UKUBAR KISHIYATA 1-END

UKUBAR KISHIYATA Page 1 to 10

” eh nagani ai su 2 ne” shima ya amsa mishi.

Tunani ya tsaya yi,ya zaiyi tunda ance su 2 ne kuma gashi bai san sunan wacce yake nema ba.

Dabara ce ta fad’o mishi ya kalli almajirin yace ” yi maza ka koma kace ana sallama da ‘yan matan gidan”.

Da toh ya amsa ya koma cikin gidan yayi sallama,

Umma ta sauke uban tagumi da zabga tace ” haba almajiri nace maka Allah ya bafa sa’a tundazu ko?”

” ni ba bara nazi yiba wani ne a waje yace ana sallama da su 2 nan” yace yana nuna su amira dake zaune da yatsa.

” su 2nan?” Umma ta k’ara tambaya tare da dafe kirji.

” eh da mota ma yazo ” yace tare da ficewa abin shi.

Zuciyar Amira sai bugawa yake tace ” oh! ni Amira kar dai mutumin jiya ne ya dawo?”

Umma ne ta katse mata zancen zuci da take tace ” sai kuje ku gani dame yazo kuma kar ku mantavda maganan Babanku”.

Dogayen hijabansu suka sa sannan suka fita suka bar Umma da tunanin waye yake neman ‘yan matan ta duka 2 kuma harda mota.

Al’ameen yana nan tsaye almajirin yazo yace ” wai suna zuwa”.

Hannu Al’ameen yasa a aljihu ya ciro 200 note ya mik’a mishi tare da cewa ya gode.shima karb’a yayi yana ta murna ya tafi.

Tun a zaure Fateema ta fara yiwa Amira magana ” kina ganin waye zai zo neman mu anya ba mutumin da ya taimake ki jiya bane?”

Ganin sun fito k’ofar gida yasa Amira k’ara yin k’asa da kai ba tare da ta amsa mata ba.

Tunda suka fito ya kafe Amira da ido yana kallon yanda take taku cikin natsuwa.

D’an nesa da shi suka tsaya a tare suka d’an duk’a suka gaishe shi.

Amsawa yayi cikin murmushi yace ” dan Allah wacece a cikin ku jiya muka had’u da ita ta taso daga makaranta?”

Fateema ce ta d’ago kai suka had’a ido ta kalli k’yawawan mutumin nan tayi murmushi tace ” gata nan yayata ce”.

” ok good ya sunanki please?”

” Fateema” 

” yayarki fa ?” ya k’ara tambaya.

” Amira sunan ta” ta bashi amsa.

Murmushi ne ya kwace mai jin sunan ta mai dad’i yace ” toh fateema nagode dama Amira nake son gani”.

Sallama tayi mishi ta koma ciki.

Musa ma ganin haka yasa yayi gaba ya basu waje.

Kallonta yake ba ko kitawa ganin har yanzu tak’i d’ago kai.

Gyaran murya yayi sannan ya kira sunata cikin sanyin murya.

Amsawa tayi da tsiririn muryarta still kanta a k’asa.

” tunda nake ban tab’a ganin mai suna amira marowaciya ba sai a kanki”.

A d’an razane tace ” rowan me nayi maka kuma?”still kanta yana k’asa at d same time tana mamakin wannan mutumin ita meye gare ta da har zaice tayi masa rowa.

” kusan 24 hrs da  mu amma kin hana ni kallon prity face d’inki”.

Bata san lokacin da ta saki ‘yar dariya ba har tsiririn wushiryan ta ya bayyana sannan ta d’ago kai a hankali suka had’a ido.

Tasbihi ya fara a zuciyan shi ganin k’yaunta mai firgitarwa.

Amira fara ce sol wanda har ja-ja take gata da dogon hanci da ya dace fuskanta ga maidaicin bakinta tare da idanun ta masu oval shape.in short  Amira tayi 100%.

Kanta ta mayar k’asa dan ba zata iya jure irin kallon k’yakyawan fuskan shi ba.

Cike da tsokana yace ” woah ashe da  2 kike b’oye min fuskan ki dan u re so ugl…..”yasa hannu ya rufe bakin shi yana dariya tare da hana bakin shi k’arasa maganan.

B’ata fuska tayi ta d’ago tana kallon shi dan ta rasa bakin magana.

Shi kuwa shagala yayi da kallonta dan gani yayi tkaman ma tafi k’yau da ta b’ata fuskan.

Dariya yayi  yace ” am sorry just kidding u re d most beautiful girl dat i hav ever seen in my life”.

Batayi magana baba sai dai murmushi da tayi tanan kallon gefe.

“Duk da baki damu ki san suna ba i’m Al ‘ameen nazo ne mu gaisa kuma mu san juna “.

Hannu yasa a aljihu ya ciro bounch ‘yan 200 yace ” ga wannan ki sayawa k’anne na choculate ni zan wuce office”.

Kallon kud’in tayi ba tare da ta karba ba tace ” nagode ka barshi kawai dan in na shiga ciki da shi Umma zata min fad’a kuma ko fitowan nan da nayi in Abba yazo shima fad’a zaiyi”.

Ji yayi ta k’ara burge shi tare da samun special place a hrt d’in shi.yace ” toh shike nan ki turo min Fateema muyi sallama”.

Amsawa tayi tare fa yi mishi sallama ta shiga ciki.

Tana shiga ta tarar da Fateema ta zage tana bawa Umma labarin wanda yazo gun Amira .

Waje ta samu gefen Umma ta zauna sannan ta kalli Fateema tace ” wai kije kuyi sallama”.

Cikin zumud’i Fateema ta fice.

Umma kallon Amira tayi tace ” da fatan kin fada mishi Abban ku baya so ko”?

Tace ” na fad’a mishi Umma”.

” yauwa gara ki ki fad’a in ba haka ba koni ba fita zanyi a wajan Abban ku ba”.

Fateema tana fita ta same shi yana tsaye a inda suka barshi,tace ” gani”

” Fateema dama dan muyi sallama ne kuma ga wannan ki sayi choculate”.

Zaro ido tayi gani kud’i sabbi fil suna d’aukan ido tace ” lah-lah Abba zai min fad’a ba zan karb’a ba”.

” ki kaiwa Umma ” yace .

“A’a itama ba zata karb’a ba ” tace tana baya dan sisai kud’in sun tsoratata.

” in kince injini zata karb’a ” yace yana kara mik’o mata kud’in.

Hannu 2 tasa ta kar’ba sannan tace ” ka jira ni anan dan in tace ba zata karb’a ba zan kawo maka kud’inka “.

Murmushi yayi ganin yarintar ta yace mata ” na yarda je ki kai mata ina jiran ki”

Da sauri tayi hanyan cikin gida.

Yafito musa yayi da gannu suka shiga mota suka bar  anguwan.

Share this

[ad_2]

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button