UKUBAR KISHIYATA Page 1 to 10

” ku shigo ta baya-ta baya..”suka kara jin tsawan sai dai wannan yafi na d’azun.
Kamo hannun Aina’u Latifa tayi ta rik’e gam sabida tsoro sannan suka fara tafiya ta bayan kaman yanda aka umarce su.
Suna dab da shiga cikin bukkan suka ji muryan d’an k’aramin yaro yana cewa ” wayyo zasu taka ni umma” .
Nan suka suka tsaya kaman an dasa suJikin sune ya fara b’ari barin ma da boka yace kan d’an autan aljani tsibiritu suka kusan takawa.Latifa kam ji take kaman ta saki fitsari a wando .
” ku shigo”aka ace musu.
Da kyar suka cigaba da tafiya ta bayan har suka shiga cikin bukkan da duhu ya mamaye kaman dare,wani haske ne ya fito cikin wani jan k’warya ya haska cikin bukkan kuma sai a lokacin boka ya bayyana a gaban su cikin wasu kaya ja-jaye ga rabin fuskarsa ma ta sha fenti ja.cikin babban murya yace su zauna.
Zama sukayi a inda ya nuna masu har yanzu Latifa tana rik’e da hannun Aina’u gam.
Aina’u ita tayi karfin halin bud’e baki da niyan yiwa boka bayani amma ya dakatar da ita ta hanyan d’aga mata hannu.
Shiru sukayi suna kallonsa yana ta wasu surkullen sa can ya d’ago kai yana kallon Latifa yace” tsibiritu da maniru su fad’a abinda yake tafe dake,kina so a rufe bakin mijinki dana dangin shi akan rashin haihuwarki kuma a kawar da idon shi akan ko wace mace ko ba haka bane?”
Cikin jin dad’in hango nasara tace “hakane boka”
Dariya ya kwashe da shi sannan kuma ya turbune fuska a lakaci1 yace “aikin ki mai sauk’i ne in kika kawo kitsen bakin jaki da makahon bunsuru da sauro mai ido 1shiken nan sai yanda kikayi dasu ”
Zaro ido waje Latifa tayi cikin tashin hankali tana kallon Aina’u bakinta yana shaking jin abubuwan da ya kirga a ina zata same su?
Aina’u ce ta d’an gyra zama tace ” ayi mana afuwa boka irinn wannan abu ai sai ku,zamu bada kud’i a taimaka a nemo mana”.
Wasu surutai ya fara da wani yare yana kallon sama can ya dawo da kanshi kasa yace ” tsibiritu ya yarda zai taimake ku sai ku ajiye kud’in acan ya nuna musu wata b’akar k’warya,belt d’in yan dubu guda 2 ta fito dasu hannu na karkarwa ta jefa a ciki nan da nan kud’insukak bace bat.
“Aikin ki ya kammala sai dai akwai wani d’an uwan mijinki kiyi hankali dashi zai iya b’ata miki aiki a ko wani lokaci”.boka yace ba tare da ya kalle su ba.
Zatayi magan Aina’u taja hannunta suka fita daga cikin bukkan.
✍✍✍✍✍✍✍✍✍✍✍✍
[3/24, 6:47 AM] Ummee Yusuf: . ????♀????♀????♀????♀????♀????♀
*~UKUBAR KISHIYATA~*
????????????????????????
( its all about love and betrayal)
Story by *~UMMEE YUSUF~*
(Maman Yusuf)
????*~FAGEN MARUBUTA WRITERS ASSOCIATION~*????
*Gidan zaman lafiya,aminci hadin kai da yardar juna insha Allah*????
*~part five~*
Aina’u bata saki hannun Latifa ba sai ďa suka zo har inda suka ajiye mota,bude motan tayi ta tura ta a ciki san an itama ta zagayo ta bude tashiga gidan gaba.
Latifa d’aura kanta tayi a kan stairyn motan ta sauk’e ajiyan zuciya.
Juyo da kanta tayi saitin Aina’u tace ” kin san Allah badan kina tare da ni a wajan nan ba,da abinda zai hani sake gudawa a jikina”.
Aina’u ta tuntsire da dariya saida tayi mai isar ta sannan tace ” matsoraciya kawai harda gudawa hahaha” tacigaba da dariyanta.
Had’e rai katifa tayi tana kallon yanda ta dage tana mata dariya tace ” wats funny here, da zaki wani dage kina dariya haka?yauwa meyasa kika hana ni magana bayan kina ji yace akwai d’an uwan my Ameen da zai iya rusa min duk aikina.da kin bari ko sunan shi na tambaya”.
Aina’u tace ” kada ki soma wanman gangancin saboda boka nan ba’a yi masa musu kuma ba’a wucewa gaban shi.kinga da yana so ki sani da kan shi zai miki bayani”.
