UBAYD MALEEK 1-END

UBAYD MALEEK Page 51 to 60

Yawwa.

Dama tanason sanin halinda yake ciki duk da tasan yanzu ko kallo bazata samu daga maleek dinba Amma tanason tabbatarwada yasamu lafiyar Dan haka ta dauki tray din ta fito kenan ta hadu da farhat tana cewa”

Aunt NURU abincin daddy ne wanna?

Gyada Mata Kai kawai NURU tayi tana cewa’ 

Bari na aje anan ki jirani na sanyo jallabiya saimu Kai Masa.

Jekadi dake fitowa daga kicin ta matso gaban NURUn a natse tace”

Abincin maleek ba’a barinsa ako Ina shiyasa ko jiya yasamu allergy.

Kallon kanta tayi taga shigar Sam Bata daceba da zuwa gurinsa zatai magana jekadi ta sauke Kai tana cewa”

Afito lafiya.

Numfashi me sanyi ta sauke tareda daukan tray din tana satar kallon hanyar dakunansu tafara hawa saman sbd kada afia ta fito.

Tana shiga palon farko ta tsaya kofar palonsa na kurya tana sauke ajiyar zuciya sbd gabanta dake faduwa ta kalli farhat data bude kofar Kai tsaye ta shige tayi gurinsa da gudu Yana zaune kan royal kushin yayi crossing fararen qafafuwansa da Babu takalmi sai daukan ido suke kaman baya taka kasa dasu.

Shigowa tayi qafafunta na Dan rawa ta qaraso ta ajiye tray din kan table tana dagowa maleek dinma na waiwayowa yayi Mata kallo daya ya juya sbd kayan dake jikinta.

##MAMUH#

_ZAFAFA BIYAR_????????????

_SAFIYYAH HUGUMA_

_BILLYN ABDULL_

_MISS XOXO_

_HAFSAT RANO_

_MAMUH GEE_

_DUKA KUDIN WANNAN DADADAN BOOKS DIN SUNA KAN FARASHIN NERA 700. WATO KUDIN PAGES KENAN. DOCUMENTS IDAN AN KAMMALA SUMA KUDIN SU DABAN.._

Ɗaya___300

Biyu____400

Uku_____450

Huɗu____500

Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????????

0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????????

*_08085405215_*

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????????

  0903 234 5899

*_Mamuhgee 29_*

_*YERWA INCENSE & MORE*_

_(The scents with diff essence for YOU& your HOME)_

_(MASARAUTAR KAMSHI)_

_Ina masu neman kayayyakin kamshi yan nahiyar ketaran chadi da Senegal? Kai harma da ingataccen had’i yan bornu? To ku matso domin nesa tazo kusa…_

_YERWA INCENSE & MORE: Sun zo muku da kayayyakin turaruka kamar haka:_

_Khumra kowacce Iri._

_Turarukan Wuta_

_Mopping khumrah_

_Washing khumrah_

_Bathing khumrah_

_body mist_

_kullaccam_

_scented hair cream/spray_

_wardrobe balls_

_carpet spray_

_air-fresheners_

_scented pebbles_

_body sprays_

_oil perfumes_

_Perfumes_

_kabbasa_

_burners_

_coal igniter_

_tong_

_kasko_

_english coal_

_dilke&halwa set_

_scented body mist_

_kai dama sauran kayayyakin da bamu ambata, YERWA INCENSE AND MORE, Na tura kayayyakin su koina a fadin Nigeria da ketare. Domin tuntubar su. Suna instagram: _@yerwaincense_and_more. Ko Facebook site:YERWA _COLLECTIONs. Ko a duba su ta number su: _*08095215215/09044191709*! _

_suna bada kayan su kan sari ko sayi dai-‘dai_

**********

Harta Gama zuba Masa ta ajiye Bai Bai Kuma waiwayowa ba amfani yake da wayarsa sai farhat dayake tankawa ahankali,

Juyawa tayi zata fice batareda ya kalla inda take ba yace”

Kijira ki tafi da kayan.

Dakatawa tayi tareda sauke ajiyar zuciya boyayya sbd atlas dai yanuna yasan da shigowar mutum ba farhat kadaiba.

Juyowa tayi ahankali tadawo daga gefe ta tsaya tana Dora kallonta kan tv dake aiki Sam bama murya kusan gabaki daya Wanda ta fahimci qaidar iya muryar tv dayake buqatane ahakan.

Ganin tsayuwar Kamar zata damesa saita sulale ahankali Takoma palonsa na farko ta zauna tana kallon tsari da haduwar palon Wanda kusan komai na palon milk ne.

