UKUBAR KISHIYATA Page 1 to 10

*~Praise is to Allah Who gives us life after He has caused us to die and to Him is the return~.*
*~Part one~*
Babban shopping mall ne mai girman gaske,wanda yake cike da kayan zamani kama ga kayan masarufi zuwa sutura,kayan kwalama da kayan tand’e-tand’e.
Duk wanda ka gani a wajan toh tabbas babban mai kud’ine ko kuma mai fad’a a ji a kasar ko kuma d’an siyasa dan haka kana zuwa bakin mall d’in sai ka saki baki wajan kallon masu zuwa shopping d’in, saboda ka zaci ko gasan nuna motoci ake ko gasan na sutura da k’walliya ake.
A’ameen da matarsa Latifa suna cikin masu shopping a wannan mall d’in,suna zagawa a hankali tare da zab’an abinda suke so fuskokinsu d’auke da murmushi kana ganinsu kasan hutu da naira sun gama ratsa jinkinsu.
Latifa sai jido kaya take hankali kwance Al’ameen na biye da ita, bayansu kuma ma’aikacin wajan ne yana tura d’an keken zuba kaya,duk abinda ta zab’a ta d’auka cikin keken take jefawa har suka gama sayayyan suka zo wajan da za’ayi musu bill.
Makud’an kud’in da zasu biya aka fad’a musu wanda ya ishi wani talakan yayi jari bayan na’uran ta gama lissafin kayan.ba tare da wani fargaba ko b’ata lokaci ba yaciro bounchs d’in 1k guda 2 ya ajiye suka fice zuwa parking lot abinsu ba tare da jiran canji ko kayan da suka saya ba.
Suna zuwa wajan motansu Al’ameen shiya bud’ewa Latifa gaban mota ta shiga ta zauna ya maida k’ofan ya rufe sannan shima ya zagaya driver seat ya bud’e ya shiga ya zauna,sai ga yaran mall d’in su 2 ko wanne da kaya niki-niki a hannu sun biyo su.boot Al’ameen ya bud’e musu suka zuba musu kayan suka rufe,sannan yaja motan suka fito a compound d’in mall din suka mik’e zuwa gidansu dake unguwar dosa.
Suna tafe suna hiransu cikin jin dad’i da annashuwa, suna wuce manyan gidaje masu k’yau har suka kawo bakin wani tangamemen gida mai kyau wanda duk layin ba gidan da ya kaishi k’yau da tsaruwa.
Tun kamin yayi horn mallam isa mai gadi ya bud’e musu k’aton gate d’in ya kutsa kai ciki.
Parking lot ya nufa wanda yake cike da cars birjik kala-kala kaman ta sayarwa,waje ya samu ya parker motan sannan suka fito zuwa cikin gida.
Masu aikin gidan sai tururuwan fitowa yi musu barka da zuwa suke,wasu kuma suna kwashe kayan da suka sayo na cikin boot suna shiga da shi cikin gida.
Cikin takun katsaita da da natsuwa suka shigo cikin waiting palour inda suka tarar da d’ika-d’ikan ‘yan mata su 2 suna zaune suna charting a wayarsu.
D’agowa sukayi suna musu sannu da zuwa,kai tsaye Al’ameen ya wuce main palour,ita kuma Latifa ta nemi waje ta zauna cikinsu tana “wash Allah na gaji”.
Har ya kai hanyar da zata sada shi da main palour ya tsaya ba tare da ya juyo ba yace” Latifa zo ki had’a min ruwan wanka” bai jira amsanta ba ya wuce ciki zuwa main palour wanda yafi wancan girma da tsaruwa komai na palourn maroon nd black ne hakan ya k’ara fito da k’yan palourn.
Hanyan part d’in shi yayi,yana taka stairs d’in a hankali har ya shigo palourn shi da yaji komai purple nd white ,an tsara shi sosai dan yafi main palourn kaya masu k’yau da tsada.
Bedroom ya wuce ya fara rage kayan jikinshi,hulan kanshi ya cire ya ajiye a kan side drower yayi dai-dai da shigowa Latifa,wuce shi tayi zuwa bathroom ta had’a mishi ruwan wankan.
Koda ta fito ta same shi ya gama cire kayan shi daga shi sai boxer da vest,tana murmushi tace “an gama ur Highness every thing is set”
Murmushi ya maida mata sannan ya wuce zuwa bathroom d’in.
Down stairs ta sauk’o har zuwa waiting palour,Fa’iza da shamsiya suna zaune suna chating kaman yanda ta barsu.zama tayi cikin su tace…
” ku dai kam ba kuda wani aiki sai ta latse-latsen waya,kuma me kuke jira tundazu a waiting palour?”
