UBAYD MALEEK 1-END

UBAYD MALEEK Page 21 to 30

Dauke wuta tayi itama ganin baya numfashi baya motsi a kidime ta haura gadon ta taba kirjinsa taji baya bugawa ta Dora kunnenta kan kirjin nanma taji tsit a haukace ta daga qafafunsa ta Dora kan cinyarta ta zare Masa safunan qafan tasaka tafin hannunta tana gogawa da qarfi tanayi tana kallonsa adduo a bakinta har batasan wainda takeyiba 

Ahankali ahankali taga numfashinsa yafara dawowa ahankali 

Wata irin wahalalliyar ajiyar Zuciya tasake sai alokacin hawaye suka gangaro Mata har batasan lokacinda ta qanqame qafafuwansa dake kan cinyartaba tana sake kukan tsananin tsoro da ace wani abu yasamesa Yaya zatayi?

Me za’ace?

Me ‘yayansa zasuce?

Ta Jima ahaka tana kukan kubuta daga muguwar masifar data tashi afkowa zuriarta gabaki daya kafin ta Dan dago ta kallesa da jajayen idanuwanta taga yanzu Kam numfashinsa yagama daidaituwa Amma bai tashiba sai hakan yasakata Jin shakka ta gyarawa dogayen qafafuwansa zama akan cinyoyinta dake filin Allah,

Jikinta daya gama daukan dumin tashin hankali yafara shiga qafafunsa gakuma tafin qafafunsa datake gogawa da tafin hannunta ‘Dan dumi yaringa shigar qafafunsa yasashi motsawa ahankali a wahalce batareda ya bude idanuwansa ba 

Itakuma taci gaba da gogawa Wanda Dole yasashi bude idanuwansa dasukai ja a wahalce ya kalleta daqyar ya maida idonuwan ya rufe Yana sauke wani numfashin me fitarda siririn sauti.

Bata ankara daya Dan farfado ba taci gaba da goga Masa tafin qafafun 

Ya sake bude idanuwansa a wahalce yanason cewa ta daina ya kasa sbd hakan datake Yana Masa wani iri temperature dinsa tana hayewa sama Amma yakasa mgn sai kawai ya maida idonuwan ya rufe bacci ya daukesa me qarfi a wahalce.

Qarfe bakwai na safe yabude idanuwansa ahankali Yana furta sunayen Allah da adduar tashi bacci cikin zuciyarsa,

Motsawa yayi ahankali tareda yunqurawa zai tashi zaune yaji qafafuwansa a riqe ya Kai idanuwansa zuwa gabansa yaganta kwance rungume da qafafuwansa baccin wahala ya dauketa.

Kallo daya yayi Mata ya dauke idanuwansa daga gurin Yana zame qafafuwansa ya zuro qasa tareda yaye labulen makeken gadon ya fito Yana tafiya ahankali duk da garau yake Jin kansa ba damuwar ciwo ko daya Amma akwai rashin qarfin jiki ya nufi toilet yashige.

Harya fito tana baccin Bata farkaba Dan haka Kai tsaye ya shirya cikin Ash Armani’s ya fesa turarensa na imperial majesty rosalle ya saka takalmin _manolo blahnik_ ya fice Kai tsaye Yana kunna wayarsa ya Kira mr Omar daya kwana zaune zaman jiran yazata Kaya yana ganin Kiran maleek yayi wuf ya dauki Kiran a qage yace”

Good morning MALEEK.

Ka kunna mota ganinan fitowa.

Da gudu mr Omar ya sauko ya nufi mota yashiga ya kunna da sauri tareda gyara parking yayi saiti daidai kofarda maleek din zai fito 

MALEEK din nafitowa ya bude Masa yashiga ya rufe ya zagaya da sauri yashiga suka wuce.

Qarfe Tara da mintuna ta bude idanuwanta dasukai mugun nauyi sbd kukan datasha dakuma bacci 

Tafara jujjuya idanuwan taga inda take a zabure ta miqe jikinta na rawa ta wuntsulo qasa tana kallon gadon taga bayanan da sauri ta fito cikin gadon har tana tuntube ta fice ko ganin gabanta batayi Takoma dakinta jikinta na rawa.

Daqyar ta nutsar da kanta Dan yin sallah tayo alwala tazo tayi sallah zuciyarta na harbawa da qarfi 

Kallo daya zakai Mata kasan a firgice take takasa samun nutsuwa tana zaune a daki tana tunane tunane har kusan 12 tayi Dole ta fito Takoma dakin ta dauko wayarta sai alokacin taga misscals din Imran da text din Mr Omar na cewan sun wuce komawa Paris MALEEK zaiga likita.

