UBAYD MALEEK Page 91 to 100 (The End)

Cikin girmamawa Mr Omar yace”
Maleek haryanxu Yana maganar son ganin ‘dansa Kuma idan aka bayyanar a kotu cewan ‘dansa ne ya mutu zai iya bayyana komai a gaban kotu Wanda zai taba gizah da Kuma Anneti sbd al’amarin zaizo Mata da tashin hankali tunda Bata taba tsammanin hakan ba daga Wanda take aure
Kana ganin yakamata mu fitar da zancen duka a kotu?
Yan media zasu yada abin fiyeda komai ta yanda zai Yi Muni.
Shiru maleek yayi na wasu mintuna kafin yace”
Yanada damar yasan mutuwar dansa saidai baida damar fadar komai bayan abubuwan daya aikata da wannan za’a yanke Masa hukunci basai anbari yafada komaiba bayan wannan…..
Shiru yayi Yana kokarin daure abin dayake ji a zuciyarsa dasuka bayyana a idanuwansa yaci gaba da cewa”
Neges Kuma sbd daraja ta auren Anneti zanji da matsalarsa ta cikin gida batareda duniya tasan abin daya aikataba sauran haqqin Rai dake kansa Kuma tsakaninsa da ubangijinsane.
Cikin yanayi na sanyi shima Mr Omar yace”
Allah ya kyauta ya sake tsare imaninmu
Allah Kuma yaqara maka tsarkin zuciya.
Ba Haka suka so ba duk su dukan Amma Kuma wani lokacin kanayin abinda shine zaman lafiyar kowa da Hana fitina.
Lokacinda aka tafi da yakoob har mortuary aka jawo gawa tareda yaye Masa yaga gawar ‘dansa amed datai fari tas sbd ajiya da sanyi.
Sarewa qafafuwansa sukai sbd firgicin ba zata daya fizgesa lokaci daya da wannan mugun ganin dayayi
Cikin tashin hankali ya zube gaban gawar Yana ihun Kiran sunan”
Amed Amed Inidēti ibakíhìni¿
Yaushe wannan mummunan Abu yasameka batareda nasaniba?
Amed katafi kabarni Banda kowa sai kai.
Dagowa yayi cikin ficewa hayyaci da tashin hankali ya kalli Mr Omar Yana cewa”
Meyasa???meyasa??
Ta yaya?
Yaushe kuka kashesa?
Meya muku?
A Daren ranar daya tafi aikin neges yamun saqon cewa Yana lafiya tafiyan gaggawa yayi…..ko shekaran jiya yamun sakon Yana lafiya Dana kira..yaushe kuka kashesa…..
Kukan tashin hankalin masifa yakeyi sbd sanin tsaf wannan umarnin maleek ne ya sake gangaro da hawayen baqin ciki jikinsa na daukan rawar Shiga tashin hankalin rashin tsammani na wannan afkuwar dabai taba kawowa aransaba ya rasa dansa kwalli kwal Wanda duk suke wannan fafutukar rayuwar dansu tsira su Tara abin kansu su gudu wani gurin su Gina rayuwa.
##MAMUH#
KUYI MANAGE YAU INADA UZURI DAN ALLAH.
*_Mamuhgee 48_*
Kallon yakoob Mr Omar yayi Yana gyara tsayuwa yace”
Allah ya yafe Masa kurakurensa tareda Kai mahaifinsa daka dorasa akan irin wannan rayuwar da batada hanyar bullewa ko a duniya ko agurin ubanginka,
Son Rai da bin zuciya qarshensa baida Dadi yakoob Amma tunda kune kuka zabi hakan hakan shine daidanku,
Babban kuskuren daka aikata yakoob shine sako ‘danka da baida kwarewa acikin wannan harkar dakai ka Jima da dadewa acikinta Dan kuwa gashi kuskurensa yakaisa ga Haka kaima yakaika ga hakan.
Allurar meriz ce ta kashesa kaman yanda kukai amfani da ita Dan kashe tsohon NEGES mahaifin maleek Kuma kukaso kashesa da ita,
Kun aikashi kashe padima saidai kun manta cewan a sashen maleek ne take
Kuma a sashen Babu wani lungu da Babu camera a maqale Wanda idonku da zuciyarku sun rufe da aikata hakan kuka saka Amed disconnecting dinsu Wanda ko karatun addini bayadashi bare na zamani Dan Haka ta Yaya kuke tunanin zainiya ciresu.
