UBAYD MALEEK 1-END

UBAYD MALEEK Page 71 to 80

##MAMUH#

*_Mamuhgee 38_*

_*YERWA INCENSE & MORE*_

_(The scents with diff essence for YOU& your HOME)_

_(MASARAUTAR KAMSHI)_

_Ina masu neman kayayyakin kamshi yan nahiyar ketaran chadi da Senegal? Kai harma da ingataccen had’i yan bornu? To ku matso domin nesa tazo kusa…_

_YERWA INCENSE & MORE: Sun zo muku da kayayyakin turaruka kamar haka:_

_Khumra kowacce Iri._

_Turarukan Wuta_

_Mopping khumrah_

_Washing khumrah_

_Bathing khumrah_

_body mist_

_kullaccam_

_scented hair cream/spray_

_wardrobe balls_

_carpet spray_

_air-fresheners_

_scented pebbles_

_body sprays_

_oil perfumes_

_Perfumes_

_kabbasa_

_burners_

_coal igniter_

_tong_

_kasko_

_english coal_

_dilke&halwa set_

_scented body mist_

_kai dama sauran kayayyakin da bamu ambata, YERWA INCENSE AND MORE, Na tura kayayyakin su koina a fadin Nigeria da ketare. Domin tuntubar su. Suna instagram: _@yerwaincense_and_more. Ko Facebook site:YERWA _COLLECTIONs. Ko a duba su ta number su: ___08095215215/09044191709! _

_suna bada kayan su kan sari ko sayi dai-‘dai_

******************

Bayan fitarsa Haka ta tsaya a inda take tana bin inda ya fice da kallo zuciyarta na rarraba tunanin shin so ne takamu dashi me qarfi kokuwa Jin dadine kawai na kusantuwa dashi?.

Waiwayowa tayi ahankali ta kalli farhat dake gefenta tana kallonta kamar Bata santaba sbd ganin bayan sabon gida da aka sauya musu hadda aunt NURU da daddy dinta kaman suma sababbine aka kawo musu.

Murmushi me qayatarwa NURU tasaki tana juyawa takoma cikin palon ta zauna tareda kunna tv da remote tana Nemo tashar waqoqin yarensu ta Amstar farhat tazo ta zauna jikinta tana cewa”

Aunt NURU Zaki fassara Mana waqan da akeyi ko?

Da mamaki ta kalli farhat din tana murmushi tace”

Sweetie bazan iya fassa Miki dalla dalla ba kawai dai suna waqan soyayyarsu ne.

Da Haka ta rufe zancen farhat din sbd bazata iya bi tana fassara Mata suba kalaman sunyiwa kunnuwanta nauyi bama zata ganeba ko fassarawar tayi Mata sbd kalaman so din ko ita datake sabon Shiga sun Mata nauyi.

Saida lokacin sallah yayi ta miqe ta nufi ciki da farhat a dakinta sukai sallar bayan tayi wankan tsarki

Suna gamawa suka fito babban Palo gaba daya cin abinci daga ita sai farhat din akan dining Haka sukaci suka tashi tunanin afia yadawo Mata

Tanajin kewarta sbd akwai shaquwa da kauna a tsakaninsu ta haqiqa Dan haka takejin kewarta tun ranarda suka baro can saidai tana Mata uzuri sbd Babu Wanda zai zabi wani yabar uwarsa koman lalacewarta Dan hakan yasa Bata ganin Jin illar afia ko kadan kawai dai laifinta daya shine 

Barin mahaifinta ta zabi mahaifiyarta daba itakeda gaskia ba ko acikin matsalar ta iyayen nata cire tunanin zancen tayi daga kanta sbd wannan ba huruminta bane dazata shiga tsakanin ‘ya da iyayentane.

Ranar dasu mum Sarah suka baro gidan bayan kowa ya fidda kayansa anzo andaukesu akabarsu su kadai har lokacin a palon suke afia na kukan rasa cikin mum da dad din wazatabi 

Lailah dakejin wata masifaffiyar hauka na bijiro Mata Jin take kamar ta Dora hannu akai tayita rusa ihu tana tsinewa maleek sbd tunda Allah ya halicceta ba’a taba muzanta taba da wulaqanta taba harma agaban bainar masu aikinta dake tsoronta da Bata girma Kamar zasu bauta Mata sai yau maleek yayi Mata wannan mummunan tabon,

Cikin tsananin ihu da masifa tareda tashin hankali ta miqe tana cewa”

Allah ya Isa tsakanina dakai MALEEK Kuma wlh bazan yardaba wannan wulaqancin dakamun kanka kayiwa Dan saina tabbatarda ka fuskanci tozarci fin wannan Kuma wlh zama matarka ko zan rasa Raina saina dawo matarka alokacin karuwarka zatasan matsayinta da nawa bazai taba zuwa dayaba Dan kuwa wlh ko zata samu damar zama cikakkiyar matarka to saidai idan Ni Lailah bana raye…….

