UBAYD MALEEK Page 91 to 100 (The End)

Kwanaki sukai suna fita wani irin shaquwa da sabuwar soyayya me qarfin gaske tasake shiga tsakaninsu musamman da yariga yagama busar Mata da idanu akan soyayyarsa ko Ina Babu ruwansu kissing juna sukeyi musamman shi ko magana take Masa wani lokacin Haka zaibi bakin Yana kissing sbd komai nata kashesa yakeyi.
Yau ba awani gajiye suka dawoba Dan Haka suna dawowa yaqarasa gajiyar dasu akan gadansu aikuwa taqarasa gajiyar gaske kafin sukai wanka suka kwanta bacci.
Wata irin sabuwar rayuwa suke a qasar ta zararrin masoyan da basa ganin kowa sai junansu
Dan kuwa yanzu ko irin kayan datake saka Masa cikin daki sun gama makantar da idanuwansa da ganin kowa bayan ita musamman da yanzu ya koya Mata batada gurin zama sai kan cinyoyinsa da jikinsa.
Tana waya dasu afia sosai saidai har lokacin takasa fada mata inda take tadai sanar da ita Bata tafi delah ba tana gida sbd cewa abata su abal su gaisa afian datai.
Su abal ma dadin duniya da farin ciki ya ishesu duk lokacinda sukai waya da ‘yarsu
Itakuma padima kullum akai waya da NURU sai kaman ciwon ya tashi sbd ta ringa Kiran sunan NURU kenan yinin tana cewa ta yafe Mata.
Satinsu uku cif suka dawo gida har lokacin su afia Basu dawoba sbd afia data gane mahaifiyarta tana samun ‘yar matsalar juyewar Kai wani lokaci shiyasa takira dad din tasake rokon yaqara Mata sati daya yakuma qara musu din.
Koda suka dawo kallo daya mum Sarah tayiwa NURUn ta dauke Kai tana yaba zallar kyau da cikar data Karo shi kansa oga kwata kwatan Mr Omar dinga satar kallonsa yayi Yana Masa barka barka akai akai har Saida maleek din ya kallesa yace”
Yaushe ka zama me saka ido Mr Omar?
Murmushi yayi Yana shafa Kai yace”
Allah dai yaqara maleek lafiya da kwanciyar hankali.
Dan guntun murmushi shima yasaki Yana share Mr Omar din sbd dama yasanshi da ‘yar Karan saka Masa ido musamman daga baya bayan Nan.
Kwanansu biyu da dawowa yayi tafiya tareda Mr Omar bayan yagama aikin bada Baki sbd kedaicin dazata shiga basu afia babushi
A ranar kafin ya wuce yakira afia yace su biyo jirgin washe gari su dawo gida
Afia tace to.
Washe gari da yamma saigasu sun dawo cikin tsananin farin ciki da murna tarbesu ta rungume farhat kafin ta rungume afia din tana cewa”
Oh my God I missed you guys so much
Musamman wannan beautiful sabuwan likitan tamu” taqarasa fada tana kallon farhat data tsuke fuska zatai mgn ta tareda da Bata kiss a goshi tana cewa”
My sweetie kinsan kece farko a zuciyana basai kince komaiba kinji.
Har dakin afia din suke duk su dukansu suka zauna afia na sauke ajiyar zuciya tana lumshe ido tace”
Alhmdlh Ya Allah
Gida me Dadi.
Murmushi NURU tayi tana tayata janye akwatin ta gefe tace”
Keda Zakiyi aure wata Ran kitafi
Amma nidai har banason tuna ranar
I don’t wnt you to leave us” taqarasa fada tana kallon afian cikin kwabe fuska.
Dariya Afia tayi tana miqewa ta dauko wayarta cikin Jakarta tadawo kusada NURUn ta zauna tana cewa”
Hmmm ki shirya to babe sbd nakusa tafiya idan kina maganar aure ne sbd….
Wani tsananin farin ciki NURU tace”
Yaushe kika fara soyayya Banda labari¿
Wane me sa’ar ne wannan?
Dan wani blushing afia tayi tana kallon NURUn kafin ta miqe ta nufi toilet tana cewa”
Zanfada Miki komai kinsani Amma saina hutu yau da daddare akwai fira.
Murmushi kawai tayi tana cewa”
To ahuta lafiya Bari naje na saka hannu a abincin yau abincin dakukafi so za’ayi.
##MAMUH#
*_Mamuhgee 51_*
Sai dare suka samu kansu a dakin afia din ma suka kwana bayan sun kwanta
Afia ta fuskanci NURUn ta sauke ajiyar zuciya da numfashi ahankali tafara cewa”
NURU mum Dina tasamu matsalar juyewar Rabin Kai dayake Dan tashi wasu lokutan idan tana tuno abinda daya faru na wannan al’amarin.
