UBAYD MALEEK Page 31 to 40

Saurin rufe fararen idanuwanta da maleek duk su ya sauko tayi cikin wani irin hali na damuwa me tsanani tace”
Ya Allah ya kabar da wannan zancen akan MALEEK dinta Dan kuwa har abada ko amafarki Bata fatan ace hakan yazama gaskia Dan kuwa sbd wannan zancen da NEGES ya fada matane ciwon zuciyarta ya tashi Wanda tasa aka bugawa MALEEK Dan kawai yazo ta tabbatarda abinda hankalinta ya dagu da jinsa.
Saida afia ta tabbatarda zuwa yanzu saqon zuwansu ya isa gurin Anneti kafin suka dungumo zuwa gurin nata.
Tun a hanya NURU ke sake shiga taitayinta tana sake Kama kanta farhat dai na maqale da ita bayi uku na bayansu.
Fadar tsari da kyawun sashen mahaifiyar MALEEK bamai faduwa bane saidai kawai ace Masha Allah da wannan daula.
A babban palonta na kurya suka taddata suna shiga da sallama dauke a bakunansu Banda farhat data saki hannun NURU tayi gurin Anneti da gudu ta fada jikinta cikin tsananin farin ciki.
Farin cikin ganinsu ya Hana Anneti rufe Baki ta budewa afia hannuwanta ta qaraso da sauri ta rumgumeta tana cewa”
Kemiri nafik’akelewi ya Anneti (I miss you so very much Anneti/nayi kewarki sosai Anneti)
Murmushin farin ciki Anneti tasaki itama cikin yare da muryarta me tsananin taushi da dattako tace”
Masha Allah li’iliti takusa zama Mata agurin me gagaruman sa’a
Ya Allah ya albarki rayuwanku ku duka.
Amin sukace dukkaninsu har NURU dake tsaye Dana farko ta kasa qarasowa.
Idanuwa ta zubawa NURU dake tsaye tana kallonsu cikin burgewa suna hada ido tayi saurin sauke kanta tareda zubewa qasa ta durqusa tana cewa”
Barka da hutawa Anneti.
Har lokacin kallonta Anneti keyi sbd kyawun NURU da yanayin kyan fatarta dake haskota yasa take Mata kallon ‘yar sarautar delah ce ta bude Baki cikin kulawa ta amsa mata tana maido kallonta kan Afia tace”
Wannan wacece??
Cikin sauri farhat tace”
Aunt NURU ce ta Dade agidanmu taredamu she’s family.
Da mamaki tasake kallon NURU tana kallon afia data share zancen Dan batason fadar matsayin NURU na ‘yar Taya zama da aka kawo musu ita wadda su tuni suka dauketa ‘yar uwa ta jini wadda takewa kallon wani bangare na rayuwarta Dan kuwa qaunace me qarfi a tsakaninsu.
Jawo wani zance afia tayi ta hanyar cewa Nuru ta qaraso ta zauna acikinsu.
A Dan kakkame ta qaraso Amma Bata zaunaba saita zauna a qasa Yana cewa hakanma she’s ok.
Ganin NURU da farhat yasa Anneti bataiwa afia maganar mahaifiyarsuba Wanda afia ta lura da hakan hankalinta yatashi sosai matuqa musamman batason ayi tambayar gaban farhat Dan zata fada cewar mum dinsu ta Dade da tafiya tabarsu.
Basu bar sashenba sai dare suna zuwa wanka sukai suka kwanta Banda NURU data fara waya da Imran.
Kasa bacci afia tayi tana saqa da warwara,
Babban abin tsoronta anan shine Dole ita Anneti zata tambaya mum dinsu Dan kuwa MALEEK ko sunyi mgnar da Anneti bazai taba fada Mata komai akaiba ita Kuma duk qaryar dazatayi na kawo wani excuse dazatace ya Hana mum zuwa bazai shigaba Dan kuwa Anneti zata gane komai Daren dadewa Dan haka take buqatan lokaci Wanda zatai amfani dashi ta shirya iyayenta kafin agano.
Da wannan tunanin tayi bacci takuma farka,
Washe gari ma agurin Anneti suka wuni saidai Banda NURU wadda ta Kama kanta ta zauna guri daya sbd yawo ba nata bane acikin masarautar gizah ta yayan masu masarautar ne
Sai washe gari dazasu yawon ziyara cikin masarautar zuwa sashe sashe na ‘yayaye da sarauniyoyin gizah shine tabisu saidai tayi danasanin Binsu Dan kuwa sake tabbatarda rashin darajarta tayi shiyasa Bata Kuma gigin binsu ba idan zasu fita acikin gizah din ta Kama kanta ta zauna guri daya sai tunanin gida da iyayenta yadawo Mata Kamar sabo.
