UBAYD MALEEK 1-END

UBAYD MALEEK Page 71 to 80

Tray din da afia ta jero Mata tea da soyayyan kwai takawo Mata ta kalla tana tsiyayar hawaye takasa cewa komai ta juya ta fice hawayenta na sake gudu tana zuwa kitchen ta ajiye tray din ta juyo ta fito kenan mum din tafito janye da akwati da handbag dinta sai wayarta a hannu 

Da mamaki afia ta qaraso tana share hawayenta dasuka kasa tsayuwa ta bude Baki muryanta na rawa tace”

Mum Ina….

Bata qarasaba lailan ta katseta da cewa”

Gizah zantafi idan Zaki iya zama anan ne to saina dawo idan bazaki iya ba ki nema gidan dad dinki ki koma can dama kece Kika hada auren saikije ki qarasa cike ladarki ta qara musu dankon zama.

Juyawa tayi ta fice tabar afia sandare a tsaye cikin ‘dibbin mamaki da tsoron mum din Tata da sauyawarta.

Da gudu taqarasa ta riqe mum din tana cewa”

Mum Dan Allah na rokeki kada kije ki wulaqanta kanki acan 

Tozarci da sake tonarda asirinki kawai Zakiyi Anneti bazata karbekiba Dan Allah kada kije mum,

Mum na rokeki Dan Allah…

Cikin quluwa lailah ta cire jikinta daga nata tana cewa”

Baki fahimci abin Dana fada Miki kenan ba nace ki nemi dad dinki ki tafi gurinsa bazan iya wannan hayaniyarba afia please just go kina batan lokaci Ina buqatan Isa airport kan lokaci.

Rabewa tayi ta wuce ta miqawa driver akwatinta ya karba yasaka mota tareda bude Mata tashiga ta rufe ya zagaya ya shiga ya tada motar suka fice.

Ajiyar zuciya afia ta sauke ahankali tanabin inda suka wuce da ido tana rasa tunanin Yi akan mahaifiyarta sbd yau da mahaifiyarta tasake tsallakewa ta barta akaro na biyu ya rusa duk wani sauran hope datake dashi akan uwarta sbd duk uwar data tsallake babbar budurwa kamarta a qaton gida irin wannan Babu kowa ta tafi ta barta batareda tunani ko fargaban wani abun yafaruba tabbas babu ‘yayanta cikin ranta,

Dad dinta tasani ta tabbatarda Koda Wasa bazai iya kwatanta wannan gangancin akantaba shida yake uba Amma uwarta mace takasa yadda ta runguma takuma yadda data zama uwa me nauyin ‘yayanta akanta.

Sake sauke numfashi tayi tareda juyawa ahankali ta koma ciki tana daga qafafuwanta dasukai Mata nauyi daqyar.

Dakinta direct ta nufa ta zauna bakin gadon tareda dagowa ta kalli dakin tafashe da kuka ahankali tana sunkuyar da kanta sbd yau ta wayi gari batada kowa atareda ita bawai Dan tarasa kowa din ba.

Ta share awanni a hakan tana kuka cikin hali na ciwon dakecin zuciyarta kafin ta share hawayen ahankali ta miqe tsaye ta janyo akwatinanta tafara kwashe kayanta tana zubawa ciki harsaidata Gama kwashewa tadawo ta zauna tana tunanin Kiran mahaifinta datasan ransa abace yake da ita.

Kasa kiransa tayi Takoma ta kwanta kan gado tana tunanin meya hargitsa rayuwarta cikin kwana daya da awanni akai.

Kasa kiransa tayi Takoma ta kwanta har batareda tasan matsayar inda ta dosa ba sbd wata zuciyarta na Bata shawaran in mum dinta gizah sbd dakatar da ita ga wani abin dabai kamataba Wanda zai iya janyo zubewar mutuncin dad dinsu da ita kanta mum din saidai Kuma Tana Jin gwara ta qyale mum din tayi nisa zuciyarta batajin kira.

Wayarta ta dauka ta duba Babu available tickets na zuwa gizah Dan Haka ta yanke shawaran jira kwana biyu tagani.

Bayan kwana biyu haka tasake dubawa ba tickets sai jikinta yayi sanyi ta sawa ranta ba alkhairi cikin zuwan nata Dan Haka tasake daurewa ta zauna har gari yasake wayewa ta yanke shawara takira dad dinta saidai Bata samesaba sai kawai ta Nemo wayar NURU takirata Kai tsaye.

Da safe ne suna cikin bacci itada farhat a dakinta washe garin ranarda MALEEK ya wuce kenan,

Basu tashiba sbd guraren karfe takwas ne taji ringing din wayarta ta lalubo ta dauka batareda ta tantance sunan me kiranba saidataji muryar afia ta wartsake tana bude ido tareda dubawa taga sunan afia din ne cikin kulawa tace”

Afia kina lafiya kuwa?

Ajiyar zuciya afia ta sauke dagacan bangaren tareda bude Baki tace”

Kituromin Edward yazo yadaukeni anan tsohon gidan Ina jira.

