UKUBAR KISHIYATA 1-END

UKUBAR KISHIYATA Page 1 to 10

Shekararun su 7 da aure amma ko b’atan wata bata tab’a yi ba,gashi Al’ameen da hajiyarsa sun fara k’orafi akan rashin haihuwan nata.

Yasha ce su tafi asibiti ko kuma su fita outtside a duba lafiyarsu,amma sai tace mishi ai gaggawa aikin shid’an ne kuma komai na Allah yana da lokacinsa kila lokacin da Allah ya nufa su samu d’ane baiyi ba.nan zatayi ta kawo masa zancen Allah da annabi har sai taga ya hak’ura take k’yale shi.

Bakomai yasa take haka sai dankar asirinta ya tonu,sabida ita kanta bata sanadadin cikin da ta zubar ba,ko cikin saurayinta Salees sau hudu tana zubarwa banda sauran samarinta.ita kanta tasan zube-zuben cikin da tayi yayi muhimmiyar bada gudumuwa a wajan hanata samun ciki a gidan mijinta.

✍✍✍✍✍✍✍✍✍✍✍✍

[3/24, 6:46 AM] Ummee Yusuf: . ????‍♀????‍♀????‍♀????‍♀????‍♀????‍♀

  *~UKUBAR KISHIYATA~*

????????????????????????

  ( its all about love and betrayal)

Story by *~UMMEE YUSUF~*

   (Maman Yusuf)

????*~FAGEN MARUBUTA WRITERS ASSOCIATION~*????

*Gidan zaman lafiya,aminci hadin kai da yardar juna insha Allah*????

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

*~ADDU’AR DA ZAKUYI A LOKACIN DA ZAKU SANYA SABBIN TUFAFI~*

اللَّهُـمَّ لَـكَ الْحَـمْـدُ أَنْـتَ كَسَـوْتَنِيهِ، أََسْأََلُـكَ مِنْ خَـيْرِهِ وَخَـيْرِ مَا صُنِعَ لَـهُ، وَأَعُوذُ بِكَ مِنْ شَـرِّهِ وَشَـرِّ مَـا صُنِعَ لَـهُ

*~Allaahumma lakal-hamdu ‘Anta kasawtaneehi, ‘as’aluka min khayrihi wa khayri maa suni’a lahu, wa ‘a’oothu bika min sharrihi wa sharri ma suni’a lahu.~*

*~O Allah, praise is to You. You have clothed me. I ask You for its goodness and the goodness of what it has been made for, and I seek Your protection from the evil of it and the evil of what it has been made for.~*

*~part three~*

Ringin d’in da wayarta ya fara shi ya dawo da ita daga dogon tunanin da ta lula.

Hannu tasa ta jawo wayan tana doka murmushi saboda ko bata kalli screen d’in wayan ba tasan mai kiranta domin ringing tone d’insa daban ne a wayarta.

Picking tayi tare da d’aura wayan a kunnenta tace ” honey na ya akayine?”

” Sunan ya fita daga bakin ki coz u dont have d right to call me with dis name,yau kwana nawa ko tex d’inki ban gani ba bare call”.taji ya amsa mata a d’an fusace.

Make murya tayi tace ” oh! Salees darling am sorry ,wallahi zirga-zirgane suka min yawa”.

” nasan ni kad’ai nake haukana tunda gashi kin kasa cika min alkawari da kika min”.

Cikin tsigan lallashi tace ” ina sane wallahi kayi hak’uri ka k’ara min kwana 2.in banyi maka ba wa zanyiwa honey?”

Ajiyan zuciya ya sauke irin na ya samu relief sannan yace ” hmmm kin iya dad’in baki bayan kin san nayi missin d’inki sosai yauahe rabon da inji d’umin jikinki?”

Wani irin mik’a tayi akan gadon kana ta amsa da cewa ” my Salees u knw i miss u 2,saboda kai na daban ne a rayuwata”.

Cikin jin dad’i yace ” toh ya anjima zamuyi video call ko zan d’an rage zafi?”

Tana murmushi tace ” in dan wannane kasan baka da matsala all my time is urs.sai anjima”.

Katse kiran tayi ba tare da ta jira amsan shi ba.

Tana shirin ajiye wayan kiran Al’ameen na shigowa,sai da ta d’an ja tsaki tukun ta d’auka tare da cewa ” my ameen”

Daga d’ayan b’angaren kuma Al’ameen yace ” haba Latifa ya kika shige d’aki kika barni,abincin ma sai na rok’a sannan za ‘a bani kuma keda wa kike waya tundazu wayarki busy?”

A zuciyarta tace kaji dashi d’ansa ido.amma a zahiri kuma tace ” my Ameen mama ce ta k’irani amma gani nan zuwa”.tana fad’an haka ta mik’e tare da ajiye wayan ta fito main palour.

