UKUBAR KISHIYATA Page 1 to 10

“Ok d’auko mana insa hannun”.
Mik’ewa tayi ta shiga part d’inta,sai gata ta fito da files a hannu.
Batare da ya karantaba ya rantama hannu ya mik’a mata
Karb’a tayi cike da jin dad’i saboda kwangila ce har ta million ashirin.
Tashi tayi da saurita tayi d’akinta ta kira salees a lokacin yana wani hotel da wata karuwan shi suna holewan su.
Ya d’auka yace “ina jinki a akayine”?
Cike da farin ciki tace” my dear ya saka hannu ga files d’in a hannuna gobe aina zan sameka?”
Yace inda muka saba had’uwa mana ko kin saki d’akin ne?”
Tace ” na isa in saki d’akin? suma ‘yan hotel d’in ganin na mak’alewa d’akin har kara min kud’i sukayi”
Yace “amma ai nasan kud’i ba matsalarki bace ko”?
Tace”kaima kasan da hakan just sai mun had’u goben”
“To bye my heartbeat”.
Fitowa tayi bayan sun gama wayan.Al’ ameen yana zauna yana kallon bbc news
Zama tayi kusa dashi suna hira sai fara’a take kaman ba ita ba.
Yau dai yayi sa’a albarkacin signing d’in da yayi yau,da kanta ta kawo kanta.
Gaba d’aya ya rikice ce jikin shi har b’ari yake saboda rabansa da ita ya kai sati 2,dan haka kusan raba dare yayi yana abu d’aya sannan ya samu natsuwa.ranan dai ya samu bacci mai dad’i.
[3/24, 6:47 AM] Ummee Yusuf: . ????♀????♀????♀????♀????♀????♀
*~UKUBAR KISHIYATA~*
????????????????????????
( its all about love and betrayal)
Story by *~UMMEE YUSUF~*
(Maman Yusuf)
????*~FAGEN MARUBUTA WRITERS ASSOCIATION~*????
*Gidan zaman lafiya,aminci hadin kai da yardar juna insha Allah*????
*~part SIX~*
Da washe gari Al’ameen da wuri ya shirya ya fita office.
Fitowa tayi cikin shirin fita da wasu english wears matsassu riga da skirt har shatin pant d’inta ana gani,ba bata lokaci ta ja mota sai prince hotel.
Reception ta nufa bayan tayi parking,ma’akatan hotel d’in suna ganinta fara well come Hajiya.
Duk wani ma’aikacin hotel d’in sun santa saboda regular customer ce.
Bata damu da kama room daban daban ba tunda ta kama room number 35, shikenan ta makale mishi.
Duk ranan da taso holewa sai dai tazo ta karbi mukulli ta wuce kuma ga kyautan kud’i da take musu shiyasa suke bala’in girmamata.
Dan haka yauma suna ganinta suka hau murna,bayan sun gaisa aka miko mata key ta fito da bounch d’in ‘yan d’ari biyar ta basu su raba, suka karb’a tare da godiya ta wuce d’akin bayan ta rufe ta rage kayan jikinta daga ita sai karamar vest skirt, ta kwanta akan gado tana kiran wayan Salees.
Yana d’aka wayar yace mata gashi nan ya shigo compound d’in hotel.
Tana ajiye wayan kaman da 10 mins sai gashi nan da kwalban wine a hannunshi ya shigo ya maida k’ofar ya rufe.
Bata motsa ba daga kwanciyar da tayi ba yana kallonta da irin kallon daya saba yi mata na zallan so.
Ya zauna dab da ita yace”ya dai babyna ya na ganki haka?”
Kamo hannun shi tayi da karfi ta jawo shi ya fad’a kanta suka rungume juna suna ta juyi akan gadon tace”kasan nayi missing d’inka sosai”.
Tashi yayi ya zauna tare da d’ago ta itama ta zauna sannan ya bud’e kwalban wine ya fara sha.
Ya sha kusan rabi sannan ya mik’o mata itama ta karb’a ta sha sosai dan ta kwana biyu bata sha ba.
Ahaka har suka shanye gaba d’aya suka koma suka kwanta suka cigaba da sheke ayansu san ransu.
Bayan sun natsu,ta bud’e hand bag ta fito da files d’in ta mika mishi tace”ina so mufara business dashi dan kud’in suyi albarka saboda haka na mika maka wuka da nama sai yanda kayi”.
Yaca”karki damu zanyi duk iya kokarina dan muyi nasara kaman yanda kema kikayi naki kokarin”. Yace yana jujjuya file di’n a hannun sa.
Sai kusa la’asar suka rabu ta wuce gida. shima ya wuce inda ya fito.
