UBAYD MALEEK 1-END

UBAYD MALEEK Page 71 to 80

Bari natayaki jejjera kayanki a dakin kafin agama breakfast muci.

Tayata bubbude kayan tayi suka jere suna fira anan NURU ke sanarwa afia din gobe zata fara zuwa Court Inshallah ita dayake tafara zuwa asibitin kafin wannan rigimar ta dakata sai itama tace gobe zataci gaba da zuwa kada tun wuri rashin bada himma yashiga cikin aikin.

Suna gamawa NURU ta fito ta nufi dakinta tayo brush ta sauyo Kaya ta cire na baccin dake jikinta wainda takejin nauyinsu tun dazun agaban afia.

Afia dasuka zauna cin abinci Bata wani samu damar sakewa taci sosaiba sbd tunanukan dasukai yawa akanta musamman na mum dinta da batasan meyake faruwaba a gizah din ga dad dinta har lokacin wayarsa Bata Shiga gashi takasa tambayar NURUn dad saidai ta tambayi farhat tafada Mata yayi tafiya baya Nan.

Sosai NURU ke kokarin janta da fira sbd su samu duk su dukan su sake dan sukoma kaman yanda suke wannan sabon yanayin nasu bayayiwa kowaccensu Dadi 

Da Haka dai gurin firar suka fara sakewa suna danne komai tareda qoqarin mantawa kawai ahaka dai har dare yayi suka kwanta washe gari kowannensu ya tashi kan lokaci sbd Shirin fara fita zuwa gurin ayyukansu 

Sukai breakfast suka fito NURUn na sanye da white long sleeves da White pencil trauser sai black kimono har qasa sai brawn and white scarf dake kanta da takalmi wedges na _Le labo_ sai handbag da Jakarta rigarta 

Afia kuwa cikin jeans da shirt take sai white coat dake jikinta ta likitocin asibiti suka fada mota Edward ya fita dasu aka fara aje afia kafin aka wuce aka Kai NURU.

*************

Ranarda jekadi suka iso gizah tundaga shigowarsu padima ta ‘dan kalli jekadi tana gyara zama cikin motar da aka daukosu daga airport tace

Saqona na NURU datace za’a bani ko za’a banishi tun ayau inason hada kayana guri dayane idan ba damuwa.

Waiwayowa jekadi tayi ta kalleta tareda sakin murmushin manya tace”

Babu matsala saqonki a Daren yau Zaki fara karban abinki basai kin damu kanki da tambayawarbama za’a Baki komai dukkanin abinda Kika cancanta.

Murmushi padima tayi tana dauke Kai tareda cewa”

Yawwa dai Ngd Sosai.

Suna Isa har kofar dazata sadasu da sassan Matar maleek ma’ana sassan NURU anan akai parking suka fito Kai tsaye suka shige hanyar suka wuce sassan NURU sukabi wata hanya sukai tafiya me tsayi datasaka padima fara waiwaye tana son yin mgna Amma tana dannewa sbd tasamu tafara riqe abinda za’a Bata din tukuna.

Sassan maleek suka nufa suka kusa can baya sosai inda wani boyayyan gurin sirrinsa yake jekadi ta waiwayo tareda kallon padima tana bude kofar tace”

Bismillah shigo daga ciki.

Ba wani tsoro padima ta qaraso tana leqawa ta shige sbd ganin kamar dakin ajiyar dukiyane ta qarasa ciki tana dube dube tanajin matsuwar abata abinda za’a Bata ta bar gurin sbd kaman tsoro da fargaban gurin na neman shigarta.

Mintuna biyar ba’ayi ba da shigarta saiga jekadi dauke da ruwa da drinks masu sanyi a tray ta qaraso tana ajiyewa kan table dake dakin tana cewa”

Bismillah.

Dagowa padima tayi ta kalli tray din kafin ta kalli jekadi tace”

Anan ne saqon yake?

Wannan karon jekadi Bata kalletaba tace”

Eh saqon ne za’a Baki idan kinyi hkr Yana isowane.

Shiru padima tayi cikin qaguwa da gagfawarta ta saqon yashigo hannunta tasaki guntun tsaki cikin ranta tareda Kai hannu ta dauki lemun takai bakinta tafara kurba ahankali tana kallon kofa tana Jin matsuwarta na qaruwa harta shanye lemun ta dauki ruwama Tasha kadan ta ajiye tareda Miqewa dagakan kujera daya tal dake dakin sai table da kayan adon daki masu kamar zaiba ta juyo tana kokarin komawa ta zauna taji wani irin gumi da zafi zafi me tsanani Yana tasowa daga cikin jikinta ta hadiye wani wahalallen yawu sbd bakinta dake gauraya da wani irin mummunan daci ta juyo da sauri tana share gumin fuskarta tana kallon jekadi da alamar tashin hankali da azaba tace”

Me Kika bani???

