UBAYD MALEEK Page 41 to 50

Da wani irin kallon mamaki afia tace”
Amma ai ba lokacin period dinki bane.
Sake yamutsa fuska tayi tace”
Eh ba lokacinsa bane Amma inaga abubuwan da akaita banine a gizah dama tun can sunata sani ciwon ciki.
Kallon mamaki da tsoro afia Tai Mata takasa cewa komai sai kawai ta juya tana cewa”
Shikenan ki koma Ni zanje nadawo.
Juyawa tayi Takoma ciki tana shiga Palo tana ta sauke ajiyar zuciya ta nufi daki ta cire rigar ta sauyo da qarama Mara kauri tabar wandon ta nufi kicin direct Dan aikin abincin Rana Kota samu abinyi dazai hanata zaman tunani.
Tanayi su Fana da mum Sarah na tayata harta gama tafito ta jera a dining tana baro dining din saiga farhat andaukota daga school tun daga Palo tana shigowa tace”
Aunt NURU yau akwai drwing dazamuyi babba na _Eiffel tower_ competition ne inason nazama 1st.
Yes yes sweetie Inshallah zamuyi shi babba me kyau Wanda zaisa ki cinye afterall who’s gonna help you drw????
Da qarfi tana tsalle tace”
Our beautiful Aunt NURU.
Hmmn that sounds like a bribe sbd bantaba Jin kince our NURU ba saidai kice your NURU to yau kenan kinyadda keda afia.
Suna qarasawa kofar shiga palon kurya farhat na cewa”
No not afia,Ina nufin me and my dad since you are his wife now.
Tsit NURU tayi sakamakon hada ido datayi da maleek dayake saukowa tayi saurin dauke kanta tana riqo hannun farhat wadda ta kwace tayi gurinsa tana cewa”
Daddy barka da fitowa.
Kama hannunta yayi Yana nufar hanyar dining Yana cewa”
Hw is daddy’s little princess?
alhmdlh dad but today I have…….kallonta yayi cikin nustuwa yace”
Go and freshen up first kafin kizo naji menene.
Da gudu tayi ciki tabarsu tsaye sai alokacin NURU tadan gyara tsayuwa tana rage murya qasa qasa tace”
Barka da fitowa.
Kai kawai ya gyada Mata ya nufi dining Wanda yasata Dole binsa Dan serving tunda dai Babu kowa agurin.
Zama yayi taqaraso cikin Jin nauyin kayan dake jikinta musamman dayake kujeransa tana seti da inda take tahowa tamafi Jin kunyar rigar dake jikinta din sbd Ana ganin yanayin kalar bra dinta fara ta ciki sbd transparent ce Amma ba sosaiba Dan Bata tana tunanin har lokacin Yana gidaba.
Tana qarasowa tafara serving dinsa cikin nutsuwar Dolen data tattarowa kanta.
Tana gama zuzzuba Masa ta nufi kicin ta hado drink dinda tasan yanasha tareda ruwa masu sanyi Amma ba sosaiba takawo ta aje tareda zuba Masa drink din a cup ta Dan dago kadan ta kallesa zatai magana ta rude ta kasa sbd kallon dayayi Mata yasata neman rudewa hartana neman fada Masa Bata saniba Saida ya tareta da hannunsa daya Wanda ya ba tsammani ya sauka daidai kan shafaffen cikinta daga ita harshi da saida suka kalli juna ya dauke Kai Yana kamewa tareda janye hannunsa tayi saurin juyawa tabar gurin jikinta na neman sakewa sbd duk duniya Babu Wanda yataba taba mararta sai yau gashi abin kamar na tsautsayi batasan yaushe rigarta tadan dagaba Dan kuwa direct taji saukan dumin hannunsa akan skin dinta da gudu taqarasa daki ta nufi toilet da gudu sbd har wani fitsari fitsari takeji na shiga rudu.
##MAMUH#
_ZAFAFA BIYAR_????????????
_Alkiblah–SAFIYYAH HUGUMA_
_Makauniyar qaddara–BILLYN ABDULL_
_Dalaal–MISS XOXO_
_Mabudin zuciya–HAFSAT RANO_
_Ubayd Maleek–MAMUH GEE_
_DUKA KUDIN WANNAN DADADAN BOOKS DIN SUNA KAN FARASHIN NERA 700. WATO KUDIN PAGES KENAN. DOCUMENTS IDAN AN KAMMALA SUMA KUDIN SU DABAN.._
Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????????
0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????????
*_08085405215_*
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????????
