UBAYD MALEEK Page 81 to 90

Faduwar da jekadi tayi ganin lailan ta nufi cikin da gudu yasata miqewa da sauri tana Kiran sunanta saidai kafin tayi wani yunkuri wani mummunan duka ya sauka akanta me tsananin azaba take ta sulale agurin ta zube a some jini na fita ta goshinta batareda taga Wanda yayi Mata dukan ba.
Lailah kuwa ganin mace a kwance cikin dakin cikin wani yanayi na Kamar majinyaci yasata takowa ahankali zuciyarta na harbawa cikin tsananin mamaki da tsoro ta iso har gabanta zata Kai hannu ta tabata padiman ta bude idanuwa ahankali baccin daya fara daukanta na sakinta ta zubawa lailah idanuwanta ahankali tana kallonta da mamaki Jin motsi abakin kofar shigowan yasa padima kallon bayan lailah mamakin ganinsa nasata kaikata Kai tana kallonsa dakyau ahankali ta bude Baki tace”
AMED????
Da sauri lailah ta juya zata waiwaya wani mugun duka ya sauka a tsakiyar kanta batareda ta waiwayo ba ta yanke jiki ta Fadi agurin sama sama tanajin padiman nasake maimaita amed har idanuwanta suka rufe numfashinta na daukewa.
******
Ruwan sanyin dake sauka kan fuskarta zuwa jikinta masu tsananin sanyi ya sanyata fara numfasawa tana motsa idanuwanta dasukai tsananin nauyi tafara budesu ahankali ahankali tana rufewa tana budewa sbd hasken dayayi Mata yawa harta budesu duka suka sauka kan mutanen dake zagaye da ita tafara Binsu da ido daya bayan daya kafin ta tsayar dasu akan fuskar maleek da yayi Mata kallo daya ya dauke Kai
Ta juyar da kanta gefe taga manyan jami’an tsaro tsatsaye agurin take ta zabura da sauri tana miqewa zaune tana sake kallon mutanen dake gurin ga qarin mamaki da firgicin ganin safiyace tas idanuwanta suka sauka kan mutum kwance miqe sambal anrufesa da farin kyalle har fuska Wanda ke nuni da gawar mutum ce,ta hadiye wani mugun yawu daga bakinta daya bushe kyam Nan take tana miqewa tsaye kanta na sarawa ta dafe kan tana Jin wani tashin hankali na shigarta sbd jekadi tasan tabari agurin jiyan da daddare bayan ta tureta, wani sabon tashin hankali da faduwar gaba me qarfi tashiga kardai wani Abu yasamu jekadi Dan dukan da turewar datai mata???
waiwaye waiwaye tafara tana neman rikicewa jikinta take yafara rawar tashin hankalinda Bata saka Masa ranaba ta nufi maleek da sauri tanajin ma ta wartsake daga ciwon da kanta keyi me tsanani ko gabanta Bata gani saidata Isa gaban maleek zatayi mgna idanuwanta suka sauka gefensa daya da jekadi ke tsaye sunkuye da Kai goshinta duk jini daga gani itama tana cikin tsananin tashin hankali
A haukace lailah ta waiwaya ta kalli gawar dake rufe agurin taji qafafunta na sagewa tayi baya zata Fadi macen dake sanye cikin uniform na hukumar qasar ta tareta tana riqeta dakyau da alamar dama ita ake jira.
Ta fizgo da qarfi tana kallon maleek bakinta na rawa cikin tsananin tashin hankali tace”
Wanene???
Me yake faruwa anan?
Kallo daya yayi Mata ya juya yana sauke siririn numfashi sbd gabaki daya al’amarin ya sauya acikin qanqanin lokacinda basuyi zatoba.
Kallon gawar padima yayi akaro na hudu Yana tunanin yanda ‘yar uwarta zata iya handling wannan mummunan al’amarin Sam an shammacesa a guri mafi mufi Dan kuwa yanzu acikin jekadi da lailah baisan wazai fara wankewaba duk da dukkanin shedu lailah suka nuna ita tayi kisan sbd baro baro jakadi ta fada cewar lailah ce tazo ta bugeta ta Suma itama lailan ta nuna hakan ta Yaya za’a fitarda lailah daga wannan ta bangare daya ta Yaya NURU zataji wannan mummunan labarin?
##MAMUH#
Kasa hakuri lailah tayi cikin sabuwar qaramar haukar dake Shirin kamata agurin take tafara kwacewa tana kallon maleek da sauran mutanen dake gurin cikin tsananin ihun dukkanin jikinta na rawa take cewa”
Meyasa zaku tafi Dani?
