UKUBAR KISHIYATA Page 1 to 10

*~part two~*
Mallam Garba mai kayan miya da matarsa Hindatu cikakkun ‘yan garin zaria ne.Allah ya albarkaci auransu da.’ya’ya 3 duka mata.
Latifa itace ‘yata farko,akwai d’an tazara tsakaninta da mai bi mata wato shamaiya ta bata kusan shekaru 10.
Shekara d’aya da rabi kawai shamsiya ta bawa Fa’iza data kasance autarsu dan daga kanta haihuwar ta tsaya musu.
Mallam Garba irin mutanan ne da abin duniya bata dame su ba,hasilama shi ba mai magana bane.tsabanin matarshi Hindatu da takasance mayyar kud’i gata da zunzurutun kwad’ayi,baya ga haka masiffafiyace ta bugawa a jarida.
Dalilin haka ta raina mijinta take abinda taga dama,shi kuma ganin tafi karfinsa yafita harkanta tare da zuba mata na mujiya.
Halinta sak na son kud’i ‘ya’yanta suka taso dashi more especially Latifa da tasu tazo d’aya da ita.
Duk abinda zasuyi indai zasu kawo mata kud’i toh fa batada matsala.dan haka Latifa tun tana s.s1 ta fara bin maza a lokacin ba ta fi 15years ba.
Maza ba irin wanda bata huld’a dasu amma babban saurayinta wanda suke son juna da gaske shine Salees.
A haka har ta kare secondry school,da cuku-cukun salees ya samo mata gurbin karatu a A.B.U zaria.
Da burin a ranta ta shiga sch d’in,babban burinta shine Allah ya had’a ta da saurayi d’an masu kud’i dan dama karatun bai dameta ba.
Ta shiga A.B.U da sa’a cox a lokacin an kawo musu sabbin malamai ‘yan service.
Al’ameen mudassir yana d’aya daga cikinsu, ya kasance crsh d’in kowace yarinya mai ji da kamta a cikin sch d’in.shi yake d’aukansu languagelanguage.
Latifa tana d’aura ido akanshi taji duk duniya ba wanda take so bayan shi,bare ma da taji yanda ake zuzuta cewa mahaifin shi Alhaji Mudassir babban d’an kasuwa ne anan cikin gida da k’asashen waje.duk k’asashen da turai dana larabawa wa’yan da suka cigaba a duniya ,yana da companies da shares ba adadi akowane k’asa dan haka fad’an yawan kud’in shi dogon zance ne.
Duk haukan da ‘yan matan keyi akansa ko kallo basu ishe shiba,saboda classy guyne shi
Alhaji mudassir inuwa haifaffen garin katsina state a batsari local govement.
Alhaji Mudassir ya gaji filaye da gonaki da sauran kadarori masu tarin yawa daga mahifinshi Alhaji Inuwa wanda ya rasu tun yana d’an shekara 17.
Bayan ya had’a degreensa na farko ya fara juya dukiyan shi,kuma cikin sa’a ya fara dan Allah ya sanyawa kasuwancin nashi albarka dan komai ya tab’a sai ya zama kud’i.
Auren zumunci akayi musu shida matar shi Halima wacce ta kasance ‘yar baffan shi.bayan auren ne ya dawo kaduna da zama.
Allah ya albarkace su da yara 6 duka maza,Hafiz,Fawad,sudais,sa’ad,yusuf sai auta al’ameen.dukansu yayunsa 5 d’inan sunyi aure suna zaune suma nan cikin kadunan sai shi kad’ai ake sa ran ganin nashi in ya gama service d’inshi.
Alhaji mudassir ya d’aura ‘ya’yan shi kan harkan kasuwancin sa,Sa’ad shine kad’ai yake son yin aiki.doctor ya karanta ,ganin yafi son aikin shi akan kasuwanci yasa Alhaji ya gina mishi asibiti anan cikin kaduna yake aikin shi.
Abinda Latifa ta lura dashi shine,Al’ameen yafi son mace mai kamun kai da shigan mutunci.saboda in yana musu lectures ta lura in akayi tambaya yafi daraja tambayan wacce ya ganta cikin shigan mutunci.
Nan itama Latifa ta dage da shigan mutunci musamman tasa akayi mata d’inkunan hijabai dogaye masu hannu har k’asa,duk dan ta ja hankalin shi,sannan duk wani hanyan da zai had’ata da al’ameen kuwa shi take bi.
Tayi sa’a dan sosai take burge shi wasa-wasa ta samu fada a wajan shi,har ya kai suna hira.kullum sai ta bi shi office ta fake da sunan karatu su sha hiransu.
