UBAYD MALEEK 1-END

UBAYD MALEEK Page 41 to 50

Tana aje wayar miqewa tayi Takoma dakinta tareda dafe kanta da tuni yadauki wani irin ciwo sbd tarin mamakinda afia ta Bata Wanda take sake Dora hakan akan rashin uwane tareda ita tarbiyarta tafara yin qaranci tana sauyawa Dan kuwa ita din Bata saniba Amma abinda tayi laifine me girma da Muni yiwa mahaifinta qarya irin wannan da zata iya zubda mutuncinsa da awani gurin ta fada hakan Dan hakanma ta yanke shawaran Babu Wanda zaisan abinda afia din tayi zata bar zancen akan MALEEK aure kawai zai qara basai kowa yasanda rabuwarsa da matarsaba bare qaryar da afian ta shata Dan Kare mahaifiyarta.Afia kuwa tana Isa sashensu a palo ta tadda NURU da farhat na zaune Kamar ko yaushe farhat na jikin NURUn suna kallon cartoon din SpongeBob ta tsaya cak tana kallonsu hawaye nason ciko idanuwanta Amma ta danne sbd tanajin zuciyarta na karyewa na abinda tayi din sbd ta Kara NURU Dan biyan buqatarta Wanda idan daga baya bayan sun koma akaji auren NURU da Imran za’a iya daukan hakan amatsayin cin amanar MALEEK datayi tunda yanzu Anneti taji cewar MALEEK zata aura..

Cikin yanayi na sanyi NURU ta dago Jin mutum a tsaye akansu ta kalleta da idanuwanta dasukai laushi sbd ciwon Kai datake ji kadan kadan ta bude baki ahankali tace da sanyin murya tace”

Afia lafiyanki k…..Bata qarasa maganar taba afian ta qaraso hawayen cikin idanuwanta na gangaro ta rungume NURUn tana rintse ido batareda tace komaiba.

Shiru NURUn tayi itama dukkanin jikinta na sake yin sanyi Jin saukan hawayen afia akan bayanta dake bayyane ta cikin doguwar riga Mara hannu.

Sun Jima ahaka kafin NURUn ta dago afia tana kallon idanuwanta dasukai jajir ta saki wani sanyayyan numfashi tace”

Menene yafaru??

Kasa kallonta afia tayi ta juyar da Kai gefe tana hawayen cikin idon suka sake gangarowa kafin ta dago ta zubawa NURU idanuwanta cikin sanyin murya da nadama tace”

NURU idan Baki saniba ayau inason kisani ke din wata babbar bangarene na rayuwata nida farhat,

Ina Jin araina tamkar yanda nakejin farhat sbd na dade da Baki matsayi na ‘yar uwar uwa daya uba daya,

NURU wlh kisani duk duniya banajin zanyi Abu Dan kawo cutatarwa gareki Dan haka nake roqonki dakimun uzuri karki zargeni da komai idan har kikaji wata magana ta bullo Miki daga Anneti duk da nasan sirrine da bazata futarba ita kanta saidai koma yayane Ina roqon alfarmarki da kadakice komai duk tsanani kada kifada komai duk abinda akace kice eh sbd hakan shine zai bani lokacin kawo gyara tsakanin dad da mum Dina Wanda kinfi kowa sanin wannan shine burina a duniya and you promise to support me akan hakan right??

Tsit NURU tayi tana kallon afia din kaman wata sokuwa sbd ita anan Bata gane komaiba sbd zancen duk a baibai yake bayan hakan ita menene nata wane matsayi take dashi da afia zatace tashigo cikin zancen komai akace tace eh,to menene zata cewa eh din??

NURU Zaki taimakemu mu dawo da mahaifiyarmu nida farhat??

Cikin tsoro da mamakin shiga huruminda ba nataba ta kalli afian da idanuwanta sukai jajir ta gyada Kai ahankali batareda ta iya bude Baki tayi maganaba sbd Jin abin take yayi Mata nauyi kaman bazata iyaba sbd Jin kamar ba zancenda zata shiga bane.

Zamewa tayi gefen NURUn data shiga tunani haka kawai ta kwanta tareda Dora kanta kan jikin farhat dake jikin NURUn itakuma da hakan duk su duka biyun suka shiga tunani.

****

Tsaf kaleeb yaga sauraron saqo me girma da jekadi tazo dashi idanuwansa nakan makekiyar TVn data kusa cike Rabin bangon palonsa zaka dauka baya sauraronta Amma tsaf yagama Jin komai ya jinjina Kai Yana sake juya zancen cikin ransa da tunaninsa.

Jekadi menene halaye munana da kyawawa na NURULHUDA??

Ya qarfin nutsuwarta da biyayyarta?

