UBAYD MALEEK Page 31 to 40

Tissue ya dauka ya goge bakinsa tareda Miqewa tsaye ya kalleta yace”
Take care princess”ya wuce.
Kasa motsawa tayi kanta na toshewa sbd hakan na nufi zancenta be karbu ba agurin dad dinta sbd hakan da yayi shine rashin amintarsa ga zance idan ankawo Masa.
Miqewa itama tayi tabar gurin Takoma daki ta zauna ta jawo waya ta Nemo numbern mum dinta tafara tunanin takira ko karta Kira,
Fasa Kira tayi tai wurgi da wayar tareda Miqewa tsaye ta sauya Kaya ta fito tashiga mota ta fice daga gidan Dan zuwa dauko NURU datasan yanzu ta Isa gamawa tunda ita yau Bata samu zuwaba.
Tunda suka dawo taketa qoqarin cire damuwarta sbd kada NURU tagane saidai NURUn tana lure da ita saidai batason takura Mata da tambaya sbd batasaniba ko matsalar ta sirrice.
Kwana sukayi ahaka suka Kuma yini ahakan har akai kwana biyu
cikin kwana biyun duk ta Hana kanta sukuni da tunanin al’amarin Wanda take ganin rushewa familynta zaiyi idan wata tashigo cikinsu amatsayin matar dad dinsu ko negestati
Itadaima tafi son iyayenta su shirya koma menene hakan yafi shigowar wata cikinsu.
Ganin dai dagaske AFIA na cikin damuwa me qarfi boye kawai take yasa NURU kallonta bayan sun kwanta tace”
Afia koma menene abindake damunki please ki rage idan bazaki iya ciresaba ko hakura dashiba sbd wannan damuwan naki bamajin dadin ganinki ahaka ko farhat dake qaraman yarinya tafara cewa menene akaiwa AFIA.
Please AFIA kicire koma menene kibarwa Allah a rayuwa dama akwai hakan duk da nasan ke koma menene damuwan ba wani babba bane sbd Babu wani abu najin dadin duniya da Kika rasa Dan Allah ki cire damuwan please baby.
Tunda tafara magana afia ke kallonta sbd wani tunani daya shigota na sha’awar bin dad dinsu gizah Dan koma menene tafison tanacan zatafi samun saukin hanawa kokuma handling maganar rabuwar iyayenta taqi barin ta fita Dan kuwa tasan daga lokacinda maganar ta fita MALEEK na gizah bazai qara awa ashirin da huduba Batareda Matar aure ko negestati ba Dan haka zasu bishi Dan toshe yiyuwar hakan Dan kuwa idan hakan tafaru dad dinta bazai karbi mum dintaba har abada Wanda ita Kuma akan hakan ko kamawa tayi tayi amfani da NURU zatayi Dan Hana wata shigowa rayuwar dad din daidai NURU tayi hkr but she’ll have to use her innocence.
Wani numfashi mara karfi ta saki tareda kallon NURUn cikin kauna da kulawa ta riqo hannunta ta rungume tace”
Thank you my NURU” ta rufe idanuwanta ahankali bacci na daukanta.
Washe gari haka ta tashi cikin walwalarta da sakewarta har hakan yasanya NURU da farhat farin ciki sosai har wasan ruwa da basketball sukai yau da yamma a playground Wanda duk abinda sukeyi dad dinsu na gidan dan haka Koda daddare yau taredashi sukai dinner Banda NURU dataqi fitowa tea kawaima Tasha sbd karatun data duqufa dayi Dan gobe tanada zuwa wani court yin wani aikin 4hours dake cikin karatunta.
Acan dining kuwa AFIA ta sanarwa dad dinta sunason binsa Dan Suma su dubo Anneti.
Kallonta yayi kadan tareda maida kallonsa kan farhat dake cewa”
Yes daddy Nima zanje Kuma zamuje da Aunt NURU ma ko AFIA?
Kallon bakin farhat din dako yaushe yake furta sunan NURU ko lewa yayi tareda dauke Kai Yana goge bakinsa yace su zama ready jibi ne tafiyar.
Cikin murna dukkaninsu sukace thank you dad.
Bayan fitarsa NURU tafara wucewa court kafin afia ita Farhat yau Babu zuwa school dinsu.
Sai yamma sosai suka dawo duk su dukansu Koda ta shigo tana waya da Imran da duk yabi ya sukurkurce Mata da cewan amatse yake da MALEEK yabawa su dad dinsa lokacin zuwa.
