UBAYD MALEEK Page 41 to 50

Kuka tayi sosai batareda tasan Kona meneneba itadai yanzu iyayenta dataji suna kusa takeson gani Dan sune zasu Mata bayanin komai ta fahimta.
Sai dare lis ta fito cikin wasu kayan dabam da aka kawo Mata akasa tayi wanka ta sauya ta fito dukkanin abindake jikinta qyalli yakeyi tundaga kayan dake jikin nata har zuwa wata siririyar diamond necklace dake wuyanta ta daqyar ta iya cin abinci tareda Anneti suna gamawa Ana kawo Mata farhat data rikice musu kwana biyu na rashin ganin NURU din tana ganin NURU ta fallo da gudu itama NURU sai lokacin taji Dan damar abinda takeji ta rungume farhat din cikin samun nutsuwa tace”
I miss you sweetie.
I miss you more my Lewa ohhh Anneti tace ke mamanace yanzu bazaki taba tafiya kibarniba kaman mum ko??
Wani dum NURUn taji takasa dagowa ta kalli Anneti dake jinsu hakama takasa bawa farhat amsa ita Tama rasa kunyace ta kamata kome?
Riqeda hannun farhat din suka fito daga sashen Anneti jekadi da sauran mabiyanta uku na bayansu suka nufi gurin iyayenta farhat nata yaba kyawu da sauyawar datayi itadai gabaki daya tafiyar kawai take hankalinta baya tareda ita abubuwa da yawane suke yawo cikin kanta wainda suka girmi tunaninta.
Suna Isa dukkaninsu jekadi daga waje suka tsaya daga ita sai farhat suka shiga bayan an wangale Mata kofar tana shiga aka rufe abal da amminsu dake zaune a Palo suka kallo qofar atare fuskokinsu na bayyanarda wani yalwataccen farin cikinsu daya kasa boyuwa itama kasa motsawa tayi sbd kasa gasgata mafarki take kokuwa gata ga iyayenta bayan wasu shekaru take idanuwanta suka ciko da hawaye suna Shirin gangarowa meryam data fito daga gurin padima tana ganin kyakkyawar halitta a tsaye cikin palon ta tsaya cak taqare Mata kallo ta tabbatarda NURUntace a guje tayo kanta tana Kiran sunanta NURU ta ware Mata hannu tareda dauketa cak suka qanqame juna tana jero Mata yarensu Wanda farhat ce kawai batasan me take cewa NURUn ba.
Daqyar suka saki juna kowanne farin cikinsa yakasa raguwa ta qaraso gurin amminta ta rungumeta tareda riqo hannun abal dinta cikin yare da muryarta me sanyi tace”
Abal ubana nagari nayi kewarku fiyeda komai da kowa nayi farin cikin ganinku cikin lafiya da wadata.
Murmushin farin ciki me sauti abal yasaki Yana dafa kanta yace”
NURU ‘yata tagari munyi farin cikin ganinki cikin koshin lafiya da nustuwar rayuwa,
Bamu taba farin rayuwaba irin Wanda Kika bamu ayanzu na aurenki da muka gani cikin ahali me girma da daraja.
Amminsu kuwa sbd farin ciki takasa cewa komai sai kallon ‘yarta takeyi cikin tsananin so da kauna tareda alfahari Wanda yasa NURUn Jin nauyin iyayenta musamman da abal ya dauko maganar auren yana Mata nasihar hakuri da nutsuwa tareda tawakalli daya santa dasu Kuma yake qara Jan hankalinta dasu akan ta rungumi wannan aure da hannu bibbiyu.
Cikin mamaki ta kalli ammi tace”
Ammi Ina padima?
Ajiyar zuciya ammin tasaki tareda Dan satar kallon abal din kafin ta kalli kofar dakin da padiman ke ciki tace”
Tana can akwance batada lafiya sosai gobema inshallah zamu koma gida sbd aje can abal dinku yasamu maganin Bata Wanda zaiyi Mata tunda ciwon na jiri ne.
Subhanallh”NURU tace cikin damuwa da kulawa kafin ta miqe ta nufi hanyar dakin bayan ta kalli farhat dake maqale da ita tacewa ammi ga farhat Nan su gaisa
Ammin tajawota ta Dora kan cinyarta tana tambayarta tana lafiya?
Tana Isa dakin tashiga Kai tsaye padima dataji zuwan NURUn tasake sassake jiki tana maqale murya tareda qaro nishin ciwonda babusa hadda hawayen da tun safe suka kasa tsaya Mata na abinda ya tsaya ya danne zuciyarta.
Da sauri NURU ta qaraso bakin gadon tana kamo padiman tana Kiran sunanta cikin tsananin kulawa Tama dungumota gabaki daya tana cewa”
Padima meya sameki bayan yau Ina cikin tsananin farin cikin ganinku ku duka.