Ahankali NURU tace”

Ok Bari nakirasa nafada Masa zaizo yanzu Inshallah.

Da haka suka kashe wayoyin kowacce cikin Jin nauyin ‘yar uwarta.

Batareda ta sauko gadonba daganan kwance ta Nemo numbern Edward ta saka kiransa Yana dagawa ta sanar dashi yaje ya dauko afia yace ok.

Komawa baccinta tayi sbd Bai ishetaba kafin afian ta iso.

Cikin bacci tasakejin ringing na wayarta ta lalubo ta daga cikin bacci tace”

Mum Sarah lafiya kuwa?

Sorry na tasheki dama afia ce tazo nace zan sanar dake za’a Kai Mata kayanta asalin dakinta da aka ware Mata.

Guntuwar hamma tasake tana tashi zaune tace”

Mum Sarah shine sai angayamin Kuma?

Eh nafada Miki ne sbd umarnin maleek ne.

Lumshe idanuwa tayi sbd sunansa da aka ambata yashigeta tace”

Ok shikenan akaita dakinta ganinan ma fitowa.

Duk abinda ake fada afia din na tsaye tana saurare tareda kallon ikon Allah daya sake kasheta da mamakin saidai batace komaiba ta nufi dakinta tashige tana kallon koina na gidan daya fi wancan gidan nesa ba kusaba.

##MAMUH#

*_Mamuhgee 39_*

_RANO NET! RANO NET! RANO NET!_

_WHO NO LIKE BETA AWUUF THINGS?_

_IDAN KAJI GANGAMI DA LABARI….! INA MASU ZUBIN ADASHEN DA BA RANAR DAUKA NA DATA?_

_TO KU MARMATSO KUJI, KU KUMA SHARE HAWAYEN KU, MUNZO MUKU DA SABBIN TSARE TSARE NA DATA, WADDA KOWA ZAI IYA SAYA DAI DAI KARFIN SA. A FARASHI MAI RAHUSA_

_RANO NET! RANO NET! RANO NET!__

     _(Afford data at chikini price)_

         _MALLAKI DATA A KUDI KALILAN DA RANO NET_

_TSAYA KUJI, A RANO NET ZAKA IYA ZAMA RESELLER KO WHOLESALER KAI MA, EH ZAKA/KI IYA ZAMA MA SAYAR DA DATA A FARASHIN SARI MUKE BAYARWA, KAI/KI KAFA KASUWANCIN KU KUMA. DA KUDI KALILAN._

_MUNA KUMA SAYARWA AKAN ‘DAI DAYA, KOWANE NETWORK MUNA SAYARDA DATA PLAN DINSA AKAN KUDI KALILAN, MASU FARASHIN SARA KUWA MA KU KUDIN BAI KAI HAKA BAMA_

_AIRTEL_

_9MOBILE/ETISALAT_

_MTN_

_GLO_

_DUK MUNA SAYARDA TSARIN DATA DINSU. KAMAR MISALI MTN MUNA SAYARDA 1GB.24MB AKAN FARASHIN NERA 300 KUMA YANA KAIWA WATA DAYA, GWARGWADON YADDA KAKE AMFANI DA DATA, 2GB 600, 3GB 900!!_

_DUKA WADANNAN TSARIN DATA DAMA NA SAURAN LAYIKA MUNA SAYRWA AKAN FARASHI MAI RAHUSA, WANDA KOWA ZAI IYA YIN TSARIN DAI DAI ALJIHUN SA_

_Ranonet.com.ng_ 

_GA SITE DINMU NAN DAKE YANAR GIZO, KAI TSAYE ZAKI/KA IYA SIYAN NAKA TA NAN. _

_KO A TUNTUBE MU TA NAMBAR TARHON MU: +234 803 081 1300/+234 808 540 5215_

_KYAU, INGANCI, RAHUSA, ADADE ANA YAWO A YANAR GIZO SAI RANO NET._

_RANO NET..!!!!_

****************

Direct dakin afia din NURU ta nufa data fito farhat ma ta tashi tana biyeda ita suna shiga dakin ta waiwayo tana kallonsu farhat ta qarasa gurinta da gudu cikin tsananin farin ciki me yawa tana cewa”

Yeeee afia.

Rungumeta afia tayi cikin farin cikin ganinta da kewarta datayi kwanakin tace”

My baby I love you I love you.

I love you too afia Kuma nayi kewanki sosai musamman kafin Aunt NURU da daddy sudawo nikadai dasu mum Sarah munata Jin dadinmu.

Rungumeta tasakeyi tana kallon NURU dake kallonsu cikin murmushi ta qaraso tana kallon afia din tace”

Sannu da zuwa.

Murmushin afia tayi tareda sakin farhat taqaraso gaban NURUn suka Dan rungume juna NURU ta bude Baki ahankali tace”

Am sorry afia ban….

It’s ok yawuce Dan nice yakamata na Baki hakuri akan abinda mum Dina ta…

No afia yawuce kaman yanda kikece abar maganar.

Zamewa sukayi NURU na gyara tsayuwa tace”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button