UBAYD MALEEK Page 41 to 50

Qarfe biyu aka daura auren UBAYD MALEEK M KALEEB da NURULHUDA ABAL YONAS akan sadakin darhaman zinare Wanda dubban daruruwan hamshaqan duniya suka shaida a masarautar delah gizah dakeda kafaffen tarihin.
Daurin auren yasamu ‘yan farin ciki da Yan sabanin hakan da masu burika daban daban akansa Dana alkhairi Dana sharri.
Maganar aurensa ita ta batarda maganar rabuwarsa da matarsa data fara bulla.
Har yamma tayi lis afia Bata cikin cikakkiyar nutsuwarta Dan haka tanajin saqon fitowa da MUSHRAH(bride/sabuwar Matar sarki/amarya)yagama bazuwa a cikin delah gizah ta shirya cikin qarfin hali da danne damuwarta ta shirya tsaf cikin shigar alfarma ta li’ilitinta tafito Dan zuwa miqa gaisuwarta datake al’ada dakuma Dole Dole ga duk wani Wanda ke cikin masarautar delah gizah fitowa Kai gaisuwa ga duk MUSHRAn NEGES wato amaryar sarki.
##MAMUH#
_ZAFAFA BIYAR_????????????
_Alkiblah–SAFIYYAH HUGUMA_
_Makauniyar qaddara–BILLYN ABDULL_
_Dalaal–MISS XOXO_
_Mabudin zuciya–HAFSAT RANO_
_Ubayd Maleek–MAMUH GEE_
_DUKA KUDIN WANNAN DADADAN BOOKS DIN SUNA KAN FARASHIN NERA 700. WATO KUDIN PAGES KENAN. DOCUMENTS IDAN AN KAMMALA SUMA KUDIN SU DABAN.._
Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????????
0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????????
*_08085405215_*
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????????
0903 234 5899
*_Mamuhgee 21_*
Tunda aka fito da ita taga sauyi me matuqar girma da mamaki sbd tsaro da girman da ake Bata kamar za’a bauta Mata yasa taji hankalinta ya ninku gurin tashi da firgici saidai sbd a rufe take Babu me iya ganin hakan gashi takasa Jin komai daga bakin kowa bare ta tabbatarda abinda yake faruwa Abu daya data tabbatar shi shine tabbas yau gurin NEGES dinta za’a miqata Wanda hakan yasa idanuwanta masifar cikowa da hawayen tausayin kanta dana im harma Dana afia da farhat dinta da zasu rabu gashi har abada Bata ikon sauya wannan ikon akanta.
Kai tsaye babban sassan MALEEK UBAYD aka nufa da ita Wanda shine yakeda ikon fara ganinta kafin tafito kowa yaganta Dan haka suna Isa tangamemiyar kofar gurinsa masu tsaro suka bude musu sbd tsananin tsaro da securities din gurin masu Kama da samudawa anan kowa ya tsaya daga ita sai jekadi suka shige aka rufo har lokacin Babu kala jekadi Bata ce ba shiyasa batama San da ita ake tareba bare tasan inda suka shigo.
A kofar palonsa na karshe Wanda dagashi saina hutawarsa sai master bedroom dinsa Dan haka daganan jekadi taja gefe ta tsaya cikin bawa NURUn girma tace”
NURU gaki a kofar shiga gurin uban gidanki Kuma mijinki na halak malak Wanda shine zai budeki kafin kifito al’ummar gizah nason sheda ganinki wato mace me sa’a.
Da haka tayi baya ta fice daganan Takoma can farkon shigowa jiran fitowar NURU din.
Kasa motsi tayi daga inda take tsaye sbd firgicinta daya koma zallar mamaki Dan kaman Bata fahimci me jekadin tagama fadaba ta wuce.
Saitaji kaman tace aure?
Girgiza Kai tayi ahankali tareda sauke Numfashi sbd sanin ba hakan bane itada samun arzikin daukar igiyoyin auren wani sai Allah tunda harta rasa igiyoyin auren im tasan aure gareta sai rabo me qarfi Dan tuni take cikin radadin hakan har lokaci da rayuwar data samu a Paris ya mantar da ita komai yanzu Kuma qaddararta tadawo gareta Dan haka ba gudu bare tsira.
Ahankali ta tura tareda saka Kai cikin qofar da jekadi ta ‘dan bude Mata ba dukaba sbd takaitawa NURU aikin bude qofar Wanda badan kofar MALEEK bace itace zata bude Mata ita har qarshe.
Wani irin sanyin AC ne Dana wani qamshi data sani suka fara tarbanta ta maida kofar ta rufe ahankali har lokacin fuskarta arufe take.
