UBAYD MALEEK Page 51 to 60

Murmushi padima tasaki cikin isashiyar muryarta tace”
Kiji da matsalar gabanki ta zaman aikin gida da renon mijin wata Ni kibarni zanji dasu abal din naki idanma labarin yakaimusu wata Rana Dan yanxu banjin zanyi lokacin isar musu da wannan labarin inada nawa sabgogin kawai dai kishirya min komai nafada Miki gida zankoma.
Wucewa tayi ta fice daga dakin tabar NURU nabinta da kallon takaici takaici sbd halin padima dai haka yake tun suna yara saidai kwana biyun Nan datazo musu tayi tunanin tafara sauyawane shiyasa taketa kiyayewa sbd kada suyi halinsu agabansu afia subarwa kansu abin takaici.
Zaunawa tayi kan kujera tana furzar da numfashi tace”
Zanyiwa jekadi magana ta maidaki tun kafin mufara halin acikin gidan Nan tunda kinji kingani kinfasa neman lafiyar ai shikenan kije ko Dan lafiyar iyayenmu.
Da daddare har daki tasamu jekadi zata zauna jekadi tayi saurin miqewa tana cewa”
Ba girmanki bane mushrah idan kinason ganinane duk inda kike zan sameki naji bayaninki ko umarninki.
Murmushin yaqe kawai tayi sbd duk ranta a jagule yake yau din daga wannan sai wannan.
Daga tsayen ta kalli jekadi da taushin murya da zallar gajiya da damuwar komai tace”
Jekadi padima zata koma gida jibi nafadawa Mr Omar yayi muku komai na tafiyar,
Idan kunje kibata wadataccen kaso acikin wainnan dukiyar dake can na dukiyar auren……kasa karasawa tayi sbd Jin nauyin fadar kalmar aurenta
Itakuma jekadi Jin tayi shiru tace”
Yanda kikace haka za’ayi Inshallah”sbd ta fahimci abinda take fada.
Gobe ku shirya saimu fita akaiku kuyi siyayyar abinda kuke buqata.
Godiya jekadi keyi Allah yaqaro girma da kusanci tsakainki da MALEEK tareda tabbaciyar qauna.
Shiru tayi batareda tace komaiba saima sanyi da jikinta yayi ta juya zata fice jekadi tadago takalleta cikin tausayi da kaunarta saitaji bazata iyaba ta gyara tsayuwa tareda aje matsayinta na jekadi takira sunan NURUn cikin tsananin kulawa kaman yanda ta Saba a da.
Tsayawa NURUn tayi tareda waiwayowa ta juyo gaba daya damuwarta na raguwa sbd tasan jekadinta ta Da ce kafin tazama Matar maleek.
Takowa jekadi tayi tazo har gabanta takamo hannunta tajata zuwan kan kujera ta zaunar da ita kafin itama ta zauna ta fuskanceta cikin kulawa a natse tafara cewa”
NURU aure da kike gani Kona soyayyane saika dage da kulawa da naci akan wasu abubuwan sbd kusan a rayuwar aure ke mace kece zakija ragamar Kama hanyar zuwa wani mataki,
NURU kinshigo wata irin baudaddiyar rayuwar aure wadda kike buqatar juriyada kokartawa kafin kisamu matsayinki na Matar gida idan ba hakaba rayuwarki da quruciyarki zasu qare su tsufa cikin tausayi me tsanani,
Aure gidan sarauta musamman irin naki auren dayake da qalubalai da tazarori masu yawa,
Shawara daya anan itace ki maida hankali ki dage karki dage a Gina karatu kawai ki zauna kiyi nazari aurenkima kina buqatan dage Masa Dan bawa kanki suna da matsayi a gidanki sbd karki tsufa agidanki bakisan suna ko matsayinki a gurin Wanda kike aureba Dan kuwa wannan wata rayuwace da Kika shigo ba Babu fita sai mutuwa hakama akwai qalubalai agabanki Dan haka ki nutsu kiyi abinda yakamata kiyiwa kanki yaqi kema Dan tabbatarda zamanki acikin aurenki sbd auren MALEEK babban rabone agareki ki,
Kibude idanuwanki ki daina yadda da kowa da komai sai abinda zuciyarki ta nutsu dashi NURU.
Sai alokacin ta dago ta kalli jekadin jikinta duk yakuma yin sanyi ta bude baki ahankali tace”
Nagode jekadi.
Gyada Mata Kai jekadi tayi tana miqewa tace”
Ranki ya dade Zaki iya tafiya.
Miqewa tayi ta nufi kofa tana Jin gabaki daya gajiya takeji sbd sanyin da jikinta ketayi ayau din daga wannan sai wannan.
Dakin farhat ta wuce kawai sbd acan zata samu nutsuwa yanzu kawai
Tana shiga ta nufi toilet tayo alwala ta fito daidai shigowan farhat Nan suka shirya sukai sallah tare daganan tacewa farhat baccin awa biyu zasuyi kafin la’asar
Nan suka kwanta.
##MAMUH##
KUYI MANAGE.
Share this
[ad_2]