A kwana a tashi ba wuya a gurin Allah,dan yanzu Latifa sun shiga 12years of marrage amma ba wanda ya k’ara takura mata akan haihuwa.tana abinda taga dama.
Hajiya Halima wato mahaifiyar su Al’ameen ta shigo palour d’auke da karamin tray ta d’aura bottle water da glass cups 2 akai.
Ajiye trayn tayi akan wani d’an karamin table na glass a gaban mijinta wato Alhaji mudassir.
Bud’e ruwan tayi tare da zubawa a glass cup d’in ta mik’a mishi sannan ta nemi waje ta zauna kusa da shi.
Ajiye cup d’in yayi bayan ya shanye ruwan,ya juyo yana kallonta yace ” dazu munyi waya da Hajiyar katsina tace gobe zasu shigo ita da ‘yar wajan Laure Sakeena”.
Hajiya cikin farin ciki tace Allah sarki ashe gobe muna da manyan baki,bari mu fara shirin tabarsu tun yanzu”.
Dariya Alhaji yayi cikin jin dad’in yanda matar shi take karrama mishi dangi a koda yaushe.
Da safe tunda wuri hajiya tasa aka gyra d’akin da surkuwar ta zata sauka ga kuma girke-girke da sukayi na musamman aka jera su kan din ing ana jiran zuwansu.
3:00pm su Hajiyan katsina suka isohajiya ta karb’e su kamn yanda ta saba yi,
Bayan sun ci sun sha kuma sun huta aka zauna hira a palour.
” wai ina angwayen nawa ne banga ko d’aya ba ko kishiyoyin nawa ne suka rik’e su?”cewar hajiyar katsina.
Hajiyar su Al’ameen tayi dariya tace ” aiko sun rike su dole su kyale tunda uwar gida ta zo”.
Alhaji yana murmushi yace Sakeena ya wajan ummanki da sauran kannenki?”
Yarinyan da aka kira da Sakeena ta sauke kai k’asa tace duk suna gaishe ku”.
” muna amsawa ” hajiya tace tana shafa kanta.
Alhaji ya ciro waya ya fara kiran boyz dinsa ya sanar dasu zuwan Hajiyar katsina.
Bayan ya gama kiransu ne Hajiyar katsina tace ya labarin matar Aminu har yanzu shiru ko?”
Hajjiya ta amsa mata ” eh har yanzu lokaci baiyi ba”.
Tab’e baki hajiyar katsina tayi tace ” hmm gobe yazo ya same ni musan abinyi tunda kun kasa nema masa mafita”.
Next day saturday ba aiki saboda haka Al’ameen yana gida.
Suna zaune tare da Latifa yake gaya mata zai je can gidansu gaishe da Hajiyar katsina da tazo jiya.
Yamutsa fuska tayi ba tare da ta kalle shi ba tace ” noo my Ameen yau fa weekend ne ya kamata ka zauna ka huta a gida dan bana son ka wahala”.
” alright ” yace kawai suka rufe zancen but kasan zuciyar shi ba haka yaso ba,yana son zuwa su gaisa dan ya dad’e bai sata a ido ba.amma ya rasa dalilin da yasa baya iya mata musu.
Ita kuma Latifa tun lolacin da boka yace mata a cikin ‘yan uwansa akwai wanda zai lalata mata sihiri take taka tsan-tsan da al’amuransa ta hana shi shiga cikin ‘yan uwansa.
” let me take a shower ” tace tare d wucewa part d’inta.
Tana shiga bedroom wayarta ya fara ringin kuma ringin tone d’in salees ne.
Tana d’agawa tace ” my only love”.
” i need u right now coz i missed u alot hak’uri na ya kare kizo mu had’u” salees yace.
” but salees i have an important thing to do at home ”
” Bana son jin komai wato am not importan to u ” yace cikin fushi.
Jin muryan shi da alamun fushi yasa tace ” pls come down Salees ba haka nake nufi bayi hak’uri gani nan zuwa”.
” better ” yace yayi hanging call d’in.
Bata son fita yau tafi son ta zauna a gida tayi gadin Al’ameen amma bata son bacin ran salees dan haka tashi tayi ta fad’a bathroom dan yin wanka.
Bayan ta fito daga wanka ta sheka kwalliya da wani leshi maroon d’inkin dogowar riga sai kamshi turare take, ta iske shi a inda ta barshi yana zaune, ta zauna kusa dashi ya juyo yana kallonta dan taci ado harna fitan hankali tace”my meen kun dade baku had’u dasu hajjiyar katsina bako?”
Ta sosa mishi inda yake mishi kaikayi yace”ai shekarune ma zance”