UBAYD MALEEK Page 51 to 60

Dasauri ta dauko cup din ta matso ta miqa Masa tareda tsayawa akansa Kamar zata fasa kuka sbd Jin yanayin take har cikin ranta.
Kurbi daya yayi ya dakata sbd abinda yakeji ta matsosa sosai cikin kulawa da damuwa tace”
Yace duka za’a shanye.
Ko kallonta Bata samu damar yayiba yasake daga cup din yasha Yana rufe ido tareda shanyewa ya miqa Mata cup din da sauri Yana saukowa gadon ya nufi toilet yafara kelaya wani irin aman azaba Wanda yasata kasa hkr tabisa ciki idanuwanta na cikowa da ruwa musamman ganin Aman hadda jini sosai aciki ta rude tana dafa bayansa da har lokacin yake bayyane ba Kaya ajikinsa Dan abin kamar daurin Rai da dai towel dinsa har lokacin be kunce ba koya kunce akwai qaramin gajeran wando ajikinsa.
Saidayayi mugun amai sosai kafin taji take zafin jikinsa ya sauka gabaki daya ta zuba Masa ruwa ya wanke fuskarsa da bakinsa ta fito tabarsa aciki ta sake gyara Masa gadon da duk suka cukuikuye sbd rudewa ta dauki cup din ta fice daga dakin tun kafin yafito sbd ta lura tun cikin toilet din yadawo MALEEK dinsa.
Gurinsu jekadi ta Isa da sauri itama cikin sa’a ta tararda ta amaye komai gabaki daya ta shigo suka kamata tareda goggge Mata jiki suka kwantar da ita take baccin wuya ya dauketa sai alokacin dukkaninsu suka saki ajiyar zuciya me qarfi abinda takeji tokare a zuciyarta ya fada Mata ta dafe goshinta tana sake sakin jerin ajiyar zuciya kafin ta dago dmta kalli mum Sarah tace”
Menene yafaru bayan shigewata da daddaren?
Ajiyar zuciya mum Sarah tasaki tareda sauke Kai qasa cikin rashin sanin takamaimai na komai tace”
Bansaniba
Kawai dai abinda nasani shine jekadi tashigo dakina acikin wannan halin
Abu daya tace shine na jininta na quna.
Wani sabon numfashin takuma saukewa me zafi kafin ta bude Baki tace”
Shikenan zuwa da safe idan duk sunji sauki zamuji abinda ya samesu
Ki lura da ita Mr Omar zai Kira Dr bayan asuba.
Juyawa tayi ta fice jikinta a matuqar mace sai yanxu takejin tsamin jikin guje gujen dataitayi daga sama zuwa qasa ta nufi dakinsu ta fada kan gado tareda lumshe idanu tana godewa Allah dayasa komai ya tsaya nan Amma Kuma zuciyarta na Bata wani irin yanayi Mara Dadi na afkuwar al’amarin sbd idan har ciwon maleek ne kaman yanda yasaba to ita jekadi fa?
Gabaki dayama wannan ciwon wani babban abune na daban sbd azabar dasuka Shiga sai me qarfin jini ne kawai zai iya dauka dan kuwa taga tsananin azabar dasuka shiga musamman MALEEK.
Bude ido tayi ahankali tasake lumshewa har lokacin tanajin dumin jikinsa daya Shiga jikinta sbd ba qaramin full body contact suka samu ba Dan ita yacire rigarta shikuma dama Babu anasa jikin.
Saurin rintse ido tayi da qarfi tana cire tunanin cikin ranta ta gyara kwanciya Dan tasamu bacci ya Dan dauketa kafin asuba.
##MAMUH#
_ZAFAFA BIYAR_????????????
_Alkiblah–SAFIYYAH HUGUMA_
_Makauniyar qaddara–BILLYN ABDULL_
_Dalaal–MISS XOXO_
_Mabudin zuciya–HAFSAT RANO_
_Ubayd Maleek–MAMUH GEE_
_DUKA KUDIN WANNAN DADADAN BOOKS DIN SUNA KAN FARASHIN NERA 700. WATO KUDIN PAGES KENAN. DOCUMENTS IDAN AN KAMMALA SUMA KUDIN SU DABAN.._
Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????????
0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????????
*_08085405215_*
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????????
0903 234 5899
*_Mamuhgee 28_*
Da asuba Saida afia ta tada ita sbd nannauyan baccin daya dauketa ta bude ido daqyar ta kalli afia kanta na wani irin sarawa sbd nauyi dayayi mata sbd rashin bacci da damuwar abinda yafaru cikin daren.
