UBAYD MALEEK 1-END

UBAYD MALEEK Page 91 to 100 (The End)

Da daddare sbd gajiya tunda suka kwanta Basu farka ba sai qarfe takwas na safe suka miqe cikin sauri sukai sallah kowa yafara Shirin fita aiki musamman afia datafi NURU buqatan fita da wuri sbd yanayin aikin nasu ba daya ba.

Cikin ikon Allah kowaccensu tafara aikinta cikin aminci da kwanciyar hankali har sun Dan fara sabawa cikin kwanaki kadan.

Yau NURU ce tajasu suka fita tare suka biya ta ajiye afia asibiti kafin ta wuce gurin aikinta tana sake trying numbern MALEEK dabata shiga tun safe rabonta dashi tun jiya cikin Daren dasukai vcall.

Tunanin rashin samunsa yasakar Mata ciwon Kai da damuwa qarshe Bata Bari yamma tayi sosaiba ta tattara ta baro office din harta Kama hanyar zuwa gida ta fasa ta nufi asibiti gurin afia sbd tayita kiranta tafada Mata zata wuce gida idan tagama takira zata Aiko Edward yazo ya dauketa Amma afian Kuma Bata dauki wayarba shiyasa Mata biyawa asibitin Dole tana sakin Dan qaramin tsaki sbd kanta dake tsananin sarawa

Tana yin parking cikin asibitin saidata dakata cikin motar ta sauke ajiyar zuciya da numfashi sbd yanzu Kam kaman hadda jiri tana gani Haka ta daure ta fito sanyeda shades sbd Rana ta nufi ciki.

Direct hanyar office din dazata samu afia wato office din Dr Damien ta nufa saidai kafin ta qarasa tana daf da Isa ta dakata sbd wani jiri daya dibeta tayi gefe zata Fadi afia data hangota zuwa ta taso tana kawowa ta tareta cikeda mamaki da ‘yar damuwa tana kallonta tace”

Lafiyanki kuwa???

Gyara tsayuwa NURUn ke kokarin Yi tana Dan dafe goshinta ahankali tace”

Bansaniba kawai ciwon Kaine yake damuna yanzu Kuma Kamar karna baro office jiri yafara kamani Ina ganin stress ne da rashin bacci.

Kallonta afia keyi da kyau kafin ta gangaro da idanuwanta zuwa kirjin NURUn ta kalla tasake maida idanuwanta kan fatar hannuwan NURUn saitaga kaman Bata gani sosai ta kalli NURUn tana cewa”

Bana tunanin stress ne kadai muje nadubaki mugani sbd jiri matsala ne zai iya jefar dakai inda zaka halaka kanka.

Suna Shiga office din Dr Damien ta zaunar da NURUn tana juyawa ta dauko ruwa takawo Mata ta Bata Tasha ta durqusa gabanta tana cewa”

Muji pulse dinki.

Bata hannunta tayi ta riqe tana Jin pulse din NURUn tayi shiru zuciyarta na bugawa 

Duk Bata yarda ba ta juya da ita kan gadon scanning din dake office din Dr Damien din NURU ta kwanta tana gyara Mata kafafunta.

Tana Dora Mata abin scanning din take cikin jikin NURUn ya bayyana baro baro ta ajiye abin tana kallon NURU da cikakken mamaki da tsoro harma da shakku da firgici duka 

Bakinta na rawa Kai tsaye ta fuxgo kalmar cikin tsananin mamaki tace”

NURU you are 7weeks pregnant.

Da sauri NURU ta kalleta tana saukowa daga gadon tana goge jikinta da tissue ta Dora hannunta kan cikinta cikin son tabbatarwa tace”

Pregnant???

Ni¿

Wani irin Murmushin farin cikin da Bata taba tsammanin yiba ta sake dafe cikin tana dagowa ta kalli afia datai mutuwar tsaye tana kallonta cikin mugun mamakin da batasan lokacinda bakinta ya furta”

Dad ne???

Sai alokacin kunyar afia din takama NURU ta Dan takaita farin cikinta tana kallonta ta daga Mata Kai ahankali tana cewa”

Yes wannan qaninki ne afia.

Wani yawun sabon mamaki afia ta hadiye tana sake dulmiya cikin tunani da tsananin mamaki alokaci daya Kuma hadda kunya tana kamata 

Daga ita har NURUn sai suka samu kansu da kunyar juna afian tayi saurin juyawa tana zaro takardar scanning din da batama Gama dubawa ta miqawa NURUn ba shiri bakinta na furta”

Congratulations.

Kallonta NURU tayi ahankali tace”

Thank you tana sakin murmushi.