Me kikeson yimin???

Innalillahi wayyo Allah 

Mutuwa zanyi azaba nakeji me tsanani….

Wurgi tayi da dankwalin kanta tana fige rigar jikinta cikin wata mummunar azabar dabata taba Jin makamanciyartaba arayuwarta ta zube qasa tana yagar jikinta tako Ina tana cewa”

Dan Allah ki taimakeni

Jikina cikinsa wuta ake hurawa

Dan Allah kibani ruwa 

Zan mutu……

Shure Shure tafara jikinta na rikidewa jajir duk inda ta Sosa Kota fizga saiyayi wani irin kumburi kaman wuta ta koneta a gurin take ta haukace tana Shure shuren azaba tana ihun mummunan yanayi Jin takeyi kamar ruwan dalma na sirkuwa cikin jininta da bargonta..

Ihunta yasa jekadi juyawa ta fice daga dakin tareda rufewa ta waje ta cire qaton mukullin ta bar gurin Takoma can kofa daganan ta dauki hanyar zuwa gurin Anneti da akaiwa isarwada sakon zuwan jekadi.

Da murmushi Anneti ta kalli jekadi tace”

Barkan jekadi da dawowa lafiya,

Muna fatan anbaro Mana su maleek da mushransa tareda ‘yayansa lafiya?

Da murmushi akan fuskan jekadi cikeda biyayya tace”

Alhmdlh muka barosu Inshallah.

Masha Allah to Yaya bakuwar mushrah?

Da ita kuka dawo dai Ina fata?

Sauke Kai jekadi tayi tace”

Da ita muka dawo saidai tariga ta wuce delah inshallah Bata biyo ta Nanba.

Masha Allah shikenan kije kihuta kin debo gajiyar Kai baquwa da dawowa da ita Dan Haka kije ki huta na tsawon kwanaki shida bakya buqatan fitowa kawo gaisuwa nabaki daman hutawa tukuicin Kai baquwar NURU da dawo da ita.

Cikin tsananin farin ciki jekadi tace”

Allah yaqarawa Anneti tsawon Rai da lafiya tareda girma, jekadi godia take sosai da matuka.

Murmushi kawai Anneti tayi tareda gyada kai tana cewa”

Amin.

Tashi jekadi tayi ta fice tana sake miqa godiya.

Tana fita hamdala ta sauke sbd hutunta zaibata ikon rike aikin gabanta da kyau su samu su gano asalin maqiyin maleek da nahaifinsa daya rasu Wanda suka shafe shekaru suna bibiya.

Sassanta NURU ta nufa inda takeda babban Palo da daki tareda makeken toilet dinta ware musamman acikin sassan na NURU tareda makeken dakin bayin sassan dake gefen nata.

Wanka tayi ta huta taci abinci sai alokacin tasamu ta rintsa dataga tafara aikata aikin kaleeb da maleek wainda zata iya bada ranta akansu.

Washe gari da sassafe ta saci jiki Babu me gani ta nufa gurin padima daukeda abinci cikin kwando tana Isa ta saka mukulli ta bude kofar ahankali tareda shigowa ta maida ta rufe ta ajiye kwandon hannunta tana kallon padima da kamanninta suka Gama sauyawa zuwa wani irin yanayi na tsoro da firgici tana fidda wani irin azababben Nishi dake fitar Mata daqyar.

Gyaran murya jekadi tayi tana kallonta batareda taji tausayinta ko dayaba aranta.

Daqyar cikin tsananin azaba padima ta dago idanuwanta dasuka kumbura suntum dama fuskarta Baki daya 

Dukkaninta tayi jajir koina jininta.

Da hannu jekadi ta nuna Mata abincin data shigo dashi tana cewa”

Ga abinci Nan kici zai taimaka Miki kadan gurin samun karfin iya daukan dose din anjima.

Wasu siraran hawayen azabane suka silalo Mata ta gefen ido ta bude bakinta daya kunbura batako iya motsashi daqyar can qasa ta iya furta”

Meyasa? Meyasa akemin Haka????

Numfashi jekadi ta sauke ahankali tareda kallon padiman tace”

Da zakiyiwa kanki adalci tun Baki lalace da yawaba da kin Fadi inda Kika samo wannan garin da kanki Amma nasan burinki da gurbataccen tunaninki bazai Bari ki zabi hanyaba.,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button