UBAYD MALEEK Page 31 to 40

Dan
A bangaren Nuru kuwa karfin hali kawai take har lokacin gashi AFIA ta nace Mata akan tafiyar da zasuyi sai anje da ita Wanda takega kaman ta wuce huruminta Binsu delah gizah ziyartar kakarsu uwa sukutum ta MALEEK,
Amma ganin batada zabi na kanta ko ikon kanta Dole ta shirya ‘yan kayanta da basuda wani yawa yawancima dogayen riguna ne Dan Bata dauki me wando ko dayaba da zai nuna tasamu dama da sake da yawa.
Tana zaune jikinta a matukar mace tana qarasa hadawa Farhat kayanta cikin nata pink akwatin me hoton frozen sisters saiga Farhat din ta shigo da gudu ta zauna kan jikinta tana cewa”
My Lewa please kumana pancakes me Honey and chocolate.
Kallon bakinta NURU tayi tareda sake murmushi tana kamo fuskanta tayi kissing goshinta tana cewa”
Kome farhat din aunt NURU takeso za’a Mata.
Muje cikin din yanzu bada dadewaba zakici pancakes sweetie.
Kicin suka nufa tana riqeda hannunta suna shiga ta dorata kan kitchen island ta zauna ita Kuma tafara hadawa farhat din na tayata fira.
Bayan sun gama a kitchen din suka ci nasu saidai na AFIA suka aje Mata a dining.
dakinsu ta nufa ta tararda Afia a kan doguwar kujera rigingine idanuwanta a lumshe ta kifa littafi saman cikinta da alama karatu take bacci ya dauketa batare data sani ba.
Murmushi Nuru tayi ta gyara mata kwanciya ta lullube bargo me taushi kafin tayiwa Farhat wanka ta shiryata cikin kayan bacci marasa nauyi ta kwantar da ita anan dakinsu itama ta nufi toilet din tayo wanka tareda dauro alwala tayi sallar ishai kafin ta Sanya kayan bacci irin na farhat din riga da wando dogo saidai rigar batada hannu sai siriri hakama kayan nada roba ajiki sai suka kwanta jikinta sbd kusan kayan baccinsu su duka ukun duk za’a siyo iri daya ake siyowa saidai banbancin size.
Ta hau gadon zata kwanta farhat ta motsa cikin bacci tace”
Aunt NURU water please.
Kallonta tayi da idanuwanta dasuke Jin bacci tace”
Ruwa farhat??
Yes aunt.
Numfashi ta sauke tareda zuro qafafunta qasa ta saka slippers din dasuke yawo dashi cikin gida ta miqe tsaye tareda daukar qaramar hula ta saka akanta dabai rufe dukaba ta fito.
Al’adarshi ce fitowa cikin dare ya duba inda ya kamata saboda tsaro da fita hakk’in na k’asa dashi, yana kula da ransu da lafiyarsu, dan duk da Maleek ya kasance mutum mai izza da mulki hakan bai sashi ya manta dokokin Allah dake kanshi ba, yana k’ok’arin sosai wajen kaucewa hakk’in mutane, dan haka lokuta da dama yana fitowa cikin dare ya duba lafiyar iyalinshi da sauran mutanen gida.
Ba ruwanshi da lek’awa d’akin kowa dan yasan muhimmancin Privacy sosai iyakacinshi kawai ya duba inda ya kamata.
Ganin haske a cikin yasashi kallon hanyar tareda nufowa cikin nutsuwa saidai bai qarasaba sbd tunda take rayuwarsa nai taba shiga cikinba tun girmansa a iya saninsa Dan haka sai ya tsaya iya dining musamman dayaji kaman motsi a kicin din.
Itakuma daukeda robar ruwa biyu a hannunta ta fito batama lura da komaiba tabi ta gabansa ta wuce saidai taku daya ta qara ta tsaya cak zuciyarta na sauya bugawa sbd idan hancinta yajiyo Mata daidai qamshin MALEEK taji agurin.
Juyowa tayi ahankali Wanda yayi daidai da qarasowarsa zaibar gurin jikinsu ya hadu da sauri tayi baya tana sauke kanta kafafunta na son daukar rawa yayi Mata kallo daya ya wuce yabarta tsaye jikinta na neman yin sanyi sbd Tama rasa halin me tashiga a tsakanin tsoro da firgita.
Daqyar takai kanta daki ta tayarda farhat din zaune tana Bata ruwan abaki tana cikin Sha AFIA ta farka ta tashi zaune tana ‘yar guntuwar hamma ta miqe ta nufi toilet.