Bakin afia mutuwa yayi murus da mamakin al’amarin dakuma kunyar dad dinta Haka ta raka NURUn har mota Dan Dole itace taja motar tabar gurin aikin ranar saidai Kuma gobe suka nufo gida tana satar kallon NURU wadda farin cikine fal cikin ranta Allah zai Bata ‘da ko ‘yar kanta.

Suna shigowa gidan tun daga motocin maleek dake harabar gidan taga alamun an sauya musu parking wanda hakan ke nuni da yadawo kenan 

Cikeda murna ta fito motar tana mantawa da komai ta nufi hanyar office dinsa na cikin gidan dayake aikin office aciki sbd hango Mr Omar agurin tasan Yana can Dan Haka ta nufi gurin cikin tsananin farin ciki da murna.

Tsaye suke daga bakin kofa tareda baqinsu ‘yan China dasukazo wani aiki harsun Gama magana sun fito kenan zasu wuce ya hangota tana tahowa 

Sanin sabon daya koya Mata da yanayin yanda take tahowar ya tabbatarda abinda zai faru ya hadiye wani ‘dan yawu ya waiwaya ya kalli Mr Omar Wanda take yagane kallon ya matso Yana washewa bakin Baki Yana nuna musu hanya da cewa”

chairman Zhou let me see off please?

Gyada Kai sukai suna sake bawa maleek hannu suka tareda Mr Omar zuwa gurin motocinsu da securities ke zagaye suna jiran fitowarsu.

Da gudu ta qarasa qarasowa ta fada jikinsa tana Dora bakinta kan nasa ta bashi wani lafiyayyan kiss daya sanyashi dagota ya kalli fuskarta kafin yasake maida fuskarsa yayi kissing din lips dinta Yana fidda wani lafiyayyan murmushin dayasa afia kusan suman tsaye sbd Bata taba ganinsa akan fuskar dad dintaba 

Ita gabaki daya daburcewa tayi ganin abinda idanuwanta suka ganar Mata wato dai ba yanzu bane al’amarin ke faruwa sbd komai data gani ya nuna dad dinta ya dade da tsunduma wata sabuwar daddadar rayuwa hakama NURUn.

Wayyo Allahna” tace tana juyawa da sauri zata bar gurin sbd ita duk kunyar komaiba ya rufeta Jin take Kamar ta nutse a qasa 

Tana juyowa saura kadan suyi Karo da Mr Omar da shima yake tsaye agurin Yana jiran sugama soyewar ya qarasa.

Kallon kallo sukai itada Mr Omar dake sakin murmushin Haka yakeson ganin megidansa ya sake kallon gefen su maleek din ya juyo ya kalleta da ido yayi Mata alamar tasake waiwayawa tagani

Ta juya ahankali daidai lokacin NURU ta Dan daga duga duganta takai bakinta kan kunnensa daya rankwafo yana riqeda qugunta cikin rada tace Masa”

_Nenyì Irìguzí_ (Am pregnant).

Wani irin Abu yashigesa ya dagota ahankali yana kallon cikin idanuwanta da ido yake tambayar” da gaske??

Kai ta gyada tana zagayo da hannuwanta qugunsa tana cewa”

And I missed you yau duka bani muryanka ba.

Dago fuskarta yayi ya hade bakinsu yabata wani irin lafiyayyan kiss daya sata kallonsa a kasale tace”

Are you this happy??

Kamar yaro haka ya daga Mata Kai Yana kamo hannunta suka nufo ciki 

Afia da Mr Omar sukai saurin barin gurin har suna ture juna tayi saurin fadawa Palo ta nufi dakinta da gudu tana cewa”

Heyyyy

NURU kin wuce tunanina

Dad kuma bazan iya cewa komaiba sbd yau Naga asalin MALEEK da bakowa zai taba samun damar ganiba sai su Mr Omar ‘yan kullum da kullum din MALEEK.

Suna shigowa dakinsa suka wuce Kai tsaye acan aka qarasa sauran murnar da farin cikin cikin Wanda yasata mamakinsa Dan Bata dauka yanada sauran son haihuwa har hakaba.

Sai dare gurin cin abinci Afia tasamu ganinsu lokacin ba kunya NURU tayi wanka tana sanye da wata lalatacciyar riga Mara tsayi Sosai gashinta daure tsakiyar Kai kaman baby shikuwa akai akai idanuwansa na kanta 

Duk sai taji abin wani iri saidai Kuma farin cikin data gani taredasu din ya tabbatar Mata da ba qaramin so sukewa juna ba

Ta ajiye spoon dinta ahankali ta dago ta kallesu cikin farin ciki tana murmushi tace”

Congratulations dad you are having another child Allah yakawo manashi lafiya.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button