Marairaicewa padima tayi itama tana rungumo NURUn cikin muryar datayi laushi ta ciwo tace”
NURU nayi tsananin kewarki wadda bantaba sanin haka nake kaunarkiba Saida Kika tafi nakasa nutsuwar zuciya,
Wlh NURU nayi kewarki fiyeda zato ga amed ya yaudareni yace yafasa aurena Amma tsoro yahani fadawasu abal Wanda hakan yasa suka tsangwameni”””kuka tasake Mara karfi sosai tana sake shigewa jikin NURUn tace”
Nidai NURU bansan ya zanyiba mutuwa kawai nakeson Yi sbd itace daidaini,
Dan Allah NURU ki yafemun abinda nayi Miki wlh nayi nadama tunda gashinan Naga ishara irin wadda bantaba tsammani ba.
Cikin mamaki NURU ta share Mata hawayenta tana cewa”
Kidaina kuka padima duk wannan yariga ya wuce Kuma shi amed kansa yayiwa sbd Allah zaibaki Wanda yafisa Inshallah idan har kin tsarkake zuciyarki.
Wasu sabbin hawaye tasaki tana satar kallon kofa tace”
NURU bazan taba daina kukaba sbd kuka yaganni.
Da tausayawa NURU tace”
Kidaina fadar hakan padima.
Padiman zatayi mgn saiga amminsu tashigo wadda takasa zama Jin sun Dade aciki tsaf hankalinsu Bai kwanta da kebewar NURU da padima ba Dan haka Bata Bari padima tasake mgn ba ta janye NURU suka fito inda ta zauna tsakiyar iyayenta suna sake zantawa Kamar kadasu tafi goben jintake Kamar tabisu kosu bita musamman Meryam wadda takeda burin dauka duk tayi aure Amma yanzu Kam ko ita Bata gama tantance matsayintaba bare harta dauko wani ya zauna a qarqashinta.
Saida jekadi taga lokacin kaita gurin maleek yayi tashigo ciki ta sanar musu tayi bankwana da iyayenta bayan anshigo da tarin kayan arziki anjere musu daga Kaleeb da Anneti sai babbar kyautar MALEEK wadda ko ciki baa shigo da itaba saidai idan sun Isa gida akai musu.
Dazata fice harda hawayenta padima ta riqo hannunta tana hawaye qasa qasa tace”
NURU ki taimakeni Banda lafiya mutuwa zanyi idan Ba’a nemamin magani ba ciwon zuciya me qarfi nake fama dashi tunda dadewa kullum bana iya bacci ki taimakeni ki tafi Dani ki nemamin magani NURU.
Kallonta NURU tayi a Dan tsorace tace”
Tun yaushe padima shine Baki fadaba idan yayi tsanani wani Abu yasameki fa?
Kallon abal tayi cikin damuwa da kulawa tace”
Abal meyasa ba’a fadamunba ko a wayane da anfadawa jekadi ta fadamun ta waya wannan ciwon ba abun Wasa bane zantambaya afia Inshallah zamu tafi da padima.
Wani mugun kallo ammi tayiwa padiman data bushe idonta ba wani alamar qarya ko yaudara atareda ita abal ya hade fuska tsaf yace”
Kije NURU Allah ya albarkaci rayuwar aurenki ya Hana duk wani Wanda beda fatan alkhairi sa’ar rabarki,
Padima bazata bikiba kowane irin ciwone zamu nema Mata magani Inshallah.
Kallon padima NURU tayi tana Bata hakuri ta ido da cewa tayi hkr Inshallah ta Mata alqawarin dawo da ita hannunta ta nema Mata lafiya idan nasu abal din baiyiba.
Da haka aka wuce da ita tabarsu suna binta da addua suka wuce ciki Babu Wanda yaceda padima dake tsaye idanuwanta sunyi jajir zuciyarta na wani irin zafi da harbawa.
Kai tsaye sashensu datake dasu afia aka maidata sbd saqon maleek daya Isa gurin jekadi ta hanyar Anneti cewar basai ankar NURU gurinsaba yau din gobe zasu koma,
Tana Isa ta tarar da Afia zaune tagama hada musu kayansu tsaf sbd suma dad ya sanar cewa gobe zasu koma dama amatse take dasu bar Nan din sukoma Kota samu kanta tayi tunanin abinda yakamata.
Tsayawa tayi daga bakin kofa tana kallon afia da duk damuwa da sanyin jiki ya bayyana atareda ita taji tausayinsu su duka ya dawo Mata sbd tafi kowa sanin burin afia akan dawo da mahaifiyarta gidan MALEEK gashi yanxu su duka qaddara ta bullo musu ta inda basa zato.