UBAYD MALEEK Page 51 to 60

Abal ya tabbatarwada padima duk yaji wani mugun labari yasamu NURU bashi ba ita har abada hakama ammi Kuma ahaka taji takuma amince saidai ta qudurta bazatayiwa NURU komaiba kodan kalaman iyayensu saidai bazata dawoba saitasamu nata rabon na ingantacciyar rayuwa ta taho tabar amed da mugun mamaki da baqin cikin daya kaisa Shan mugun qudurirrika akan ko zaiyi yawo tsirara bazata jimaba zaimata aikinda ko wata bazata rufaba acan saita dawo saidai Kuma wani tunanin daban yasashi Kiran mahaifinsa dake cikin amintaccin NEGES yafada Masa zuwan padima Wanda shima atake yafadawa NEGES.
Kallon jekadi Anneti tayi lokacinda take miqa Mata saqon NURU na wata sabuwar madarar raqumi da akaiwa Hadi da sinadarun Karin kyan fata Da wasu abubuwan ma tace”
Wannan sakon NURU ne da hannunki kullum Zaki ringa Bata tana shansa harya qare sbd na yanke shawaran kece Zaki Kai Mata ‘yar uwarta ki zauna acan sai lokacinda tagama ziyararta kudawo tare sbd dalilai na Kare maleek da iyalansa duk da ‘yar uwartane Amma bamusan Yaya halayenta sukeba musamman gashi ziyarar tazo a bazata.
Yanda kikace haka za’ayi Anneti.
Miqewa tayi ta fice Tana sake miqa gaisuwarta.
Tana fitowa duk da darene sosai saitaji tana buqatan zuwa ta duba lafiyar ‘yar amanar NURU Dan kuwa tamkar amanartane NURU tabata Dan haka ta nufa sashen Kai tsaye.
Tun daga nesa taga kamar wutar sashen a kashe take sai abin yabata mamaki ta Dan dakata tareda dudduba sauran sassan duk hanyoyinsu wuta a kunne.
Daga can ciki kuwa gyara tsayuwa yakoob yayi Yana kallon padima dakewa tarin darhamai da danyen zinarai daya zube agabanta kallon haramun Kamar zata cinyesu abakinta yace”
Yaya Zaki iya kokuwa??
Hadiye wani yawu tayi tareda danne kwadayinta ta kallesa tsoronta na bayyanuwa tace”
Bazan iya kisaba wlh sbd ban iyaba bantabayiba.
Wani kallon Kai tsaye yayi Mata Yana sake zuba Mata wasu akan wainnan yace”
Ba kisa zakiyiba zuba Masa kawai Zakiyi a abunsha sauran aikin anan zamu qarashi,
Idan Kika cika wannan aikin akwai alqawari me girma na cikar buri da akai Miki alqawari daga shugabana haka zalika Kuma fitar maganar daidai take da bakin rayuwarki.
Wani kallon tsoro biyu tayi Masa kayan cikinta na juyawa sbd duk balainta batakai na kashe wani ba
Waninma maleek datake ‘dan yiwa kanta kwadayinsa dukda tasan da wuya ita ko bashiba burinta dai gidan mulki
Yanxu ta Yaya zata iya kisa?.
Kuma aikinma batasan na ainihin wayeba tunda yadaice shugabansa bai fada ko wayeba.
Ciro wani qyalle yayi ya miqa Mata tareda cewa wannan ki warware gashinki ki dauresa aciki idan kinje can so daya kawai akeso ki juye Masa duka a abunsha kawai Banda abinci,
Idan kinzuba kiyi flushing din kyallen.
Miqa Mata yayi ya juya ya fice Yana cewa”
Sauran bayanin idan andawo Nan zakijisha.
Fitowa yayi fuskarsa rufe da kayan bayi Mata ya wuce batareda waiwayeba ya fice gabaki daya daga gurin.
Da mamaki jekadi tabi bayan baiwar data fito daga sassan Dan Haka ta qaraso da sauri tana sake duddubawa kafin ta nufa kofar Kai tsaye tashiga
padima dataji motsi tayi saurin boye darhaman tareda janyo abincinta da bataciba gabanta tareda zaunawa ta kishingida tareda rufe idanu har jekadin tashigo.
Da rashin yarda da mamaki jekadi ke kallon koina kafin ta kalli padima Kai tsaye tace”
Waye yafita yanxu daga Nan?
Bude idanuwa padima tayi tana ganin jekadi tayi saurin miqewa tareda russunawa tace”
Allah ya taimaki jekadin jekadai.
Sake maimaita tambayarta jekadi tayi tana kallon padiman har lokacin.
