UBAYD MALEEK 1-END

UBAYD MALEEK Page 41 to 50

Daga waje Kuma amed ganin Bata fitoba harya gaji da tsayuwa ya juya ya wuce Yana cewa”

Kome Zakiyi wlh sai anci dukiyar Nan Dani sbd rabona ya koka aciki Dan kuwa nasan yanzu tunda Zaki tafi gurin NURU a gizah dukkanin burinkanki kinsamu damar cikasu wlh maqalewa yanzu nafara Miki mutu ka raba komai Zaki samu taredani zamu cisa.

****

Zaune yake cikin makeken palonsa na quryar sashensa Wanda bayan masu gyarawa Babu Wanda yataba shigarsa ciki Koda kuwa mahaifiyarsace.,

Kyawu da tsarin palon kawai ya isa sanyaka lissafinda bazaka iya kaiwaba musamman sbd komai na sassansa na daban ne Dan zamowarsa MALEEK.

Akaro na biyu ya sake wani boyayyan numfashi Yana sake lumshe fararen idanuwansa dasuka Dan sauya sbd ciwon Kai me qarfi daya damqesa lokaci daya da kaleeb yakirasa ya sanar Masa da aure za’a daura Masa da negestatinsa abisaga umarni dakuma roqon alfarma da neman cika biyayya daga mahaifiyarsa da Bata taba neman wata alfarma daga garesaba ataqaice wannan ne Karo na farko data yanke hukuncin wani Abu akansa tun bayan rasuwar mahaifinsa Yana qarami.

Kaleeb ya sanar dashi an aika komai ankai qarshen komai jibi za’a daura auren Wanda har zancen ya fita shin tayaya zai musa wannan auren da yarinyar datake tamkar ‘yar cikinsa Dan kuwa idanma lissafin yaje daidai afia zata girmeta Koda da shekara biyune ko daya.

Ta Yaya aure zai shiga tsakaninsa da wadda yakewa kallo daya da farhat qanqanuwar yarinyar da batafi shekara gomaba.

Wayarsace tayi haske tana vibrating ahankali ya bude idanuwansa ya kalla wayar ahankali yaga sunan Mr Omar akai dauke Kai yayi tareda mayarwa ya rufe tsawon lokaci ahakan kafin ya bude idanuwan daidai Mr Omar nasake Kira sbd sanin MALEEK dakyau da yayi yasa yake iya kwatanta mintunan sake Kira na biyu idan yayi na farko cikin sa’a kuwa ya daga batareda yace komaiba.

Da sauri cikin girmamawa da kaucewa dogon bayani da MALEEK bayaso yace”

Barka da hutawa MALEEK.

Dama ‘yan media ne sukeson yada zancen…um..um..maganar auren ko za’a sirrantane?duk Wanda ya fitar Kuma mu dauka mataki akansa.

Kai tsaye yace”

Aure Yana boyune???

Jin haka yasa mr Omar cewa”

Allah ya huci zuciyar MALEEK.

Kashe wayarsa yayi ya ajiye tareda Miqewa yayi ciki Dan kuwa kila Babu me sake ganinsa sai gobe idan kaleeb ya iso daura auren Dan yasan zancen yanzu cikin awanni kadan zai bazu koina musamman NEGES da tun jiya yake son ganinsa Amma baya cikin mode dinda zai iya ganin kowa.

Yana daf da shigewa breaking news din auren THE KING OF DELAH GIZAH MALEEK UBAYD ya sauka acikin cikin qatuwar TVn dake palon ya juyarda idanuwansa ahankali zuwa kan time sai kawai yashige sbd Dama yasan media jira kawai suke abasu tabbacin zancen gashinan mintuna uku da zancen harsun sake breaking news.

*******

Qarfe shida na yamma daidai lokacinda zancen auren ya fita adaidai lokacin Anneti tayo aike me qarfi na daukar NURU zuwa wani kebantaccen sashe dake cikin sashenta Wanda Babu Wanda yasan inda aka Kai NURUn har afia kuwa Dan Koda aka tafi da ita afian na bacci Dan ko daki ba’a Bari Takoma ba daga Palo Dan haka Koda afia ta tashi da mummunan labari biyu daya Bata mummunan shock taci Karo na farko tun a waya tasamu labarin auren mahaifinta ta fito a rude saikuma tasamu labarin kebe NURU Wanda kowa yace baisan inane aka kebetaba.