Da sauri afia ta rufe bakinta cikin tsananin baqin cikinta da wannan karon yakai maqura baya boyuwa hawayenta na tsiyaya tace”

Mum mekike fadarwa kanki Haka?

For God’s sake meye amfanin hakan?

Tun farko nayi gudun hakan mum ba kalar rokon daban mikiba karki tafi sbd duk duniya Babu abinda zakije kisamu dayafi Miki ‘yayanki da mijinki Wanda mum ga dukkanin abinda nasani nake Kuma gani dad bazai taba dawo dakeba kema kinsani sbd kinsan wayeshi,

Kin Mata umarnin da kaleeb yabaki mum duk Kika shure Kika tafi?

Mum na rokeki ki hakura ki aje komai tunda yabar Miki Nan din kiyi zamanki tareda Gina sabuwar rayuwa ki maida hankali kan aikinki I promise to be with you aduk halinda Zaki shiga matuqar Zaki janye wainnan kalaman naki ki hkr da abinda zai ringa jawo Miki wulaqanci dacin fuska,

Mum menene amfanin wainnan maganganun na cewa saidai idan bakya raye 

Mum ba’a yiwa Allah ganganci wainnan maganganun har daureki zasu iyayi Dan Allah mum Ina rokonki kadakiyi abinda zai cutatar da dad ko NURU sbd ita ba laifinta bane 

Idan akwai me lefi nawane nice na hada auren…

Wani mahaukacin kallo lailah tajuyo tana yiwa afia da idanuwanta dasuka fiffito sukai jajir kamar me bori tace,

Kikace mene afia?????

Kallon mum din tayi tana dakewa tace”

Nice na hada auren batareda raayin ko dayansub……

Wani gigitaccen Marine akaro na biyu ya sauka a fuskarta Saida tayi baya ta zube kan kujera a dimauce ta dago lailah tace”

Wannan na tabbatar min da kikai bare tafi Miki uwarki 

Dan kuwa kece silar duk komai daya faru ayau tsakanina da dad dinki.

Juyawa tayi a masife tayi ciki ko gabanta Bata gani sosai ta nufi dakinta tana shiga ta rufo wani irin kuka dataketa dannewa tsabar baqin ciki ya subuce Mata ta zube kasa tana sakinsa tareda rufe bakinta da hannuwanta kada afia ta jiyota abin ya Mata yawa.

Afian ma kasa bin mum din Tata tayi ta zauna agurin tana kuka ahankali ahankali.

Da daddare daqyar kowannensu ya iya kwantawa Babu ci bare Sha hakama kwanciyar kawai sukayi Babu Wanda ya samun bacci ya daukesa sbd fargaba da tashin hankalin rashin ko masu gadi Babu ko motsin komai aduk girman gidan sai rashin tsaro da motsin yasa sukaji basa cikin kwanciyar hankali musamman afia data rasa tunanin me mum dinta keyi tareda tunanin meye niyarta.

Washe gari Lailah tarigada ta yanke shawaran zuwa gizah Dan takasa hkr a Daren takira NEGES datasan shikadaine yanxu zai iya saka Baki a maganar sbd kaleeb ko Ana Mata dukan mutuwa bazata fara tunkararsaba bare Anneti datasan duk duniya bazatabi bayan kowaba indai akan ‘dantane MALEEK,

Tariga ta yanke zuwa gizah sbd dawo fry da matartabarta na matsayin Matar maleek bazata taba yardaba ‘yar bayi jikar bayi tasha gabanta harta karbi matsayinta.

Koda afia tashigo dakin da safe lailan na zaune tana duba agogon hannunta Dana wayarta akai akai sbd tayi booking din ticket na tafiya jira take lokaci yayi ta nufi airport 

Drivern dadyn Imran takira aturo Mata shi take jira yakaita airport din 

Shigowar afia yasata dagowa ta kalleta da idanuwanta dasukai jajir sbd rashin rintsawa da tashin hankali tareda masifar datake ciki ta dauke Kai daga afian tana Dan yamutsa fuska tace”

Afia idan kinzo Nan danki dameni da koke kokenkin Nan kokuma wani shirmen daban kadaki fara sbd inada ciwon kan danake fama dashi already bana buqatan wani sabo Dan bama zan dauka ba kece naki ran zaiyi mummunan baci so just get out of here”taqarasa fada tana nuna Mata kofa da ido.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button