UBAYD MALEEK Page 71 to 80

Washe garin ranar lailah ta sauka a gizah Wanda yasa kowa cikin mamaki sbd sanin Bata taba zuwaba sai tareda maleek shima Saida babban dalili bare yanxu dasukejin kishi kishin rabuwarta da maleek sai zuwan nata yasaka kowa cikin mamaki musamman Anneti saidai Bata nuna Mata komaiba.
Matsalar farko data fara fuskanta shine sassanta shine akaiwa sabon gyara da tsari yazama na NURU saidai tun kafin zancen ya habbaka yazama wani al’amarin daban Anneti tasaka aka gyara Mata wani sassan daban Wanda beyi girman na NURUn ba ko kadan aka Aiko Mata da bayi biyu masu Mata hidima Wanda hakan yayi mummunan baqanta Mata wato har anan dinma saita fuskanci wulaqanci irin wannan?
Hmm zatayi lokacin kowa daga baya har Annetin sbd bazata dauka wulaqanci irin wannan ba.
Wanka tayi sai alokacin tasamu damar Dan cin wani abinci Takoma daki ta kwanta Dan hutu take tsananin buqatar yi ayanxun ko kyawun fuskarta ya dawo daidai na rashin hutu da bacci da nutsuwar dabata samuba tun shekaran jiyan sbd fitinar dake gabanta Dan haka zata huta sosai kafin tafara fitowa aganta asan haryanxu tana Nan a LAILAH MALEEK dinta kyakkyawar mace me lokaci.
Ta bangaren jekadi kuwa ganin yadda jikin padima yarikice yasata kebe kanta cikin dakinta ta nemi numbern Mr Omar tayi Masa bayanin dukkanin komai ta Dora cewa lailah na gizah ta iso.
Shiru Mr Omar yayi tareda sauke Dan numfashi sbd baiso katse hutu da Jin dadin maleek ba Dan kuwa hutun gaske maleek din keyi a kwanakin Dan ko ayyukansu tuni suka taru suna Nan Yana Dan kokari Yana rage masu rayuwar sbd maleek din yasamu hutawa dakyau Amma Kuma wannan zancen Dole ya sanar Masa dashi.
Sake sauke numfashi yayi yace”
Zan sanar Masa duk abinda yace zakiji Amma dai kafin Nan inaga ki Dan Bata maganin meriz din kadan tasamu karfin Koda kyakkyawan numfashi ne sbd na tabbatarda maleek bazaiso ta rasa ranta ba dama amfanin riqeta din asan asalin su waye suke aikin Amma dai zan sanar Masa yanxu Inshallah.
Kashe wayar yayi tareda sake fitarda numfashi me zafi Yana tunanin Dole ya isarwada maleek wannan sakon batareda Bata lokaciba duk da ba Haka yasoba
Yaso ubangidansa yasake samun hutu wadatacce Dan kuwa tsawon shekaru Basu samu irin wannan hutawarba sbd kullum cikin aiki da bincike suke matuqar ba ciwoba maleek baya sati biyu a jere zaune baiyi tafiya sai kwanakin Nan dayaga alamar kila har fiyeda watama zasuyi suna hutawa yanxu ga wani aikin.
Ajiyar zuciya ya sauke akaro na biyu kafin ya daga wayarsa ya Nemo numbern MALEEK ya saka Kira Yana nutsuwa tareda daidaita murya
Saidata kusa yankewa kafin maleek din ya daga cikin kamewa yace”
Yes Mr Omar.
Barka da hutawa MALEEK,
Dama saqone daga gizah, jekadi takira jikin yarinyar Nan yakasa daukan meriz tana cikin mawuyacin halinda kowane lokaci zata iya rasa ranta shine jekadi ke neman qarin umarnin taci gaba da aikinta kokuwa ta dakata daga Bata din?
Shiru yayi na wasu seconds daidai fitowar NURU daga wanka fatar jikinta na daukan ido ya zubawa fuskarta fararen idanuwansa batareda ta ankareba yaji tunaninsa na sauyawa akan padiman ya sauke boyayyan numfashi ahankali tareda Miqewa tsaye ya fice daga dakin ya nufi Palo Kai tsaye yace”
Kada ta Bari wani Abu yasameta ta Bata magani sosai
Zamu sauya tsarin bincikenmu batareda yarinyar ba ta jinyaceta ta warke a maidata gida gurin iyayenta
Kada abari iyayen su San abin daya faru da ita sbd kada su ‘dagawa ‘dayar ‘yarsu hankalin.
Angama maleek.