Murmushi kawai tayi sbd Bata taba tunanin maleek daya Bata ingantacciyar rayuwa tareda ‘yayansa zai Bata ingantacciyar rayuwa ta har abada ba ta hanyar bada damar azo neman aurenta Dan tunda haryace idan yadawo zai Basu Daman zuwa ayi magana kenan da yiyuwar barinta tayi aure da rayuwar aure kaman kowaba babban mamakinta data kasa yadda dashi shine yau itace tasamu damar ace MALEEK na Delah gizah guda shine da kansa zai bada aurenta tabbas wannan tunanin idan yafado Mata kanta da tunaninta kasa dauka suke.
Ga tarin dibbin mamakinta tana shigowa Palo Imran suka tarar zaune Yana sako Mata murmushi da wani irin kallon Sonta daya gama yiwa tunaninsa da zuciyarsa mugun kamu saiyakejin kamar bazai iya rayuwa Babu itaba Dan kuwa komai zai iya faruwa dashi idan bai samu NURU ba amatsayin matarsa uwar ‘yayan dazai Haifa.
Afia na ganin hakan ta wuce ciki tana Masa dariya da cewa”
Uncle Imran take it easy fa kada ka rasa 6sense dunka akan soyayya mu shiga uku barr IMRAN jalal ya zauce.
Da wata Yar dariyar qarfin hali yabi afia da zancenta idanuwansa suna Jan NURU dake tahowa cikin dogon wando da farar riga sai black scarf daure kanta duk da agajiye take sosai kyawunta ke bayyane tana qarasowa gap dashi ya miqa Mata cup din drink me sanyi da aka kawo Masa Yana cewa”
Have this my love kingaji ko?
Murmushi tasakar Masa takai hannu takarba takai bakinta ta kurba kenan idanuwanta suka sauka cikin na MALEEK dake tsaye da waya a kunnensa yanayi daga Palon ciki take ta qware da qarfi tana sakin tari ta miqawa Imran cup din tarinta na tsananta sosai
Cikin sauri da kulawa ya miqe Yana qoqarin Kai Mata cup din ruwa bakinta Tasha kozata ji sauki sauki sai kawai yaji anriqe cup din ya juyo da sauri sukai ido biyu da Mr Omar dake kallonsa cikin ido Ras ya Dan sake fuskar wata gantalalliyar murmushi tafito Masa yayiwa mum Sarah dayazo da ita kallo daya tayi saurin kallon NURU tana riqota tana Mata sannu tajata sukai ciki
Saida suka shige ya dago ya kalli Imran cikin girmamawar data so kularda Imran yace”
Barr IMRAN idan Babu damuwa zamu iya zuwa palon baqi dake gefen wannan sashen sbd dokokin gidan sun Dan qara tsauri yanzu Babu me sake shigowa sashen MALEEK dagashi sai ‘yayansa.
##MAMUH#
_ZAFAFA BIYAR_????????????
_Alkiblah–SAFIYYAH HUGUMA_
_Makauniyar qaddara–BILLYN ABDULL_
_Dalaal–MISS XOXO_
_Mabudin zuciya–HAFSAT RANO_
_Ubayd Maleek–MAMUH GEE_
_DUKA KUDIN WANNAN DADADAN BOOKS DIN SUNA KAN FARASHIN NERA 700. WATO KUDIN PAGES KENAN. DOCUMENTS IDAN AN KAMMALA SUMA KUDIN SU DABAN.._
Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????????
0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????????
*_08085405215_*
*_Mamuhgee 18_*
Oumahmad collection’s
07014488636
Kitchen utensils
Fabrics
Shoes nd bag
Phones
Veils
Children’s wears
Furnitures
Dubai,china,India,turkey,Malaysia
Kano hotoro
Fcbk Maryam muhd.
**************
Shiru Imran yayi yana bin Mr Omar da ido baice komaiba sbd Kamar bai gama fahimtar me Mr Omar dinba yace Kuma baiyi abinda yace mishi yayin ba, kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa ya juya ya fice daga Palon Yana fita harabar gidan ya shiga motarshi ya fice Dan Yana buqatan samun iska me kyau Dan yayi refreshing kwakwalsa dayakejin kaman ta toshe baya gane komai.
Mr Omar mabayanshi yabi da wani irin kallo mai ma’anoni da dama, ciki kuwa harda na tausayawa dan ya hango tsantsar soyayyar Nuru a cikin kwayar idonshi wadda yasan abin kamar da wuya Dan kuwa zancen me girma ne dayafi qarfinsu su ‘yan qasa qasa Dan kuwa yana da tabbacin aure tsakanin Nuru da Imran ba abune me yiwa ba duk da dai fadan hakan ba huruminsa bane.