0903 234 5899
*_Mamuhgee 24_*
Saida safe dukkaninsu sukasan farhat batada lafiya Koda suka Isa dakinta tana zaune jikin dad dinsu Yana zaune bakin gadonta sanye da black jallabiya ta maza me tsananin taushi sai kyallin maiqo takeyi alamar ta masu abun duniya ce.
Itace agaba ashigowa kafin Afia Amma tana ganinsa tayi slow afia ta wuceta tana qarasa dayan gefen ta farhat din ta zauna tana cewa”
Gud morning dad,
Farhat bakida lafiya bamusaniba mum Sarah ke fada Mana yanzu da safen Nan.
Dago fuskarsa yayi dake fayau dinta sai wani daukan ido take ya kalleta da idanuwansa Wanda itama daidai shi ta sata kallo suka hada ido tayi saurin sauke idonta muryarta da wani irin salon sanyi dabata saniba tace”
Barka da safiya.
Har lokacin kallonta yakeyi
Tasake dagowa ta saci kallonsa suka sake hada ido sai kawai tunanin ganin dayayi Mata jiya da daddare kusan Babu komai a jikinta take wata matsananciyar kunya ta mamayeta batasan lokacinda ta rufe idoba ta fita da gudu Kamar karamar yarinya.
Da mamaki afia ta dago ta kalli kofar kafin ta juyo ta saci kallon dad dinta da bataga alamar ma yasan da NURU tashigo bare tace kofar yake kallo ta maida kallonta kan farhat tana cewa”
Sorry baby aunt NURU taje Sanyo kayane sbd batasan dad na Nanba ta taho da sleeping dress ajikinta shine Takoma ta sauyo nasan kin matsu tazo gurinki ko baby?
Gyada Kai farhat din tayi tana kwantawa jikin afia din tace”
Afia I saw mum yesterday a school dinmu she was there before I fainted……
Da sauri AFIA ta dago ta kalli farhat din tareda kallon dad dinsu da sauri shima saidai ko Gama juyowa batayiba ya miqe ya fice kamarma baiji me farhat taceba afia tabi bayansa da kallo kafin tadawo da kallonta kan farhat cikin mamaki tace”
Baby dagaske Kinga mum?
Gyada Kai tayi tana kallon afia din tace”
Eh naganta tazo kafin ta iso gurina I fainted daganan shikenan saidai Naga dad kawai.
Wani yawu afia ta hadiye kafin ta ta danne mamakinta da farin cikinta tana miqewa tace”
Ok baby Bari naje naturo Miki NURU tazo tayi Miki wanka da brush saita Baki abinci akwai abinda zanyi yanzu na gaggawa ok baby.
Wucewa tayi ta fice da sauri ta nufi dakinsu ta janyo doguwar riga tasanya akan kayan baccin jikinta ta dauki wayarta da sauri ta fice ta nufa library dinsu Dan Yin waya.
Doguwar kimono NURU ta doro akan kayan jikinta na bacci kafin ta wuce ta nufa kicin ta hadawa farhat Dan guntun breakfast sharp sharp ta dauko a qaramin faranti ta nufa dakin tana adduar Allah yasa ya fice.
Ganin baya dakin yasata qarasowa da wuri ta ajiye tray din tana cewa”
Sweetie kiyi hkr bamu San bakida lfy ba,jiya ma anan nayi wanka Amma banluraba sbd hankalina yatafi wani gurin dabam na……kasa qarasawa tayi tana sake tunano abinda yafarun sai kawai ta sauya zancen da sakin qaramin murmushi tana cewa”
Ok sweetie muje ayi brush kizo ga breakfast sai asha magani.
Tayar da ita tayi suka nufi toilet din suka shige.
Harsuka gama komai har wanka da Shirin farhat din kafin suka fito zuwa nasu dakin itama NURU tayi wanka ta shirya cikin doguwar riga suka fito Palo ta kunna Mata cartoon takoma ciki tayi Shirin makaranta tazo ta fice har lokacin afia Bata shigowaba tanacan.
Tsaye take cikin libry din idanuwanta sunyi jajir sbd tsananin baqin cikin dake mamaye da zuciyarta ayanxun datake waya da mum dinta cikin tsananin sanyin murya da sarewa tace”
Haryanxu Babu ‘yayanki acikin ranki kenan?sbd wani burinki na duniya mum kike fadar haka? Tayaya kike tunanin dad zai iya rayuwa ahaka for how long kikeso yayita jiranki?mum please ki……