Tashi tayi daqyar ta nufi toilet tashiga tayo alwala tafito ta tsaya gefen afia ta tada tata sallar.
Suna idarwa afia ta ringa satar kallonta a kaikaice sbd duk wani motsin NURUn qamshin turaren dad dinta takeji ajikinta yana tashi.
Shiru tayi sbd batamasan mezatace ba Amma mamakinta anan Ina NURU ta hadu da qamshin?
Ta Yaya?
Ganin idan tayi magana Kamar ta muzanta NURUn ne yasata yin shiru ta Adana kalamanta tukuna.
Gari nafarayin haske NURU ta fito ta nufi dakin mum Sarah ta dubo jekadi har lokacin bacci takeyi saita fito ta nufi dakin padima ta tura tajisa arufe taga key din ajiki ta waje saita bude dakin tareda shiga har lokacin bacci padiman keyi ta qarasa bakin gadonta ta taba bargonta ahankali zata tasheta
Padiman tasaki wani razanannan ihu tana zabura zaune gumi duk yagama jiqata idanuwanta duk a waje take kallon fuskar NURU jikinta na Dan rawa ta sharce gumi tana saukowa daga gadon.
Da mamaki da tsoro NURU ke kallonta tace”
Lafiya padima?
Mafarki kikayine kike wannan ihun kina hada gumi haka?
Kasa kallonta padima tayi sbd har lokacin gumi takeyi cikin tsananin firgicin mummunan mafarkin datayi batareda ta waiwayo ba ta nufa hanyar toilet tana cewa”
Mafarki nayi sbd banyi addua ba na kwanta.
Bayanta NURU tabi da kallo cikin mamaki sosai kafin ta juya ta fice daga dakin ta nufi kitchen tana Danna Kiran Mr Omar.
Saidata tabbatarda ita kadaice a kicin din tace”
Gud morning Mr Omar.
Barka da tashi ranki ya dade”yafada daga can bangaren cikin girmamawa.
Shiru tayi cikin nazarin abinda zata fada Masa…shikuma Jin hakan sai ya gyara murya cikin nutsuwa da Bata tabbaci yace”
Dr Damien yazo ya duba MALEEK tun six harya wuce ma inshallah komai ya wuce.
Sake yin shiru tayi tana wani nazari kafin ta sauke ajiyar zuciya me sauti tace”
Mr menene wannan ciwon?
Shin kodai wani abun sukaci kokuma ya taba skin dinsu?
Tsit Mr Omar yayi Jin tambayar tata saidai baija shirun da tsayiba Dan kada ya Bata hope na zai amsa tambayar ya Dan sake gyara murya cikin Bata girma yace”
Ranki ya dade Inshallah allergy ne kawai Amma bana saka ran da…
Qin qarasawa yayi tareda dauko zancen itama jekadi kowane lokaci duk zasu farka lafiya Inshallah.
Ajiyar zuciya ta sauke zuciyarta na wasi wasin abinda yace na cewan allergies ne,
Wane irin allergy ne wannan me tsananin azaba.
Daga sama tajisa Yana qara saita murya yace”
Ranki ya dade idan na hali Dan Allah basai ‘yayan MALEEK sunsan meya faruba,kowama Dan Allah kada yasani sai maleek ya tashi anji daga garesa shida jekadin.
To” kawai tace tana kashe wayar cikin ‘yan tunane tunanen dasuke shigarta.
Kasa yin komai na breakfast tayi tabarwa Fana aikin ta wuce daki tashiga wanka tafito lokacin har afia tagama shirinta itama tahau shiri suna gamawa ko breakfast NURU batayiba afia ce kawai tayi suka wuce makaranta.
Tunda suka Isa NURU batada sukuni tunanin halinda yake ciki ya hadu da karatun exams dinta ya hargitsa Mata Kai har wani jiri jirin ciwon Kai takeji sauqinta dayane daga yau tagama exams dinta hutun gaske zatayi kafin sudawo hutu inshallah sbd tana tsananin buqatar hakan.
****
Qarfe goma Sha ‘daya da mintuna shida maleek ya sauko ahankali yake tafiya cikin nutsuwa da kamewa Yana sanyeda jallabiya milk sai daukan ido takeyi sbd maiqo da laushin yadin jallabiyan.
Mr Omar dayake tsaye tuntuni Yana jiransa a palo yayi saurin sake sauke kansa cikin tsananin biyayya ya sake ja baya maleek ya wuce yabi bayansa cikin tsananin girmamawa yace”
Barka da fitowa MALEEK.
Allah yaqara lafiya da Nisan kwana tareda tabbataccen tsari da kariya.