Wayar dad dinta ta nema arikice tafara Danna Masa Kira Bata shiga hannuwanta dukkaninsu rawa suke da qafafunta tana sake Danna Kiran dad dinta Kiran Imran sai shigowa wayarta yakeyi na kakkautawa tana kashewa Dan ayanzu batasan ma a Ina kanta yakeba ta zari takalmi tayi sashen Anneti saidai tana shiga bata samu ganinta ba sbd Wai tana hutawa Bata fitowa lokacin dawowa tayi a haukace ta nema numbern kaleeb ta Danna Masa Kira shima Bata samu damar magana dashiba Yana cikin dakin hutawarsa.

Ji take kamar ta Ari hauka sbd so take tasamu bayanin abinda tagani take kumaji idan zancen datayine aka dauka da gaske take ake Shirin auren tun anan.

Palo tadawo ta zaune tana neman rusa kuka sbd idanuwanta dasuka kada sukai jajir ta dafe kanta dake neman tarwatsewa.

Wayartace tayi ringing a zabure ta wawuro wayar tana dubawa sai jikinta yayi wani irin daskarewa sbd tsananin sabon firgici da mamakin data shiga sbd ganin sunan””

MUM” baro baro akan screen dinta sai kawai jikinta ya saki tana kallo wayar na ringing harta tsinke Bata iya dagawa Dan kuwa rabon data ji mum dinsu shekarunma batasaniba tun bayana tafiyarta sai yau Wanda tasan dalilin Kiran baya wuce labarin auren dad dinsu data gani a duniya.

Zubewa tayi kan kujera tareda sake kuka Mara sauti tanajin wani zafin mum dinta da duk itace silar watsewar farin cikinsu” i hate you mum”takeson cewa Amma zuciyarta na hanata saidai wani irin zafin mum din takeji,

Babban baqin cikinta biyu ta rusa rayuwar NURU bayan tasan yanda sukeson juna da Imran hakama Imran ta rusa Masa farin ciki uwa uba me gaba daya bazata iya yadda ta karbi wata ba mum dinsuba amatsayin matar dad dinsu Dan haka Dole zatasan yanda zatayi ta Raba wannan auren ko an hadashi sbd kowa yasamu abinda yakeso.

***

Duk wani gyara da shiri na musamman anfara yiwa NURU shi atake da aka zo da ita Wanda Kuma kala Babu Wanda yake cewa ga duk tambayoyin datake musu sbd ita tsoro da firgici abin yake Bata Dan batasan meyake faruwa duk ta daga hankalinta musamman dataga ire iren gyara na musamman da ake Mata tamkar wata sarauniya Wanda Kuma ta tabbatarda wannan Shirin na aurene kokuma na Shirin kaiwane ga NEGES,to kenen gurin NEGES dinta datake negestatinsa za’a kaita..wasu irin hawayene masu matuqar zafi suka ciko idanuwanta tuno komai ya ruguje kenan daga yanzu a rayuwarta.

DELAH GIZAH ta dauki babban amo na jama’a manyan qasashe da dauloli dabam dabam hadda turawa da larabawa na nesa Dana kusa sun cika gizah damqam shiyasa tsaro da matakai harsunyi yawanda ko matso na Wasa basayi sbd atake zakayi ta bakin ranka sbd matakan tsaron ba dama musamman idan washe gari tayi ranar daurin auren kenan matakan saisunfi tsananta dan kuwa ko yanxu bashiga ba fita a gizah idanba na manyan baqinsuba na daurin aure.

Anneti duk wani farin ciki tana cikinsa musamman datai ido biyu da kyakkyawar fuskar NURU wadda cikin kwana biyu kacal ta sauya sbd tsananin gyara daya maidata tamkar asalin sarauniyar gizah musamman har wani sheqi fatarta keyi tuni tasake bada odar dasa sabon gyaran ciki Wanda zaibadu damar janyo zuciyar MALEEK gareta daga sun kusantu.

Washe gari jekadi na isowa tareda iyayen NURU dasu padima acikin tawaga ta musamman ta kaleeb Wanda Yana shigowa gizah aka rufeta gabaki daya ba shiga ba fita sai bayan daurin aure da qarfe biyun Rana.

Guri na musamman aka sauke iyayen NURU wainda suketa fama da padima da zazzabi me qarfi ya rafketa reras Banda some some Babu abinda takeyi daqyar suka samu tayi bacci kafin sukaci abincin alfarma fiyeda kala goma suka koshi aka kawo kayan Shirin abal dinsu ya shirya masu tafiya dashi suna jira yafito suka nufi can bangarenda za’ayi daurin aure yabar amminsu da sallar nafila tana zuba adduaoin a daura auren Nan lafiya yasa idan akai auren sai mutuwa NURUnta.

Meryam Kuma a zaqe take dataga NURU wadda Babu me ganinta kaf sai mijinta idan tafara fitowa daga maboyarta Wanda wannan al’adarsu ce.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button