A kan dinning table ta hango shi ya zuba tagumi da hannaye 2 yana kallon yaran larabawa da suke ta wasa a tashan m.b.c3.

 Damuwa ce k’arara shimfid’e akan fuskanshi saboda shi ya kasance mai matukar son yara.

Ta iso daf dashi ta tsaya amma baima san da mutum a kusa dashi ba saboda yayi zurfi a tunani.

Hannu tasa ta dafa kafad’an shi,ya juyo a d’an firgice yana kallonta,can ya d’an kak’alo murmushin yake yace ” har kin iso?”

Bata amsa ba sai zagayawa da tayi taja kujera dake opp da nashi ta zauna ta zuba mishi ido for some seconds sannan tace ” nasan kana cikin damuwa mijina kaman yanda nake ciki nima koma ince nama fika shiga damuwa saboda ni mace ce.amma ina so kasani cewa komai yayi farko toh tabbas zaiyi karshe,saboda kullum cikin fad’awa mahallincin mu muke nasan ba zai barmu haka ba,dan ma bana fad’a maka yanda nake tsayuwar dare saboda wannan babban bukatar namu,ga malamai da nake basu abin sadaka suna taimaka mana da addu’a.ina son ka kwantar da hankalinka insha Allah komai zai zo da sauki.haba my Ameen  kai da kake namiji ma kana haka ni kuma inyi yaya kenan?”tace tana mishi murmushi.

Ajiyar zuciya yayi sannan yakamo hannunta na dama yana murzawa a hankali.fuskarsa d’auke da tsadaden murmushinsa dake k’ara fito da aininhin k’yan sa yace ” shiyasa nake godewa Allah daya bani mata saliha mai kwantar min da hankali a duk lokacin da nake cikin damuwa,dan haka bana k’yashin baki komai nawa dan nasan a hanya mai k’yau zaki sarrafa su”.

Murmushin jin dad’in yanda mijinta ya yarda da ita ta saki sannan tace ” toh ya isa haka ranka ya dad’e,irin wannan yabon ai sai kasa kaina ya fashe.bari in baka abinci kaci ko?”

Gyada mata kai yayi still yana murmushi.

Warmers d’in ta fara bubbud’ewa tace ” me zan zuba maka ur highness?”

” Duk abinda kika zuba min zanci”.yace yana kallonta.

Plate ta d’auko ta zuba rice nd stew da yaji naman rago zallah sai peppe soup d’in kayan ciki ta turagaban shi tace ” Bismillah”.

Cin abincin ya fara suna hira sama-sama har ya gama ya kora da ruwa sannan suka dawo palour suka zauna kallo tare da canza channel zuwa al’jazeera news har zuwa karfe goma da rabi na dare snnan suka koma up stairs part d’in Al’ameen .

Suna shigowa bedroom d’in bai tasaya wata-wata ba ya fad’a bathroom yayi wanka,yana fitowa Latifa ma ta shiga wankan kamin ta fito har yayi shirin bacci cikin kayan baccinsa dark blue masu taushin gaske.

Yana kwance akan gado ta fito,akan idonshi ta shirya cikin wata arniyan night wear, yana kallonta yana had’iyan yawu.

Yamutsa fuska ta fara tana wash-wash,bayan ta gama fesa turarukan ta masu kamshi yana kallonta amma takaici ya hana ya tanka mata mata ba.

Ganin ba zai kulata ba yasa tace  ” my Ameen wallahi wani irin ciwon kai nake ji kuma gashi ina son yin nafilfilu cikin dare”.

“Uhum…” yace yana kallonta.

” Zan je insha magani in d’an kwanta kamin lokaci yayi” tace tana wani dafe goshi.

” Toh “kawai yace mata tare da juya mata baya.

Yana jinta ta bud’e k’ofa tayi ficewarta ba tare da damuwa da halin da ya shiga ba.

 Yana jin ta rufo mishi k’ofa,ya juyo yana kallon k’ofan cike da takaicin hali irin na Latifa da kullum bata tashi rashin lafiya ko ibadarta sai sai sun zo kwanciya,a ko wani lokaci da abinda za ta kirkiro dan karma ya nemi wani abu a wajanta.in har ta yarda suka kwana waje d’aya toh fa lalle tana da wata tana da wata muhimmiyar bukatarta a wajan shi.

Tana zuwa part d’inta ta kulle k’ofa harda murza key.

Wayanta ta dauko ta kira Salees,video call suka fara, tana kwance akan gado ba sutura a jikint shima haka sai maganan batsa suke yana cewa  shafa min nan murza min can.wai duk su a dole zasu biya bukatar su a haka.kuma shaid’an ya basu sa’a abinda suke nema,su basu kwanta sai wajan karfe ukun dare sannan suka.( WA’IYAZUBILLAH)

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button