UBAYD MALEEK Page 21 to 30

Kina magana ne?
Batareda ta juyoba hankalinta na kan littafin datake karatu ita afian tace”
Eh inaga Imran Yana bakin qofane doorbell Yana qara.
Kallon hanyar fita palon zuwa palon farko NURU tayi cikin nazari saidai Kuma dama tasan zaiyi wuya Imran din yaqi dawowa yau din sbd sauyin daya gani tattareda ita dakuma nacinsa akan maganar aurensu.
Zame farhat tayi daga jikinta tareda Miqewa tsaye ta nufi daki ta doro qaramin mayafin doguwar riga akan kayan jikinta ta fito ta nufi qofa ta budu Kai tsaye tareda bude Baki zatai mgnar idanuwanta suka sauka kan Mr Omar dake Danna doorbell din gabanta yayi mummunan faduwa ta saci kallon bayansa daidai isowar MALEEK din sai Imran a bayansa Wanda da gani shima isowarsa kenen mr Omar ya juya da sauri yabar gurin ganin MALEEK ya qaraso,
Take taji qafafunta na neman Gaza daukarta tayi saurin kaucewa daga bakin qofar tana sauke kanta sbd wani irin kwarjini da cika Mata idanuwa dayayi saikuma shedan dake dawo Mata da tunanin abinda yafaru dasu a Vegas sai kunyar al’amarin na bayyanuwa atareda ita Wanda yasata dagowa ahankali ta sake kallonsa daidai kawowarsa daf da ita idanuwanta suka hadu da nasa idanuwan dasuka kusa sata zubewa agurin batasan lokacinda ta bude bakiba da siririyar muryarta tace”
Barka da dawowa.
Akaron farko daya bude Baki ya amsa Mata da”
Yawwa.
Gabaki daya Jin tayi tana neman rikicewa har batasan lokacinda ta rufe qofa da qarfiba Wanda ta daki hancin Imran daya fara shigowaba da qarfi har baisan sanda ya saki qara me qarfiba wadda tasata dawowa hayyacinta da sauri ta bude qofar cikin damuwa da kulawa tayi kansa tana cewa”
Oh my God, I’m so sorry Im banluraba na manta kana baya, please let me take a look”” tafada tana duba hancinsa da harya fara ja abinka da farin mutum ga idanuwansa tuni suka cicciko da ruwa sbd hancin daya bugu sosai.
Rufe hancin yayi Yana cewa”
No karki damu ba wani matsala bane buguwane kawai.
Im dan Allah kayi hakuri bansan meyake damunaba bansan tunanin me nakeba.
Shihhhh ya isa haka just relax sweetheart am fine
Duba kiga hancinma ya sauka.
Fuskar tausayi tayi tana sake kallonsa da alamar ban hkr tace”
Shigo ciki na dauko ointment sai a shafa agurin.
Ki barshi zanje gida zanshafa idan naje gidan kishiga gobe zandawo da safe dama nazo Naga ko kina lafiyane kishiga ciki Saida safe.
Im you sure you’re ok??tafada tana kallonsa.
Murmushi yasakar Mata Yana cewa”
See you tomorrow.””ya wuce.
Saidataga tashin motarsa kafin ta sauke numfashi Mara sauti ta juyo ciki ta rufe kofa tanajin ba Dadi cikin ranta.
Hanyar kicin ta nufa Dan daukan ruwa tana kaiwa dining room ga tarin dibbin mamakinta saitaga maleek zaune akan dining da kayan daya shigo dasu Wanda ke nuni da kaman tunda yashigo Yana gurin bai qarasa samanshi ba kenan ko su afia Basu San da dawowarshiba.
Fatar wuyansa dake sheqi take kallo har zuwa hannayensa data tuno tsananin laushin dasukedashi da sauri ta Kori shedan tareda juyawa zatabar gurin kamar daga sama taji muryarsa me kamewa yace”
Serve me.
Tsayawa tayi cak daga inda take tsaye sbd Bata taba tunanin yasan da tsayuwarta a gurinba,
saidata sauke numfashi ta daidaita nustuwarta kafin ta juyo cikin nutsuwa ta qaraso gabansa a ladabce tasake bude Baki tace”
Barka da fitowa.
Bai amsaba sbd fuskarsa dake kame
Ta matso sosai tareda fara bubbude abincin ta zuba Masa Kamar yanda ta kwatanci zaici ta juya zuwa kicin ta bude fridge ta dauko qaton royal silver jug na fresh fruit juice ta kawo daidai fitowar farhat data biyo bayan NURUn ganin ta dade Bata dawoba daga bude kofar sbd matuqar NURU na gida Bata iya dadewa ba ajikintaba.
Ta kofar Palo ta hango dad dinsu a dining zaune cikin tsananin farin ciki ta qaraso da gudu tana cewa”
AFIA Daddy is back.
Qarasowanta da gudu yayi daidai da tsayuwan NURU a gefensa Dan zuba Masa juice ta fada jikin NURUn da qarfi wadda dama ita kuma ta fada jikinsa gabaki dayanta har ita har jug din juice din daya zube ajikinsu duk su biyun da sauri ta dago ta kalli fuskarsa da idanuwansa suka sauya launi ta kalli kanta datake zaune dare dare kan cinyoyinsa fuskarta da tashi na tsiyayan ruwan juice a rude batama saniba tsaban firgici ta zame qaramin gyalen kanta takai fuskarsa zata goge ya kauce fuskan sai hankalinta yayi mummunan tashi ta sakata tafin hannuwanta masu wani irin taushi ta Dora kan fuskarsa tahau gogewa arude jikinta na rawa Kuma har lokacin tana kan cinyarta.
Ahankali ya bude idanuwansa masu sake rudata ya zubawa hannayenta ya dauke Kai tareda sake kame fuskarsa ya dago hannayensa duka biyun zai janye jikinsa kamar daga sama muryar AFIA ta sauka da cewa”
What’s going on here????
Kallon tsananin mamaki da tsoro tareda firgici da rudewa take musu musamman NURUn dake zaune kan cinyar dad din.
A zabure NURU ta miqe jikinta har Yana rawa ta kalli afia batasan lokacinda ta qaraso gabanta ba tana cewa”
Juice ne farhat ta turo ya zube.
Kota kansu baibiba ya miqe yabar gurin gabaki daya Yana zare agogon hannunsa daya jiqe shima.
##MAMUH#
Share this
[ad_2]