tsoron datake ciki baya misaltuwa ganinta kwance kan gadon da za’a iya raba gangar jikinta da kanta akan laifin hakan.

Wata irin rawa jikinsa ya dauka kamar Yana fizga sosai Sosai take hankalinta yayi mummunan tashi ta turesa gefe daqyar daga kanta ta tashi zaune tana gyara Masa kwanciya hannuwanta na rawa ta fara Kiran sunansa da DADDY cikin masifaffen tashin hankali ganin Yana jijjiga da qarfi.

Da gudu ta sauko gadon tana wurgi da kimonon jikinta ta fita da mugun gudu ta dauko wayarta hannunta na rawa daqyar ta iya riqe wayar ta Nemo sunan Dr Damien ta Danna Masa Kira tana dawowa dakin da gudu cikin firgici take koro Masa bayani muryanta na rawa tuni zufa yayi Mata sharkaf.

Cikin son Samar Mata nutsuwa Dan ta fahimci bayaninsa yace”

Ki kwantar da hankalinki please ki fahimci abinda zanfada miki.

Jijjiga Kai tayi tana saurarensa cikin qaguwa tana sake hada zufan tashin hankali ko qarasa sauran bayanin baigama yiba tayi cilli da wayar ta nufi gaban madubi tafara dudduba allaurar da Dr Damien din yace 

Bata ganiba tahau bubbude drowers cikin tashin hankali take na rashin ganin allaurar 

Tayo gurin luggage dinsa ta bude tahau yamutsawa cikin sauri da tashin hankali cikin sa’a kuwa ta ganta da sauri tayo kansa tana zuwa kaman yanda Dr yace tayi ta Zuqa Masa allurar take yasaki wani wahalalle numfashi dukkanin jikinsa na sakewa numfashinsa ya tsaya cak ya daina motsi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button