Cikin girmamawa tace”
Abincine takawo sbd dazu Koda aka kawo banajin dadin cikinq nace amaida zuwa anjima adawo dashi.
Kallon tsaf jekadi Tai Mata kafin tayiwa abincin da aka kawo din ta tako ahankali tana kallon abincin takai hannu ta bude tayi Masa kallon tsaf tareda Dan Kai hannunta a kaikaice taji dumin abincin Wanda baida dumi ko kadan ta dago ta kalli padiman kallon tsaf tasaki wani murmushin bazata dayasa padiman Dan washe Baki itama tace”
Saida safe ki huta lafiya”” ta juya ta fice batareda yiwa padima sauyiba ko alamar komai.
Tana fita padima ta sauke ajiyar zuciya tareda warware gashinta tasake gyarawa kullin zama cikin yalwataccen gashinta.
Ta zaro uwar dukiyar data boye tana tunanin inda zata kaita kafin tadawo.
Zagaye tafara cikin tsananin tsoro da firgici Dan ganinta da wannan darhaman masu tarin yawa zasu iya kaita lahira, gabaki daya tsoro da tashin hankali takeji wace masifar ce wannan daga zuwanta ko Paris din Bata qetaraba ta hadu da wannan balain yanxu idan taqi Yi ance abakin ranta,
Idan tafadawa wanima abakin ranta,hakama idantace zata tona tafada gskia batasan waye ya aikoba Dan aikenma fuskarsa rabi arufe babbar masifar datafisu shine idan ta aikata tayi kisan Kai ga Wanda tasan ko gunduwa gunduwan gawarta Kare suka samuci tayi arziki to ita Kam wane tashin hankali ne wannan.
Tana hada wani mugun zufa ta dauresu waje daya tareda cusawa cikin kayanta na sawa takoma gefe ta zauna har lokacin gumi take hadawa ta Nemo numbern amed sbd sanin shikadaine abokin cin mushenta na rayuwa.
Yana ganin kiranta yasaki ajiyar zuciya sbd abinda yake jira kenan Dan mahaifinsa ya fada Masa komai Dan shine yaje gurin padiman.
Dauka yayi cikin matsewa sbd har lokacin takaice yake da ita yace”
Lafiya dai ko Kira da wannan tsohon daren.
Wani wahalallen numfashi tasaki cikin qasa da murya tace”
Amed inason ganinka a Giza komai tsanani gobe Dan Allah.
Kallon mahaifinsa yayi sbd tun Rana ya iso Giza din yau shima sbd wannan tarkon nasu ya Dan sake Bata murya yace”
Sbd me zanzo kiranki?
Kinga karki rainamun da hankali Mana.
Cikin rawar murya tace”
Dan Allah amed kazo kokuma idan bazaka samu zuwa ba ka hadani da mahaifinka wlh Ina cikin wani mummunan tashin hankali ne na….. shiru tayi tana tuno maganar da Dan Aiken yafada Mata dazu hawayen cikin idonta suka gangaro Mata ta sauya zancen da cewa”
Akwai dukiyar NURU ce a hannuna inason baka ka Adana min harna dawo sbd bazan bataba batamasan da itaba.
Washe Baki yayi Kai tsaye Yana cewa”
Ganinan tafe yanzu kuwa.
Da mamaki tace” yanxu Kuma?
Kana gizah ne dama?
Da sauri yahau gyaran zancen da cewa”
Aa inanufin zan fadawa mahaifina zaishigo ya karba ta sirrance.
Bata yadda dashiba Dan taji gargada a zancensa Amma yanxu tunda tanason kubuta daga wannan saita ciro maganin da aka Bata ta Raba biyu ta bude gaban wata sarqar daham dake cikinsu tasaka dayake qaramine saiya shige ta maida Dan locket din ta rufe tana cewa”
Idan ta ‘batarmin acan tareda zamuje qasa Dan ga shaida nan nasaka acikin kayan Kuma bazaka taba ganowaba.
##MAMUH#
_ZAFAFA BIYAR_????????????
_Alkiblah–SAFIYYAH HUGUMA_
_Makauniyar qaddara–BILLYN ABDULL_
_Dalaal–MISS XOXO_
_Mabudin zuciya–HAFSAT RANO_
_Ubayd Maleek–MAMUH GEE_
_DUKA KUDIN WANNAN DADADAN BOOKS DIN SUNA KAN FARASHIN NERA 700. WATO KUDIN PAGES KENAN. DOCUMENTS IDAN AN KAMMALA SUMA KUDIN SU DABAN.._
Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????????
0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????????
*_08085405215_*
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????????