UBAYD MALEEK Page 71 to 80

Shiru tayi tana nazarin zancensa sbd Bai wani shigetaba zancen Dan kuwa duk me lafiya ya kalli al’amarin dakyau zai fahimci cewan Babu wani dalilin sauyawar maleek zallar halinsane rashin daukan reni ko kadan sai aure daya qara take hasaso wani abun daban Amma tunda yafadi hakan zata bincika tagani Dan a shirye take da maganin dukkanin abinda zai shata Mata layi da zamowa Matar maleek.
Batareda ya kalleta ba yasake Dora Mata tunanin bibiyar daddaqin abinda maleek ke tunani ta hanyar bibiyar jekadi sbd itace mafi amintar maleek a duk gizah da rayuwarsu bayan kaleeb da Mr Omar ko mahaifiyarsa Anneti batasan sirrinsaba sai wainnan mutanen uku.
Da wannan tunanin sosai lailah tasakawa jekadi ayar tambaya Dama tajima da sanin jekadi maqiyiyarta ce ba kauna atsakaninsu munafukartace kodan yanda tasamu cikakken bayanin jekadi itace tsaye akan komai na NURU a rayuwar maleek Dan Haka ta kanta zata fara saita rusa yardar dake tsakaninsu da maleek bayan tasan menene matsalar tukuna.
Bayan tabaro can sassan Anneti ta nufa akaiwa Anneti shelar isowarta tashigo cikin shigar alfarmarta kamar koyaushe ta zauna ta gaida Annetin Kamar dai yanda suka Saba cikin yanayi na Ni Matar neges nikuma Matar MALEEK Babu wata qarin Hira akai sbd Lailah har cikin ranta duk tsanarsu da qiyayyarsu takeji sbd sune munafukanta dasuka tsayawa NURU akan auren MALEEK Dan Haka Bata wani tsayaba ta wuce tabar Anneti da bin bayanta da kallon mamakinda baigama sakintaba saidai bazatani takan zancen lailah ba zata jira maleek yazo tana buqatan bayanin dawowan lailan.
##MAMUH#
[ad_2]