Ranarda muka samu labarin zuwan lailah gizah muka tabbatarda akwai dalilin zuwan nata Wanda anyi kirantane Dan ayi amfani da ita hakan yasa muka sauya tunani ta hanyar Dena shayarda padima meriz sbd ga hanyar sauki tazo Mana,
Tunda neges yayi magana da lailah tafara bibiyar jekadi Wanda jekadi tagane hakan ta sanar Mana daga lokacin mukasan meyake faruwa har lokacinda muka tabbatarda amed na bibiyar lailah itama bamui wani motsiba muka barku Dan ku aiwatar da naku Shirin dazai bamu tamu damar.
Kaf gizah Babu Wanda yasan da padima na cikin masarautar shiyasa muka kyaleku Dan munsan Dole bazaku barta ba duk da batasan ainihin waye yasakata aikin daya sakata ba ahaka rashin nasararku yakaiku aika amed kashe padima wadda taji sauki da kanta zata iya Kare komai kuma a Daren ranar jekadi ta miqa Mata allurar meriz a hannunta ta sanarda ita duk Wanda ya shigo kawo Mata farmaki ta tabbatarda ta kwaci kanta da allurar Wanda hakan zai fidda ita daga wannan rigimar gabaki daya har abada.
Padima na son ranta fiyeda masoyinta amed Wanda shima yakeson dukiya fiyeda rayuwarta Dan Haka a Daren ranar abindaya faru shine bayan yaja lailah da dubara zuwa gurin Dan kisan ya hau kanta mun gani Kuma mun sanarda jekadi komai kafin isowarsu gurin Dan Haka jekadi tasake nanatawa padima tana sane ya fito lailah ta doketa saidai bamuyi tsammanin amed yaqara doke jekadin ba yasamu ya qarasa dakin ya bige lailah ta hanyar kwada Mata katako akai Wanda ganinsa yasa padima shiga tashin hankali saidai Bata Bari tsoronta yabarta barin amed yasamu sa’ar kashetaba tayi amfani da matsayinta na mace ta nuna Masa kanta amatsayin su Raya darensu na qarshe kwadayin Zina yajasa ga rasa ransa batareda yasamu abinda yake kwadayinba.
Babu Wanda yasan padima na kasar tayaya Yan jaridar suka San waye aka kashe bayan Babu Wanda yaga gawar da idanuwansa wannan shine babban kuskurenku na biyu daya kawo karshenki batareda ansha wuyar hakan ba,
Padima ta kashe amed sbd Kare Kai itama Allah yabata nata sakamakon ta hanyar rasa cikakken hankalinta kamar lailah Da Haka kowa zai girbi nasa aikin.
Allah ya tsare Mana imaninmu yabamu kariya daga mutane kamarku Wanda suka Tara arziki ta hanyar kisa da miyagun ayyuka gashinan dukiyar Zaki tafi ku barta abawa mutane suna Kuma tsine muku.
Juyawa yayi ya fice yabar yakoob din tsaye cikin rashin sanin makamar tunanin Yi sbd dukkanin gangar jikinsa da jininsa sun tsaya cak Babu abinda yake motsi ajikinsa bayan zuciyarsa dake bugawa ahaka aka jasa Yana tangadi aka fice dashi
Take ‘yan jarida aka sakar musu labarin suka fara yadawa cewan
Yakoob amintaccen bawan neges ne ya kashe tsohon NEGES na gizah
Take aka bayyanarda shedu dasuka hada da garin meriz dake ciki sarkar da padima ta taba boyewa da aka samu a sashensa gurin bincike.
Hankalin jama’ar gizah ya tashi tareda girgiza matuqa sbd kishin kishin fara zargin NEGES da akai Wanda yasa akai gaggawar yankewa yakoob hukuncin kisa ta hanyar cire kansa sbd kada ragewa fitinar tsayi
Amma duk da hakan ba a daina bayyanarda zargin NEGES ba Wanda yasashi kasa fitowa sbd tsananin kunyar kansa da baqin ciki me nauyi daya lullubesa sbd Kai tsaye ko an boye laifinsa saidai yasa jama’a yin shiru Amma wannan zargin da laifinma gabaki daya bazai rufu ba musamman da kaleeb da maleek sukai shiru sunki saka Baki a maganar sai hakan yasake bawa jama’a kwarin gwiwa aka fara kishin kishin sauke neges jama’a da jinin sarautar gizah da ‘yan delah gabaki daya kowa yafito ya nuna sha’awarsa ta sauyin neges sbd kobabu saka hannunsa zamtowar bawansane ya aikata hakan to tabbas hakan ya shafesa Dan Haka gabaki daya kusan ya rasa girmansa da mutuncinsa a idon jama’a
Musamman Anneti da yakejin Kamar bazai iya hada idanuwa da itaba sbd girman kunyar abindaya aikata Wanda yasan itama yagama fahimtar komai saidai kawai tayi shiru sbd wani abin basai kafadaba Allah ya kyauta kawai yafi maka saukin fada