Tunda ta iso tsakiyar palon ta tsaya cak batareda ta qara taku ba sbd bugun zuciyarta daya qaru Yana fita da qarfi Dan zuwa yanzu tagama tabbatarda qamshin datake ji musamman data iso tsakiyar palon taji yasake gauraya gurin.
So take ta yaye fuskarta taga inda take sbd firginta daya sake dawowa Amma ba hali sai kawai qafafuwanta suka hau rawa da dukkanin jikinta dama gashi ko abincin kirki tadaina ci kwana biyun sbd tsoro da shakkun datake ciki na abinda yake faruwa
Hannunta dake tsananin rawa ta daga ahankali ta shafo fuskarta dake lullube taji zufan tashin hankalin turaren MALEEK datakeji tako Ina na shiga hancinta take ta lalubo kujera ba shiri sbd jirin dayake Shirin dibarta ta ta zauna akan kejeran cikin rudewan rasa abin,
Dauke wuta tayi atake sbd Jin kusada mutum ta zauna batareda tasaniba rintse ido tayi cikin tsananin tashin hankalin rashin sanin meyene Wai yake faruwa da ita ta yunqura da sauri zata tashi taji anriqe hannunta ta tsaya cak tareda saurara abinda takeji na qamshin MALEEK zuciyarta na harbawa da qarfi kaman zata faso kirjinta.
Lullubinta taji an yaye ahankali Wanda yasata yin qasa da kanta tareda rufe idanuwanta sbd koma wanene bazata iya kallonsa Kai tsaye ba tunda shugabantane.
Tsit gurin yayi Babu wani motsi Babu wata magana tsawon mintuna shida ahakan kafin ya miqe ahankali har lokacin kayan daurin auren ne ajikinsa dasukai Masa matuqar kyau suka sake boye manyancinsa tareda bayyanarda asalin kyawunsa abun Kamar almara Amma har wani kyalli yakeyi Wanda ake cewa na anganci.
Ciki ya wucewarsa batareda yace komaiba,
Har lokacin Bata dagoba saidataji shigewarsa ta bude fararen idanuwanta ahankali ta dago Amma takasa bin inda yabi Koda kallo ne,
Hannunta daya Kama ta dago ahankali takai hancinta gabanta yasake wani irin faduwa,
Duk Wanda ya yaye fuskarka daga fitowarka wankan boyo shine yakeda Kai da ikonka Kona aure Kona negestati,
MALEEK???
MALEEK???
Toshewa kanta yayi gabaki daya Bata fahimci komaiba ta miqe har lokacin qafafunta na rawa ta fito dama wannan al’adace Kuma ancikata tunda ya yayeta.
Tana fitowa kallo daya jekadi Tai Mata ta hangi tsagwaron rudu da firgicewa atareda ita da hanzari ta qaraso gurinta cikin kulawa da girma tayi qasa da murya tace”
Ki nutsu kada ki daga hankalinki taron mutane ne keson ganin MUSHRAn MALEEK.
Cak ta tsaya tareda waiwayowa ta kalli jekadi da idanuwanta da zuwa lokacin tuni hawaye suka fara gangaro musu kenen dai ta tabbata maleek ne hancinta da wasi wasinta yazama gaskia.
Da sauri jekadi ta Kara gabanta ta boyeta tana cewa”
Allah ya taimaki mushrah wannan ba girmanki bane bayyanarda hawayenki agabanmu Dan Allah ki kwantarda hankalinki
Allah kuma ya huci zuciyarki da salama idan bazaki iya ganin kowaba ayanzu ko zamu rakaki gurin iyayenki dasuka zo kifara mgana dasu wannan sakone daga Kaleeb Kuma Yana Tayaki murnar tareda sanyawa aure albarka.
Ita gabaki daya batasan lokacinda kuka yazo mataba ba shiri jekadi ta nufi sashen Anneti da ita Wanda yafi kusa daga Nan din suna zuwa Anneti tace akaita kuryar dakinta abarta ta huta tukuna dama zataji abin wani iri tunda batada masaniyar komai.
Take aka sanar kowa ya tafi NURU tana hutawa bazata samu damar fitowaba yanzu Wanda hakan yasa kowa yafara mamakin irin sa’a da gata tareda daurewa da NURUn ta samu na take al’ada tun aranar farko.
Afia ma Bata datazo yau da mamaki Takoma sashensu sbd Bata samu damar ganin NURU ba sbd dolen Dole abarta ta huta tasamu nutsuwa Wanda itakuma tasan NURU na buqatarta yanzu sbd tayi Mata bayanin kada ta tayarda hankalinta idan sun bar Nan komai zai koma daidai zata samu Imran dinta.