UBAYD MALEEK Page 41 to 50

Shekara daya ciwo ajiki shine NURU Bata taba fadaba.?
Menene matsalar?
Ciwon zuciyane yanzu nakai Ina amai da tarin jini wani lokacin.
Innalillahi padima meyasa bakuje ko English hospital na can ba.
Shiru padima tayi tana hawaye da shehekar data sake bawa afia tsoro tafara Mata tambayoyin akan yanda takeji da kalar jinin datake gani tana nazartawa da ‘dan nata ilimin na likita da Bata qarasa zamaba.
Girgiza Kai tayi cikin jimami da tausayawa tareda tsoro tace”
Padima this is serious yakamata kiga likita cikin gaggawa gaskia.
Kuka padiman tasake fashewa dashi tana cewa”
Bansan Yaya zanga likitaba Dan Allah li’iliti ki taimakeni NURU takasa taimakona banason na mutu yanzu.
Ki taimakeni ki kawoni gurinki ki kaini gurin likita Dan Allah.
Shiru afia tayi ciki rasa sanin abinyi Nan take Sadai koma menene batada ikon kawo padima Nan take Dole saidai NURUn ce zatace akawota tukuna akawota din sbd kawo mutum Kai tsaye gidan MALEEK wani aikine Dan kuwa sai ankaita gizah an tantance kafin akawota gidan MALEEK Wanda yanzu Kam NURU ce kawai takeda ikon kira gizah tafada tanason akawo Mata padiman.
Ajiyar zuciya ta sauke tareda nutsuwa cikin son fahimtarda padiman tace”
Kiyi hkr padima Inshallah Zaki samu lafiya Amma yanzu dai Ni inshallah zan nema appointment na babban likitan da Zaki gani anan Amma maganar zuwanki zanyiwa NURU magana idan ta tashi saita Kira inda za’a kawo ki anan din.
Nagode sosai Allah yaqara girma ina gaida NURUn idan ta tashi.
Katse wayarta tayi tareda wurgi da ita tana jerowa daga afia din har NURU zagi sbd Sam sunqi hawa yanda takeson suhau su rikice da tausayinta yazama basa tunanin komai saina tausayinta tasamu Isa qasar.
##MAMUH#
Share this
[ad_2]