Wani abinda ya d’aure mata kai game da al’ameen shine duk shak’uwar da sukayi bai tab’a furta mata kalman so ba,dan haka ta nemi shawaran k’awarta aina’u.
Labarin wani shahararren boka aina’u ta bata,dan haka ba b’ata lokaci suka isa gare shi dan neman taimako.
Cikin satin da ta fara amfani da k’walli da turare da boka ya bata Al’ammen ya furta mata kalaman so kuma yace da gaggawa yake son a d’aura musu aure.
Yanzu kullum shi yake kaita makaranta kuma ya dawo da ita gida da daddare kuma ya dawo suyi hira,takai ta kawo abincin dare ma agidansu yake ci wanda yasha surkullen boka.
Murna a wajan Hindatu da suke kira da mama ba magana ganin irin babban kamu da ‘yarta tayi,saboda har sunyi hannun riga da talauci tun kamin ayi aure dan kullum Al’ameen yana cikin jik’asu da naira.
Wata 2kacal akasa na bikinsu murna wajan Latifa ba zai fad’u ba ganin burinta ya kusan cika.
Ana saura 1month bikinsu yace ta shirya ya kaita ta gaishe da mamyn shi da matan yayun shi.
Mamy kwata-kwata Latifa bata kwanta mata ba saboda kana ganinta zaka san idonta a bud’e yake.daurewa tayi ta.karb’eta hannu 2. ya zatayi tunda zabin d’an autan tane.
Brothers d’inshi ma basuyi farin ciki da zab’in shi ba sai dai ba wanda ya nuna mishi a fili tunda Mamy ma batayi magana ba.
Sa’ad shine kad’ai ya fad’a masa abinda sauran ‘yan uwansu da mahaifiyarsu suka kasa fad’a mishi kuma a gaban Latifan ma ya fad’a saboda shi wani irin mutum ne mai wuyan sha’ani duk cikinsu ya fita daban,bai cika magana ba bare fara’a gashi da rashin shakka da tsoro in gasiyace ko ubanwa fad’awa yake.
Latifa hankalinta ya mugun tashi jin abinda Sa’ad d’in yace,taso yi masa rashin mutunci amma ganin yanayin shi kada’i yasa ta had’iye duk wani rashin mutuncinta.atake wani tsoronsa ya darsu a zuciyarta.
Ta d’an samu relief ganin Al’ameen bai kula da zancen d’an uwan nashi ba saima fushi da yayi suka bar gidan.
Ana saura 2weeks bikinsu yazo gidansu Latifa as usual suna hira yake ce mata baya son su sayi koda tsinke ne saboda ya gama tsara gidanshi ya zuba komai a ciki.
Cikin jin dad’i take kollon shi jin abinda yace tana yaba k’yau irn na Al’ameen gashi fari da dogon hanci sai dai bashi da manyan ido amma ya k’arawa fuskan shi k’yau gashi da pink lips,dogo ne shi mai faffad’an kirji.infact Al’ameen ya had’u over da ko wace mace zata so ta mallake shi.
Yayin da Latifa kuma ta kasance bat da wani k’yau saboda d’an hasken da take da shima na kanti ne,gata gajeruwa ga jiki.amma Al’ameen baya gani dan burin shi ya auri mace saliha dan samun zuri’a d’ayyiba kuma a ganin shi ya samu.
Kamin ya tafi 2millions ya damka mata wai na hidiman biki.
Kasa rutsawa sukayi ita da mama a wannan daren sai jujjuya kud’in suke cike da al’ajabi,ashe duk yanda suke jin labarin dukiyansu a gari ya wuce nan.
An daurauren su da Al’ameen an kashe kud’i anyi hidimomi da events na kece raini sai dai yawancin events d’in amaryace ta shirya su,wasu ango ya halarta wasu kuma bai je ba saboda shi baya son yawan hayaniya.
Danginta sai mamakin irin hidimomin suke saboda basu tab’a ganin biki makamancin sa ba,duk wanda yaga lefenta da kyar yake iya tashi wajan.ak’watuna set 2 aka had’a mata komai na ciki disiners ne masu tsada ga golds birjik kaman abin banza a ciki.
An gama hidiman biki lafiya ta tare a gidan mijinta wanda ya kasance kaman aljannan duniya dake unguwar dosa a cikin garin k.d
Babban burinsu ya cika ita da mahifiyarta na samun miji mai kud’i,tana abinda da taga dama da dukiyar mijinta ba mai taka mata biriki.
Matsala 1dake take fuskanta a gidan mijinta kuma yake gusar mata farin ciki a duk lokacin da ta tuna shine rashin haihuwa.