Bani nakashetaba wlh,
Dan Allah ki tsaya nayi muku bayanin abinda yafaru wlh tallahi bani bace
Dan girman Allah maleek kace su barni kasan bazan taba iya aikata wannan mummunan abin ba
Ba halina bane,
Dan Allah ki sakeni wallahi bani bace ku tambayi jekadi Dan Allah maleek karka Bari su tafi Dani….
Tana ihun tashin hankali dukkanin jikinta Babu inda baya wani irin mazarin tashin hankali da ficewa hayyaci musamman data tabbatarda tabbas kisa akai Kuma itace ake nufin tayi kisar kenan kasheta za’ayi itama tabar duniya da ‘yayanta
Tunanin hakan ke saka haukatarda kwanyarta tafara fizgewa tana kokarin zuwa gurin maleek dake tsaye batareda ya dago ya kalletaba sbd kunyar hakan da baqin cikin hakan dake cinsa koba komai ita din uwar ‘yayansace matarsa ta farko wadda koman lalacewarta za’a kirata da matarsa ta farko har qarshen rayuwarsu.
Dayake har bakin kofar sassansa qatuwar baqar motar jami’an tsaron take suna Isa aka sanyata aka rufe tana wani irin kuka da neman ceto daga maleek tana rantsuwar ba ita din bace har muryarta tafara dishewa musamman daya zamto kallon karshene takewa koina Dan tasan hukun kisarta bazai dauki delay ba tunda komai a bayyane yake tasake sakin wani mahaukacin kuka tana buga kanta da tint windon motar da qarfi tana kuka tana Kiran sunan maleek cikin dukkanin bada imaninta ga shikadaine zai iya cetonta
Haka aka janyo jekadi itama aka saka cikin motar aka rufe Kafin
Ja motar suka wuce sai alokacin maleek ya dago ya kalli Mr Omar dake tsaye a gefe tsaye kansa sunkuye cikin yanayi na tsananin jimami idanuwansa suka kada sukai jajir ya dago Yana kallo ‘yan motar asibitin dasuka Kira suka matso Dan daukar gawar su wuce da ita saiga shelar sanrwar tahowar NEGES da kansa zuwa sassan Dan tuni abinda yafaru ya karade gizah saidai Babu Wanda yasamu iko ko damar shigowa sassan hakama Babu Wanda yasamu masaniyar shin wanene aka kashen daga jami’an tsaron da Mr Omar yakira sai motar asibitin da jami’an tsaron sukazo dasu Dan daukan gawar sai Anneti data iso sassan cikin tsananin tashin hankali tana zubda hawayen ganin wannan mummunar qaddararriyar ranar ace kisa acikin gizah Kuma daga sassan maleek qari da Dadi tsohuwar matarsa da jekadinsace cikinsu daya ya aikata wannan mummunan Abu me duniya zatayiwa MALEEK kallo?
Gashi Anki bude gawar bare asan wanene aka kashen.
Neges na zuwa cikin tsananin jimami da tashin hankalin wannan mummunan al’amarin ya kalli MALEEK Yana bayyanarda damuwarsa da rashin Jin dadinsa akan al’amarin yace”
Ina me jajanta maka wannan al’amari
Saidai nayi maka alqawarin hukunta duk Wanda aka tabbatarda shine yayi kisan a tsakaninsu biyun Dan kuwa wannan al’amari babbane dazai iya tana darajarmu gabaki daya da ikonmu Dan Haka komai zai tafi abisaga adalci da doka wannan alqawarinane.
Sai alokacin maleek ya dago ya kallesa da idanuwansa dake bayyanarda zallar bacin Rai da wani irin zafi na iko da mulki dake yawo jininsa ahankali ya bude Baki cikin kamewa yace”
Godiya maleek yake Kuma Ina fatar zaka tuna wannan alqawarin naka Dan cikakkene jinin delas basa alwawarinda basa cikawa Ni nayi maka alqawarin tayaka cika wannan alqawarin za’a tafiyar da komai bisaga adalci da doka.
Jinjina Kai neges yayi Yana danne abinda yakeji gameda maleek din ya sassauta kallonsa zuwaga gawar da aka dauka za’a shigar ambulance ya waiwaya ya kalli yakoob Yana cewa”
A tabbatarda gawar kafin su tafi da ita.
Matsowa Mr Omar yayi Ya tarewa yakoob hanzari Yana sauke Kai cikin tsananin girmamawa ga neges Yana sassauta harshe da cewa”