Farhat data gama Shan ruwan da NURUn ke Bata ta daga Kai ta kalli NURUn tana sake shaqar jikinta tace”
Aunt NURU kina qamshin irin turaren daddy.
Cak Afia dake gaf da shiga toilet ta tsaya batareda ta waiwayo ba ta Kira Jin amsarda NURUn zata fadawa farhat din.
Kasa cewa komai NURU tayi sbd batasan mezata fada ba saidai jin alamar AFIA ta tsaya yasata bude Baki daqyar a Sanyaye tana kamo abinda zata samu cewa tace”
No sweetie hancin kine sbd kila kinyi mafarkin daddy yanzu da kikai bacci.
Kwantar da ita tayi tana cewa”
Koma bacci kinsan gobe akwai zuwa school da wuri gakuma tafiya gizah.
Ajiyar zuciya kusan suka sauke tareda AFIA ta zame ta kwanta gefen farhat din tana rufe idanu ba shiri itama Afian toilet din tashige tana sake sauke numfashi me sanyi.
Washe gari tun 8 ta fice zuwa school bayan tagama breakfast da Shirin farhat data wuce school itama ta wuce sbd Kira da massages dinda Imran keta danno Mata gabaki daya hankalinsa a tashe yake musamman data fada Masa cewan daita za’aje gizah din saiyakejin kaman ya bisu Dan har zuciyarsa tafara bashi shawarar aje contact din Nan daya riqesa Wanda ya Hana rayuwarsa shaqat bare sukuni.
Tana Isa makaranta a can ya tarar dashi harya rigata Isa da kallon mamaki daga ita har afia suke binsa musamman ganin duk yayi wani iri idanuwansa sunyi laushi kaman ma kwana yayi bai rintsa ba.
Cikeda tausayinsa suke kallonsa duk su dukan hardai ita NURUn da idanuwanta sukai rau rau hawaye na neman cikowa cikinsu sonsa na qara shigarta ta tsaya daf dashi tana kallonsa cikin kulawa me tsanani da taushin murya tace”
Im lafiyanka kuwa?
Kana lafiya?
Bakayi bacci ba ko?
Kasa Bata amsa yayi sai kallonta dayakeyi kaman zai hadiyeta afia na ganin hakan ta wuce tabarsu anan tana yar dariyarsu.
Motarsa suka koma suka jingina anan yafara zayyane Mata shawarar dayakeson yankewa ta ajiye aiki sai bayan aurensu tukuna ta girgiza Masa Kai tana cewa”
Karkayi haka im idan muka saka gaggawa a al’amarin zai iya zuwa da tangarda,
Dan Allah kabi komai a hankali.
Murmushi kawai yayi Yana kallonta Yana cewa”
Idan kuka tafi zanyi missing dinki my love.
I will miss you too im Amma fa ka ajiye maganar aje aikin Nan please.
Gyada Mata Kai yayi kaman qaramin yaro sai hakan yabata dariya ta murmusa tana Dan juyar da kanta gefe daganan ya suka fara fira yanata sake langwabe Mata.
Ranar ko wani karatun kirki batasamu yiba sai yamma dasuka dawo Wanda shine dakansa ya dawo da ita tun a gate yana ajeta ya juya ya wuce.
Batajin yunwa Dan taci abinci a makaranta Dan haka wanka tayi tai salloli tana idarwa tasake hada sauran kayansu na tafiya Dan yau da daddaren zasu bi jirgin Daren zuwa gizah.
Kasa zaune tayi takasa tsaye gabaki daya batajin nutsuwar zuciya data gangar jiki daurewa kawai takeyi Amma wlh tana cikin wani hali na tsoro da shakka na zuwanta can din sbd sanin matsayinta Kuma idan taje can Dole tayi bauta kaman sauran bayi matuqar ba maganar zamtowanta negestati zai fito fili ba kuma idan hakan ta fito fili Dole amiqata ga NEGES dinta Wanda duk wannan cigaban rayuwar data samu zai tashi a banza.
Daga ita har afia qarfin haline kawai sukeyi suna sakewa Kamar suna cikin farin cikin tafiyar Wanda kowaccensu cikin ranta a matuqar tsorace take kaman zuciyoyinsu zasuyi tsalle su fada kowa da bikin zuciyarsa.
Qarfe Tara na dare jirginsu zai tashi Dan haka suna sallame sallar ishai suka fito masu aiki na janye da akwatinansu dasuke kaman set Dan duk iri dayane,
Ita doguwar rigace purple ajikinta sai gyale light purple data daura sai handbag da wayarta da sauran Yan abubuwanta qananu dasuke ciki
Qafartama flats Versace ne black a sanye sai face mask data Sanya Dan kaman iska iska takejin yamata yawa.