Sai maganar Mahaifiyarsu li’iliti tana gizah ta Isa Kuma ga dukkanin bayaninda jekadi tayi Kamar da umarnin neges ta Isa can sbd bada umarninkaba,badana Anneti ba badana kaleeb ba to tabbas idan badakuba shikadaine yakeda ikon Bata damar zuwa tunda ba sauran ummnnn wannan a tsakakaninku.”ya qarasa fada Yana Dan rawar murya fada sbd girmama auren MALEEK din duk da ya rabu.
Shiru maleek yayi Jin abinda mr Omar yace
Ya Dan sake gyara tsayuwa Yana tunanin Dole akwai dalilin neges na bawa Lailah damar zuwa gizah ta zauna itakuma gata idanuwanta sun rufe gabaki daya batada tunanin komai yanxu saita yanda zata farfado da kanta ta jikinsa take ya yanke shawaran zuwa gizah ya bude Baki cikin nutsuwar murya yace”
Kayi Mana Shirin komai gizah din zamuje wannan karon Ina buqatan tunatarda wasu waye maleek Incase idan sun samu mantuwa.
Yes maleek”Mr Omar yafada Yana kashe wayar maleek din take yakira ya sanarda tafiyar maleek aka garzaya karban tickets da komai.
Yaso barinta anan gidan yaje yadawo tukuna Amma Kuma bazai iyaba sbd duk tsoron dazai Bata hankalinsa zaifi kwanciya idan tana cikin mutane shiyasa ya maidata can gida zibrian gaba daya kafin suka wuce.
A gizah kuwa sosai yakoob yagano akwai abinda jekadi ke boyewa musamman Dama sunsan Dole itakadaice tasan inda padima take sbd itace wadda tashigo gizah din da ita Dan Haka ya kasa ya tsare cikin taku sosai harya gano inda take zuwa acan bayan sassan maleek duk da Bai Isa cikin sassanba ya isa kofar yasan akwai babban abinda maleek yasakata take boye gurin dangane da padima Dan Haka yakoma yafadawa neges komai
Cikin wani irin yanayi neges ya murmusa Yana jinjina Kai yace”
Ayi aike gurin tsohuwar matar maleek lailah cewa nabata damar zuwa muyi mgn.
Allah yaqara ma girma da lafiya.”yakoob din yafada Yana yin baya baya ya juya ya fice.
Ta bangaren lailah kuwa yau ta samu damar Isa gurin hutawar neges Dan maganar aurenta da maleek data kawota har cikin palon akai Mata iso ta qaraso gabansa ta gaidashi cikin girmamawa kafin ta zauna cikin tata isar ta zamtowarta Matar asalin me mulkin
Take aka fara shigo da kayan marmari dasu Zuma da kayayyakin tabawa aka cike gurin tsab ta dago ta kalli kayan tareda dauke Kai sbd hakan tamkar cin fuskane ga maleek ace macen dake matsayin matarsa tana zaune gaban wani Wanda ba maleek ba har akawo Mata abinsha Dana ci Ana nufin taci gabansa wannan rashin darajar yayi yawa tana matsayin Matar maleek guda.
Numfashi ta sauke tareda waiwayowa ta kallesa Kai tsaye cikin tausasa harshe tace”
Allah ya taimaki neges me gizah ta yanxu ina maka barka da hutawa tareda barka da ganin wannan lokacin.
Kallonta yayi daka zaman hakimcen dayake ya Dan saki fuska wani murmushin dattijantaka na sauka kan fuskarsa yace”
Neges ya amsa Kuma Yana biki barka da fitowa medakin maleek na gizah.
Lailah tunda tashigo cikin zuriarsu take tsaye a wuyansa sbd mace ce me tsananin son mulki da Isa tareda kwadayin komai yazama Yana qarqashinta da ikonta Dan kuwa Jin take kamarma itace maleek din sbd sosai ikonta da gadararta ke bayyanarda mijintane me kujerar sosai take shigar Masa hanci Yana dannewa sbd taku da zamanta sirikarsa amma zai Bata darasi daidai da ajinta sbd ita takawo kanta gurinsa yanzu neman mafitar matsalarta da maleek.
Cikin nutsuwa da kulawa ya Dan juyo da Kai a kame yace”
Abu dayane akan matsalar aurenku da maleek shine karkata da hankalinsa yayi ta wani bangaren
Ma’ana wani Abu daya rinjayi tunaninsa akan iyalinsa.
Dagowa tayi cikin mamaki tace”
Akwai abinda ya rinjayesa kuwa bayan wannan auren da yayine…
Wani murmushin yakuma saki Yana cewa”
Mace bazata juyarda maleek ba ko wacece kuwa nafi sakaran wani Abu daban Wanda Banda sani akai Amma Dole saikin Saka ido kin bincika kin gano kafin asan inda gyaran zai faro.