Ajiyar zuciya ta sauke duk da bawai tasamu nutsuwa bane dajin hakan sbd ita yanzu qaddarorinta yawane dasu yanzu dame zata Kira qaddarar datakaita hawa gadon MALEEK na DELAH Giza Wanda ko ‘yayan sarauta bila adadin ba kowane yaga ko gurin zaman Shan iskansaba gata tsautsayi da qaddara yasata ganin makwancinsa dako ‘yayan cikinsa Basu taba ganiba Dan daga afia har Farhat Babu Wanda yataba shiga bedroom dinsa nako Ina Bare suka shimfidar kwanciyarsa.

Kiran Imran ne ya katse damuwarta da tunaninta sbd rashin daukan wayanta tun jiyan yasashi shiga damuwa Dole ta Dan sake suka hau magana sama sama qarshe dai Dole hakura yayi da wayar akan tayi bacci ta huta zai kirata zuwa anjima danma Bata fada Masa abinda yafaru ba bakuma tajin zata taba iya fadawa kowa har abada.

Wanka tayi sai alokacin yunwar dake cikinta tun ta jiyan ta taso Mata ta nufa kicin ta dumama sauran abincin dabaiciba jiyan taci Tasha orange juice Takoma daki sai alokacin takira Afia suka hau fira itama sama sama harsaida afian tagane tace”

NURU are you sure you’re okay???

Numfashi ta sauke kafin tace”

Eh kawai ciwon Kai ne ke ‘dan damuna shima sbd I didn’t sleep well last night ne.

Ok tom kiyi bacci yanzu Koda na 1 hour ne you’ll feel good inshallah.

Aje wayar sukai ta kwanta Dan tasamu tayi baccin Amma Sam takasa har lokacin zuciyarta Bata cikin Dadi qarshe jekadi ta Kira taji lafiyan iyayenta tukuna ma tasamu ta ‘dan rintsa baccin ya dauketa.

Bata farka ba sai yamma tana tashi wanka tayi tayi sallolinta ta Sanya riga da guntun wandon jeans baqi ta fito ta dafa kwai da farar noodles taci Tasha ruwa ta dauko ledar crunchy chips chops tazo ta zauna kallo tana ci saiga Kiran Afia ta dauka Nan suka hau waya yanzu cikin sakewa Dan baccin ya taimaketa sosai.

Karatunta yadau zafi sbd tafara exams din kammalawa shiyasa yanzu batada wani lokaci sosai karatu ne a kanta ko lokacin fira ta waya batadashi Dan wani lokacin wayar a kashe take yini saitazo kwanciya ta kunna da afia kawai take waya kafin takuma maidawa ta kashe ahaka ta gama exams dinta kwana uku ta qara akai ta tattaro tadawo gida ranar murna da farin cikin farhat Bata misaltuwa hakama afia datai tsananin kewan NURUn kusan daima kowa yayi kewarta shiyasa ranar gidan kaf acikin walwala suke Dan Jin suke kamar rayuwar gidan tadawo sbd AFIA ko yaushe tana library gurin karatun batada lokacin kowa na gidan 

Farhat ma haka take turata daki tace taje tayi karatu itakuma NURU tana shiga cikinsu tayi aiki harma tayi Wasa da dariya dasu uwa uba idan ta biyewa farhat gurin wasan yara na guje guje ko qasa a playground na gidan Wanda ka zuba komai na wasan yara domin farhat Wanda ita kanta farhat yanzu take morewa playground din data samu abokiyar dake tayata shiriritarta shiyasa yanzu batada kaman NURUnta.

Hutun sati biyu kawai NURU tayi Mr Omar ya kammala komai na karatunsu dazasu fara yanzu na cikan burirrikansu,

NURU lawyer itakuma AFIA likitanci.

##MAMUH#

_ZAFAFA BIYAR_????????????

_Alkiblah–SAFIYYAH HUGUMA_

_Makauniyar qaddara–BILLYN ABDULL_

_Dalaal–MISS XOXO_

_Mabudin zuciya–HAFSAT 

RANO_

_Ubayd Maleek–MAMUH GEE_

_DUKA KUDIN WANNAN DADADAN BOOKS DIN SUNA KAN FARASHIN NERA 700. WATO KUDIN PAGES KENAN. DOCUMENTS IDAN AN KAMMALA SUMA KUDIN SU DABAN.._

Ɗaya___300

Biyu____400

Uku_____450

Huɗu____500

Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????????

0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????????

*_08085405215_*

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????????

  0903 234 5899

*_Mamuhgee 15_*

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button