Juya idanuwanta tayi kan wani qaramin hoton LAILAH dake cikin qaramin milk frame tana tareda maleek din dukkaninsu cikin qananun Kaya black shi Yana zaune gabaki daya hankalinsa nakan wayar dake hannunsa itakuma ta rungumosa tana dariya fararen haqoranta tas a bayyane sunyi kyau.

Dokawa taji qirjinta yayi ta dauke kanta daga kallon hoton tareda Dan hadiye yawu tana qoqarin Wasa da yatsun hannunta.

Kasawa tayi tasake juyowa gabaki daya ta qurawa hoton ido tana qarewa LAILAH kallo.

Kyakkyawace da kyanta yake a bayyane,gata da kyawun jiki Kamar ba ita ta haifi afia ba Kamar dai yayarta,

Wayewarta ko acikin hoton a bayyane take sbd yanayin shigarta da yanda take nanuke ajikin MALEEK Wanda son datake Masa yake bayyane afili shima alamunsa da yanda hankalinsa ke kwance qarara a hoton ya bayyanarda soyayyarsa ga matarsa.

Sake dauke kallonta tayi daga hoton jikinta nayin sanyi bugun zuciyarta na qaruwa ta waiwaya gefenda kofar dakin lailah din saitaji jikinta na Gaza Mata ta miqe tabar gurin ta koma cikin palonsa wannan karon sallamarta daqyar ta fito qasan maqoshi sbd shaqewar dataji maqoshinta yayi.

Qarasowa tayi kanta a qasa ta dauki tray din ta fice batareda tabi takan farhat ba dasukazo tareba.

Tana saukowa kitchen takai kayan ta wanke da kanta ta maidasu gurinsu ta fito ta nufi daki batareda Takoma gurin padima ba.

Tana zuwa daki ta fada kan gado takwanta tareda rufe idanuwanta tana sauke ajiyar zuciyarda batasan Kota mececeba.

Har dare Bata sake fitowa daki ba Koda padima tazo ta tambayeta ce Mata kawai tayi kanta na ciwo hutu take buqata.

Padima Bata damu da hutun da NURUn tace tana buqataba ta zauna gefenta tareda kallonta Kai tsaye tace”

NURU inason zankoma gida Kuma cikin gaggawa sbd kwana biyun Nan inata mafarkai marasa Dadi na abal da ammi kaman dai da akwai babbar matsala Dan haka Ni inaga zankoma gurinsa kada ya zamto babuke akusa Babu Ni.

Tashi zaune NURU tayi tana kallonta da yanayi na damuwa tace”

Amma ai nayi waya da abal ko dazu Kuma banji alaman matsala ko wani damuwaba bayan haka meye amfanin zuwanki kema idan Baki ga likita ba akan Taki lafiyan.

Yamutsa fuska tayi tana cewa”

Kibar maganar nawa ciwon sbd bana tunanin zan tsaya ganin likita naji sauqinsa sosai Dan dama kila hadda damuwar rashinki akusa ne yasa abin yayi tsanani yanzu Dana zauna dake naji saukin komaima kawai damuwata anan iyayenmu ne kiyi tunani kema kinsan Koda damuwa abal bazai taba Bari kiganeba barema Koda na baro fa bayajin Dadi kwana biyu Yana fama da ciwon tari…

Da wata sabuwar damuwar NURU ta kalleta tana cewa”

Amma meyasa tun zuwanki Baki fadamun abal bayajin dadiba padima?

Kinga shine ya gargadeni akan kada na fada Miki Kuma ko yanzu kada kiyi Masa maganar Dan zaisan cewa nafada Miki 

Nidai gida zankoma jibi kiyi Shirin duk abinda Zaki bani da Wanda Zaki karbomin daga MALEEK,

Ni bana wannan ba NURU meyesa nakeganin kaman ba zaman aureba kike a gidan nan??

Dan Babu wani alamari daya danganci aure danaga Yana faruwa dake.

Shiru NURU tayi tareda dagowa ta kalli padiman tsawon mintuna sbd batasan me zataceba tunda kusan gaskia padiman tafada, ta sauke numfashi tareda Miqewa tana cewa”

Kidaina wannan tambayar padima 

Ba lallai komai ake bayyanawaba 

Tunda dai akwai auren komaima ahankali za’ayi.

Miqewa padiman itama tayi tana cewa”

To dai iyayenki saisu daina dukan gaban ‘yar so tana auren MALEEK na delah gizah Dan kar ayi zaton wuta a maqera ajita a masaqa.

Juyowa NURU tayi ta kalli padiman da manyan idanuwanta ta matso daf da ita harsuna shaqan juna tace”

Ko a kasuwa za’a jita ba ruwanki bane ki Kama bakinki kadaki fadawa su abal abinda zaisasu damuwa sbd padima ba ruwanki da abinda zai kawo musu bacin Rai ko damuwa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button