Fa’iza tace” uhum Aunty kenan chating fa muke kuma muna jiran wata friend d’in mu data ce zata zo”.
“Hmmmm chatin ko,ba karatu ?yayi muku kyau”.
Fa’iza tace”yauwa Aunty shekaran jiya dana je gida mama tace in fad’a miki tana buk’atan wasu kud’ad’e”.
Harara Latifa ta balla mata sannan tace “shine sai yau kike fad’a min?”
“Wallahi Aunty mantawa nayi”tace tana maida hankalinta kan wayarta.
“Laifina mama zata gani taga kaman na share tane,haba aiko wannan jaraban charting d’in da kuka d’aura akan ku ba zai barku ku tuna da kanku ba bare wani abin”.
Shamsiya tana jinsu bata ce komai ba.
Latifa mik’ewa tayi hanya part d’inta tana ta mita.
Wanka ta farayi sannan ta had’e cikin arnen less maroon d’inkin riga da skirt ya zauna das a jikinta.
Make up tayi mai rai da lafiya kaman mai zuwa gidan biki,perfumes masu d’an karan kamshi tayi amfani dasu wajan feshe jiki ta sannan ta tashi a gaban mirrow ta dawo kan gado ta zauna.
Hannu ta mik’a ta d’auko wayanta da ta ajiye akan pillow,no mamanta ta dannawa kira,yana fara ringing,sai da ya kusa katsewa sannan ta d’auka.
Sallama tayi ta amsa bayan sun gaisa Latifa tace” mama dan Allah kiyi hak’uri,wallahi ban samu sak’onki ba a wajan shamsiya sai yanzu take fad’a min kuma ashe tun wai shekaran jiya kika fad’a mata”.
“Haba Latifa yarinya ‘yar kwalisa tauraruwan ‘yan mata ba sai kin bani hak’uri ba,nasan baki samu sak’ona ba akan lokaci saboda nasan ba kya wasa da al’amarina”.mama tace a d’ayan b’angaren.
‘Yar dariya tayi mai cike da jin dad’in irin yabo da kirarin da uwarta take mata tun kafin tayi aure,tace “toh mama gobe insha Allah Shamsiya ko Fa’za zata kawo miki saboda yanzu dare ya farayi”.
Cikin farin ciki tace ” yauwa Latifata godiya nake”.
“Uhum mama ina baba?”Latifa ta tambaya.
Tabe baki Mama tayi kamin ta amsa ” wannan solofiyon uban naku yana can me mataccen zuciya me ya iya banda zaman banza”.
“Toh Mama sai da safen ko “?”Latifa ta katse Mama duk da tunda suka taso haka taga tsakanin Mama da Babansu amma sam baya mata dad’i.
” Toh Allah ya kaimu ‘yar kwalisa”.
Ajiye wayan tayi ta kwanta rigingine a hankali kan gadonta tana tariyo rayuwarta ta baya da yanda burinta ya cika na samun miji mai kud’i dan ta zama tauraruwa a cikin familynsu,nd ra’ayinsu da tsarinsu yazo d’aya dana uwarta nason kud’i.yanzu haka ita ta d’auki nauyin wasu daga cikin ‘yan uwanta,shiyasa ta d’auko shamsiya da Fa’iza kannenta su samu karatu mai k’yau da inganci kuma suyi kasuwa.
Hope u will like it.
✍✍✍✍✍✍✍✍✍✍✍✍
[3/24, 6:46 AM] Ummee Yusuf: . ????♀????♀????♀????♀????♀????♀
*~UKUBAR KISHIYATA~*
????????????????????????
( its all about love and betrayal)
Story by *~UMMEE YUSUF~*
(Maman Yusuf)
???? *FAGEN MARUBUTA WRITERS ASSOCIATION*????
( *Gidan zaman lafiya hadin kai, aminci da yardar juna insha Allah*)
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~Gaskiya naji dad’in yanda kuka nuna min kauna da goyon baya ta hanyan comments,ina yinku sosai sosai.dan haka nima zan cigaba da antayo muku ba kakkautawa~*
*~ADDU’AN DA MUTUM ZAIYI A LOKACIN DA ZAI SAKA KAYA~*
الْحَمْدُ لِلّهِ الَّذِي كَسَانِي هَذَا (الثَّوْبَ) وَرَزَقَنِيهِ مِنْ غَـيـْرِ حَوْلٍ مِنِّي وَلَا قُـوَّةٍ
*~ALHAMDU LILLAHI LATHEE KASAANEE HAATHAA (ATHTHAWBA)Wa RAZAQQNEE MIN GYAYRI HAWLIM WA LAA QUWATIN~*
Praise is to Allah Who has clothed me with this (garment) and provided it for me, though I was powerless myself and incapable.