‘dan shiru tayi tana sake juya al’amarin cikin ranta ta bude Baki tacigaba da cewa”
NURU mum ta rokeni alfarmar na amince na auri Imran sbd nuna sha’awarsa da yayi ga aure Dan samun cikakkiyar nutsuwar Bata kulawa shine ta nuna sha’awarta nason auren Hadi a tsakaninmu idan har dad Dina ya amince,
Na zauna nayi nazarin maganarta NURU Nima inason kasancewa tareda ita Dan samun lafiyarta Dan Haka na amince da maganar auren saidai bansaniba ko hakan danayi nayi daidai kokuwa?….
Ajiyar zuciya ahankali NURU tasaki tana kallon afian cikin tsananin tausayinta da qaunarta sbd a rayuwa tasamu gata da dukiya da kyakkyawan asali da ilimi da komaima na rayuwa Allah yabata Amma ta bangaren mahaifiyarta ta hadu da jarabawa me qarfi wadda gashi dai daga karshe tayi sacrificing rayuwarta kacokan akan auren Hadi sbd neman lafiya da kawo sauyi a rayuwar uwarta Wanda hakan yaqarawa NURUn ganin girman afian fiyeda koyaushe sbd tabbas tsakaninta da Allah takeso da kaunar mahaifiyarta komai halayenta kuwa.
Cikowa idanuwansu duk su biyun sukai da hawaye NURU tace”
Ina Miki fatan kyakkyawar nasara arayuwa fiyeda kowa afia,
Allah ya dasa Jin Dadi da kwanciyar hankali tareda soyayya me girma acikin wannan auren Kuma Inshallah dad dinku ma bazaiqi hakan ba sbd burinsa dama akanki karatunki ne Kuma kin kammala Dan Haka burinsa na gaba akanki bazai wuce aurenki ba.
Ahankali ta furta”
Thank you NURU.
Murmushi tasaki tana dafa hannunta ta girgiza Mata Kai.
Washe gari a washe suka tashi kowa da nasa farin cikin sbd takardunsu dasuka fito Kai tsaye tare data aikinsu
Murna da farin ciki a ranar ma Saida sukai partynsu cikin Palo wannan karon afia harda rawa Tasha
Farhat da itama farin cikin ganinsu cikin farin ciki duk ya lullubeta itama tasha rawarta duk da Bata iyaba
Saiga Imran yakira afia din vcall ta zauna sunayi tana gyara gashinta data sauyawa kala daga baqi zuwa dark brown suka fara fira sama sama wadda yawanci idone yake kafe dasu sbd wasu halayenta da kyakkyawar kamilalliyar fuskarta dasuka fara saka Masa Sonta.
Mum dinta yafita yakaiwa wayar suka hau murna mum dinta na cewa”
My baby I love Allah ya albarkaci rayuwarku duka.
Amin ta amsa tareda janyo NURU dake can gefe tana waya da Alama duk wanda take wayar dashi yanada mahimmanci a rayuwarta ta kara Mata wayar tana cewa”
Mum ki gaisa da NURU ki tayata murna itama.
Kallon kallo sukayiwa junansu tareda yin tsit na wasu sakanni kafin NURU ta Dan ago tana kakalo murmushi cikin nutsuwa tace”
Ina wuni?
Ya gida?
Ajiyar zuciya tareda numfashi lailah tasaki kafin ta kalli NURUn cikin nutsuwa tace”
Congrats to you.
Thank you.
Sake kallonta lailah tayi tace”
Kiyi hkr da duk abinda yafaru abaya Ina fatan Zaki yafemun komai ya wuce?
Murmushi NURU tasaki tana girgiza Kai a natse tace”
Yariga yawuce na Dade da yafe Miki sbd girma da darajarda afia take dashi a zuciyata.
Nagode sosai” lailan tafada tana sake murmushin daya qarawa kyakkyawar fuskarta kyau ta Dora da cewa”
Ina gaida farhat.
Jawo farhat NURUn tayi tana cewa”
Sweetie zo ga mum dinki ki gaisheta.
Zama farhat tayi tana karban wayan fuskarta daukeda farin ciki sbd yanzu tafara sakewa da mum din tasu sbd ta sauya sosai yanzu har cikin ranta takeson yayan nata ita Kuma farhat dama tsorone yasata take shakkar kusantar lailan.
Har Imran suka gaisa dashi kafin NURU ta miqe Takoma ga tata wayar datakeyi da Bata oga kwata kwatan Wanda duk wayar datayi da lailah da gaisawa datai da Imran duk yanaji Kuma shima hakan yasashi farin ciki ganin atlast dai afia tasamu soyayyar mahaifiyarta dataketa kwadayi tun tasowarta.