Duk yanda Afia ke zamewa Anneti sbd kada tasamu damar yimata maganar mahaifiyarsu yau da kanta taje gurinta Dan tabbatarwa da kaman jita jitan da kaman yakeson fita na rabuwar iyayenta din sbd shekaran jiya da jiya duk sashen dasukaje sai anyi tambayar matar maleek guda ace bataxo duba Anneti ba wane irin uzurine wannan.
Hakan yasa hankalinta tashi matuqa sbd tabbas Kam kowa zaiyi nasa tunanin daban daban ace Annetin delah gizah mahaifiyar MALEEK guda ace matarsa batazo dubata ba tabbas zance yafara bayyana take ta aika sako na musamman ga mahaifinta na cewa akwai karatu me mahimmanci a makaranta sunada buqatan komawa Kuma tana roqonsa daya koma taredasu sbd shine jigonsu bazaso komawaba bataredashiba.
Hakan datayi saiya sake saka Anneti cikin shakka da mamaki sbd sakon MALEEK saiya biyota gurinta yake Isa gurin maleek Dan haka ta aika aje akawo Mata farhat batareda sanin afia din ba.
Agurinta ranar farhat ta kwana da daddare bayan sunyi Shirin kwanciya ta kalli farhat din tana shafa Mata Kai cikin kulawa tace”
Farhat mamanki meyasa bata biyoku ba bayan ga abal dinku dayafita ayyuka yazo dubani??.
Kai tsaye farhat tace”
Mum ta Dade da tafiyanta munata kuka nida afia
Daddy ma da kansa yace idan ta tafi kada tasake dawowa yabata da ita koyaushe.
Wani mummunan bugawa zuciyar Anneti tayi har Saida ta dafe Dan kuwa kiris ne yahana ciwon zuciyarta tashi duk da hakan wani radadin tashin hankali takeji,
Idan dagaske MALEEK yarabu da lailah zancen yafito Babu ta yanda zai karbi mulkinsa Dan kuwa kaf a tarihinsu sarakuna basa sakin matansu wannan wace irin masifa ce.
Cikin tashin hankali tasake sanyaya harshenta tace”
Tun yaushe ne ta tafi?
Tun kafin aunt NURU tazo ne ta tafiyan munata kuka hadda Afia Amma tunda aunt NURU tazo daga delah jekadi takawo Mana ita shikenan muka daina kuka sbd Aunt NURU tana Sona sosai tunda tazo AFIA tadaina damuwa suka zama Best friends tanamun pancakes da komai nakeso Kuma daddy ma tana Masa abinci fa yafi nasu mum Sarah Dadi aunt NURU tafi mum sbd ita Bata barina Ina kuka Kuma tace bazata tafi tabarniba kaman yanda mum tayi idan sunyi aure da uncle Imran ma Dani zata tafi.
Wuta Anneti ta dauke gabaki daya
Numfashinta yafara yankewa tana dannewa,zufa kuwa kaman tana cikin dakin gashin biredi.
Daqyar ta iya daidaita numfashinta ta kalli farhat tana nazartan zantuttukanta daya bayan daya tana fahimtarsu tana kawowa inda farhat tace jekadi takawo musu NURU daga delah sai kawai ta tsaya anan ta shafa kan farhat din tareda kwantar da ita tana Mata addua har tayi bacci.
Palon hutawarta ta Isa ta zauna tareda daukar wayarta ta Nemo numbern jekadi ta Danna Mata Kira.
Cikin girmamawa me girma jekadi ta dauki wayar tareda zubewa qasa tana jerowa Anneti gaisuwa cikin tsananin girma.
Shiru Anneti tayi na mintuna biyu kafin tace”
Jekadi bayanin komai nakeso na NURU yarinyar dake zaune agidan MALEEK.
Tsit jekadi tayi tana juya zancen zufa na karyo Mata cikin tsananin ladabi da girmamawa tayi kasa da Kai kaman agaban Anneti din tace”
Allah ya taimaki Anneti kimun afuwa nafara tambayo izinin fadar wannan magana agurin KALEEB.
KALEEB?” Anneti ta fada ahankali cikin mamaki duk da tasan dama Dole Saida sanin Kaleeb jekadi ke komai.
Katse wayar tayi ta Nemo numbern kaleeb da kanta takirasa.
Kira uku tayi se Ana hudu ya daga cikin muryar girma da mulki take itama tayi qasa da murya tahau gaisuwa cikin tsananin girmamawa tana sake tambayarsa manyanci.
Shiru tayi bayan gaisuwar tarasa ta inda zata faro har Saida yayi gyaran murya a kame yace”