UBAYD MALEEK 1-END

UBAYD MALEEK Page 31 to 40

Kiyi maganarki kada ki damu kaleeb zai duba koma menene.

Cikin sanyin murya tace”

Allah ya taimaki kaleeb idan banyi shishigiba inason sanin wacece yarinyar da jekadi takai gidan MALEEK.

Murmushin manya yayi Kai tsaye yace”

Negestatinsa ce sbd ya rabu da matarsa.

Hawaye ne suka ciko Mata ido tace”

Allah ya taimaki kaleeb nagode Allah yaqara girma ina fatan ban dameka ba da Kiran dare danayi.

Bakomai Anneti Allah ya taimakemu duka.

Maganar rabuwar MALEEK da matarsa kuwa kinsan meya dace kiyi qato shiru sbd fitar hakan barazanace ga maleek.

Inshallah kaleeb ngd ahuta lafiya.

Kasa daurewa tayi Saida wasu irin hawaye me zafi suka gangaro Mata sbd wannan masiface agurinta babba.

Ta Yaya zata Hana fitar maganar rabuwar MALEEK da matarsa.

Jekadi takira anan jekadi ta fayyace Mata komai na yanda rabuwar take Wanda yasa ran Anneti baci sai yanzu ne tagano dalilin qin barin ayi maganar da afia keyi sbd Kare mahaifiyarta kada mutuncinta ya zube.

Ko so daya adaren Anneti Bata rintsaba Dan kuwa ki NEGES bazata Bari yaji zancenba tunda zargi kawai yake zata barshi yayita zargin kawai batareda ya tabbatarba.

Washe gari tun qarfe Tara ta aika cewa tana gayyatar su AFIA  cin abincin safe a sashenta tareda ita.

Da farko AFIA taji wani Abu na kwanan da farhat tayi acan gurin Anneti Amma da  bataji bayani ko ganin sauyi afuskan Anneti ba saita sake abinta Dan ma kada asamu damar yin maganar saita saka NURU shiryawa Dole suka taho tare.

Tunda suka zauna cin abinci Anneti tayiwa NURU kallon sakanni ta dauke kanta ta maida kan Afia dake cin abinci ba damuwar komai aranta.

Suna gamawa NURU ta fice daga sashen gaba daya sbd kallon da Anneti ke Mata yasa hankalinta tashi matuqa tashiga wani irin matsanancin tsoro.

Kai tsaye Anneti ta kalli afia bayan fitar NURUn tace”

Maleek da lailah sun rabu gaskia ne kokuwa???

Wani irin mummunan tarine ya kufcewa afia ta dago da jajayen idanuwanta ta kalli Annetin cikin tsananin firgici da tashin hankali tace”

Aa Basu rabu ba sunanan tare.

Meya hanata zuwa ita?

Sake dagowa tayi dukkanin idanuwanta na qarasa sauyawa cikin dakewa da qarfin hali tace”

Ayyukane sukai Mata yawa tayi tafiya.

Murmushin takaici na manya Anneti ta sake tana kallon zallar kuruciyar afia da yarintarta tace”

Idan har hakane kuna buqatar uwar dazata kula daku da mahaifinku sbd….

Cikin tsananin tashin hankali da firgici afia ta miqe tsaye jikinta har ‘yar rawa yakeyi ta zube gaban Anneti cikin rawar murya da Bata girmanta na uwar MALEEK tace”

Anneti Ina roqanki da kadaki kawo Mana kowa bama buqatar wata uwa sbd munada me kula damu wadda take tamkar uwa.

Kallon tsaf Anneti ta Mata saidai tasan zallar kuruciya kecin afia Amma tace”

Wacece ita?

NURU tafada Kai tsaye.

NURU ba mata bace Matar uba ake magana wadda zata zauna daku har abada.

Rintse ido tayi sbd fadar abinda zata cutatar da NURU saidai Dole zatai hakan Dan kawai abar zancen su samu su taciyarsu batareda wani maganar aure aure ba wa dad dinsu.

Bude idanuwanta dasukai jajir tayi ta sauke Kai muryarta na rawa tace”

NURU da dad zasuyi aure idan munkoma…….

Wani razanannan kallo Anneti tai Mata cikin tsananin mamakin mahaikaciyar kuruciya irin tata,

Wace irin zuciyane da afia dazata yiwa mahaifinta qarya Dan Kare mahaifiyarta?.

Ji tayi zuciyarta ta sosu da abinda afian tayi saidai ta danne bacin ranta sbd gudun shedan yashigo cikin lamarin sbd afia ta dauko wata mummunar sabia me qarfi qararda zance irin wanan akan MALEEK guda idan har Bata dauka matsayinsa na mahaifi agaretaba.

Tabbas yau zata nunawa afia yaro man kaza ne,

Ta dauko magana me girma Dan Kare darajar wadda batasan daraja ba Dan haka yau zatasan ba’a Wasa da magana irin wannan.

Kitashi kije zancenki ya karbu.

Ajiyar zuciya boyayya afia ta sauke duk ganin takashe maganar qara auren mahaifinta duk da zuciyarta bata daina bugawaba kamar zata faso ta miqe ta fice tana istigfarin na neman yafiyar ubangiji.

Bayan fitarta waya Anneti ta daga ta Danna Kiran jekadi Kai tsaye cikeda bada umarnin me qarfi tace”

A isarwa kaleeb saqo daga Anneti cewan muna roqon alfarmar auren NURU daga negestati zuwa Mata ga MALEEK na Delah gizah UBAYD MALEEK.

Da qarfi jekadi ta zube qasa tana yiwa Anneti wani irin kirarin tsananin farin ciki da girmamawa.

##MAMUH#

Share this

[ad_2]

Previous page 1 2 3 4 5 6 7

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button