Key tayiwa motan suka fara tafiya tace ” oh god ya zanyi ne?”
“Abinda zakiyi kawai kiyi taka tsan-tsan da’yan uwansa”Aina’u ta bata amsa.
Shawara yanda zatayi da ‘yan uwan Al’ameen Aina’u take bata har suka shigo garin k.d,direct gidan su Aina’u tayi dake kawo a bakin k’ofan wani yamutsesen gida tayi parking.
Hand bag d’inta ta bud’e ta ciro bounch 200 guda1 ta mik’awa Aina’u tace ” ga wannan ki rik’e ba yawa besty nagode sosai”.
Karb’a Aina’u tayi tana mata godiya tace “baza ki shigo ku gaisa da umma ba ?”
Gurgiza kai Latifa tayi a zuciyarta tana ina zataiya shiga gidan nan amma a zahiri kuma tace ” no besty kinga yamma tayi sosai yanzu kila ma my Ameeen ya dawo,soo gwara na karasa ki gaishe min da ita.sai next time in nazo zan shigo mu gaisa”.
Murmushi Aina’u tayi tace” shikenan sai munyi waya “daga nan ta bud’e motan ta fita Latifa taja tayi gaba abinta.
Burinta na karshe ya cika dan yanzu duk cikin dangin mijinta ba mai yi nata maganan rashin haifuwa balle kuma shi uban gayyan wato Al’ ameen ya zama rakumi da alaka sai yanda tayi dashi dan duk wani documents da files dinshi masu amfani da mahimmaci a hannunta suke tana wandaka da dukiyarsa yanda taga dama.
Yanzu abin nata yayi gaba saboda boka ya bata sa’a har cikin gidan wasu samarin nata suke biyota a sunan yan uwanta dan haka gidan kullum a cike yake suna shagalinsu.
Fa’iza da shamsiya suma abin nasu yayi nisa dan suma kullum cikin kawo kawaye suke, su shige bangaren su,tare da saka key suyi abinda suka ga dama, cikin haka suka samu wata da ake kira Binta wacce jarabarsu tazo iri daya dana su fa’iza dan haka yawanci tana gidan su kwana tare su tafi makaranta tare.
Kaman kullum yauma Al’ameen ya dawo daga office ya tarar da latifa da salees da wani abokinshi suna hiran su hankali kwance a waiting palour.
Sallama yayi ya shigo, tashi Latifa tayi da saurita, ta taro shi tare da karban jakan hannunshi tana mishi sannu da dawowa ya amsa cikin sakin fuska,su salees ma suka gaishe shi ya amsa sannan suka wuce bangaren shi tare da ita.
Bayan ta taya shi cire kayan jikn shi ta hada masa ruwan wanka sannan ta fito tace”ruwanka na jiranka my Ameen ”
Murmushi yayi ya mike zuwa bathroom.
Ganin haka tace”bari inje in had’a maka abincinka kafin ka fito ko?”
du
“duk yanda kikayi gimbiya dai daine”.
Wuce shi tayi tana dariya,yayin da shi kuma ya k’arasa shiga bathroom d’in.
Direct wajansu salees ta dawo tazo ta rungume shi sannan tace” yanzu ku tafi sai munyi waya zaka ji komai zan san dai yanda zanyi yayi signing dinsu karkaji komai”.
Manna mata kiss yayi a kumatu yace ” nasan zaki iya babyna, sai naji ki”.
Fitowa sukayi ya d’auki motan shi da latifa ta saya mishi suka fita daga gidan.
Latifa dawowa tayi palour na biyu tare da duba kan dining taga an shirya komai,neman guri tayi ta zauna tana jiran fitowan shi.
Sanye da kananan kaya wanda suka yi matukar karb’an shi ya fito ya zauna a d’aya daga kujerun dining.
Plate ta jawo ta fara serving d’in shi, cus cus ce da miyar ganye tasha tsokar kaji har ta gaji.
Fara ci yayi hankali kaman wanda baya son cin abincin.
Gyara zama Latifa tayi tace ” my Ameen na nayi maka maganan kwangila nan amma har yanzu bakayi magana ba,kasan k’anne na maza ‘ya’yan yayan baban mu basu da aikinyi shiyasa nake son taimaka musu da abinyi”.
yana kallon ta yana tauna abincin dake bakin shi cikin natsuwa sannan yace ” aina gaya miki duk wani abu inza kiyi na taimako ba sai kin tambayeni ba dan nasanki ta hanya mai kyau zaki sarrafa su”.
Tayi yar dariya tace “toh wannan d’in yana bukatan sa hannunka shiyasa”.