Ya qarfi da girman son duniyarta take?

Sake zubewa qasa jekadi tayi cikin girma da tabbacin abinda zata fada Kai tsaye tace”

Allah ya qarawa Kaleeb Nisan kwana da lafiya.

NURU negestati ce wadda zance komai nata da yardar Allah yayi abisaga tsarin da kake son Matar MALEEK ta kasance,

NURU jikace Kuma ‘yar asalin amintaccin bayinka da kakanta da mahaifinta,

NURU baiwace me biyayya tareda da’a wadda takaita ga samun ribar zaman rayuwa,

Anneti ce da kanta tayi zabin NURU tazaman Matar aure ga MALEEK wadda zan bada rayuwata akan Anneti Bata yanke komai akan garaje Wanda wannan halin na zurfi da tsaftataccen tunanin daukarsa tayi daga cikin halayen girmanka da adalcinka ya kaleeb.

Jinjina Kai yakuma Yi tareda kallonta wannan karon ya bude Baki cikin gamsuwa da zallar cikar ikonsa yace”

Ahada dukiyar neman auren MALEEK UBAYD zuwaga mahaifinta tareda saqon ‘yantawa ga dukkanin zuriarsu tareda tukuicin zuwa gizah ga dukkanin ahalin Dan halartar auren ‘yarsu.

Sake zubewa jekadi tayi tana miqa tsagwaron godia da kirari tareda fatan nasara da tarin aduoi ga wannan aure harta fice tanayi cikin tsananin farin take da wannan aure sbd har cikin ranta Allah yasanya Mata kaunar NURU take Kuma fatar cigabanta Wanda tun zuwanta ta yaba takuma Yi tunanin kyawu da halaye na gari irin na NURU matuqar ta zama negestatin MALEEK to ko Bai auretaba wata Rana to tabbas saita zamana negestatinsa datafi matansa daraja a zuciyarsa saigashi abin yazo alokacinda Babu zato ba tsammani Dan haka ko minti biyu Bata qaraba aka fitarda saqon kaleeb take aka fara hada dibbin dukiya da tarin zinarai masu nauyi da daukar ido Wanda yasa take maganar ta fito filin Allah zancen auren ya bazu Kamar wutar daji wasu Basu tabbatarba Saida aka Kai dukiyar gidansu NURU yakasa dauka take aka sauya musu muhalli acikin qanqanin lokaci gari kuwa ya dauka tako Ina zancen akeyi wasu na qaryatawa wasu kuwa mamaki da firgici ya hanasu yadda.

Padima dake zaune bakin kofar dakin da aka jere dukiyar neman auren NURU dakuma Wai MALEEK UBAYD Wanda sunansa kawai sukeji kaf delah din Nan kila idan ba kakansaba sai wasu qalilan ance Babu Wanda ya taba ganinsa koda cikin sa’a ne.,

Sam Bata yardaba da wannan zancen tafi yarda da cewan wani dai acan gizah zai auri NURUn Amma badai MALEEK ba Dan kuwa har abada ko ita datake gaban NURU akomai Bata taba kawosa cikin rantaba bare NURU sokuwa wannna masarautar delah ta boyewa su abal ne amma tasan tsohon da take negestatinsace zai aureta Kuma a iya saninta ba ace musu maleek ba da akazo daukarsu negestati.

Kallonta amminsu tayi lokacinda ta fito dayan dakin riqeda hannun meryam daketa tsalle tsalle da farin ciki me tsanani tun jiya da akace Mata zasuje inda zasuga NURUnta.

Da mamaki ammin tace”

Padima tun jiya kin kasa dogon motsi kin kasa kin tsare kofar dakin Nan bayan kinsan Babu Wanda zai shigo gidan Nan idanma sata kike gudu ki kwantar da hankalinki Mana idanma tambaba kike na waye NURUn zata aura ai zamuje saimu tabbatar sbd muma munkasa yadda da abin al’amarin yazo mana a wani irin girmame saidai koma wane munsan wannan babban cigabe da abin farin ciki ga NURU sbd aure abune me girma dazai tabbatarda darajarta.

Qala padima Bata samu cewaba dan kalma daya acikin zancen ammin Bata fahimta ba babban burinta da damuwarta yanzu shine su tafi gizah din tasamu ganin NURU taji komai daga bakinta shine kawai zai Bata kwanciyar hankali tanaji meryam na fada Mata amed na kiranta waje harso shida tayi kamar batajitaba qarshe korata tayi da wani mugun kallo dayasa meryam din tafiya gurin ammi tana waiwayen padiman sbd ganin yau ko gyaran dogon gashinta batayiba Wanda kullum sai tayi gyaransa Kamar wani sarki.

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button