UKUBAR KISHIYATA Page 1 to 10

Tace”hmm shikenan kaje ku gaisa,nima zaje gidan mama in dawo”
Ya kama washe baki yace”toh shikenan ki gaida ta nima ba d’ad’ewa zanyi ba ke sai yaushe?”
Tace”my meen kenan zaria fa zanje kaga kuma na d’ade banje ba ina ga sai kusan magrib zan dawo”.
” sai kin dawo,” yace tare da mikewa yayi part d’in shi .ya shirya cikin manyan kaya na shadda dark green ya sha bugu sai maik’o yake.
Shi kad’ai ya d’auki mota ya fita,bai nemi drivern shi ba.
Direct gidansu dake unguwar rimi ya nufa,yana zuwa mai gadi ya bude mishi gate ya shiga.
A parking space yaga motocin brodthers d’in shi dan haka shima cikin farin ciki ya nufi palour.
Tun daga bakin k’ofa ya fara jin muryoyinsu anata hira da raha,sallama yayi suka juyo gaba 1 su suka amsa ya nemi guri kusa da kkafar hajiyar shi ya zauna.
[3/24, 6:47 AM] Ummee Yusuf: . ????♀????♀????♀????♀????♀????♀
*~UKUBAR KISHIYATA~*
????????????????????????
( its all about love and betrayal)
Story by *~UMMEE YUSUF~*
(Maman Yusuf)
????*~FAGEN MARUBUTA WRITERS ASSOCIATION~*????
*Gidsn zaman lafiya,aminci hadin kai da yardar juna insha Allah*????
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~ADDU’AR DA ZAKUYI A LOKACIN DA ZAKU BAR GIDANKU~*
بِسْمِ اللَّهِ تَوَكَّلْـتُ عَلَى اللَّهِ، وَلاَ حَوْلَ وَلاَ قُـوَّةَ إِلاَّ بِاللَّهِ
~Bismillaahi, tawakkaltu ‘alallaahi, wa laa hawla wa laa quwwata ‘ illaa billaah.~
*~In the Name of Allah, I have placed my trust in Allah, there is no might and no power except by Allah.~*
*Part seven*
Gaishe da Hajiyar katsina ya farayi sannan ya gaishe da iyayensa da brothers d’in shi tare da matansu.
Bayan gaisawan ne ya d’auki babyn yayan shi Sa’ad wanda bai wuce 6months ba yana masa wasa.
Hajiyar katsina ce take tambayarsa ina Latifa me ya hana ta zuwa su gaisa ko taji tsoron uwar gida ne?
Dariya yayi yace ” a’a ba ko mzaria 1ta tafi dubo mamrta bata jin dad’i”.
Allah ya suwak’a kowa ya mata sannan suka cigaba da hiran su cikin raha da zolayan juna.
Ganin yanda Al’ameen hankalkn shi ya tafi kan affan yana ta mishi wasa yasa Hajiyar katsina magana tace ” kai k Ameenu matarka har yanzu ba labari ko?”
Bai tsaya da wasan ba yace mata ” eh Hajiya lokaci baiyi ba kinsan komai lokaci ne”.
Hajiyar su itama tace ” haka ne komai lokaci ne”.
Shiru hajiyar katsina tayi na d’an lokaci kana tace ” toh me zai hana ka kara aure ko rabo ‘yar uwarta ce ya danne nata kadan hakan yana faruwa”.
Al’meen gumi ne ya fara karyo mishi ta kowane hujin gashin jikinsa.ga wani irin damuwa da tashin hankali da suka bayyana karara akan fuskan shi lokaci guda.
Hajiyar katsina ce ta lura da halin da ya ahiga tace “mai gidan lafiya kuwa daga maganan aure sai ka birkice haka?”
Share gumin da ya tsatsofo mishi a goshi yayi sannan yace ” gaskiya a bar maganan dan ni ba wani aure da zan iya k’arawa.haihuwa ài na Allah ne,a yanda muka dage da addu’a nasan Allah zai share mana hawaye lokaci ne bAiyiba”.
Rik’e baki Hajiyar katsina tayi tana kallon shi a matukar mamakince can dai ta daure tace ” dan nace ka kara aure shine kake min suratan banza,ni zaka gayawa Allah?toh tun kafin a haifi ubanka nadan Allah.in yarinyar da zaka aura ne baka samu ba sai ka duba nan cikin ‘yan uwa ka aura”
Cikin firgici yake kallonta yama rasa me zaice mata,yana zaman-zamansa zata zo taja mishi bala’i dan in Latifa taji zancen nan ya shiga 9 ba 3 ba.
Alhaji ya kalla yace “,dan Allah ku fahimtar da ita ta rufa min asiri ni ban tashi aure ba.pls leave me alone”.
Hajiyar katsina ta kasa magana saima hangame baki da tayi tana kallon ‘yan palourn duka saboda bata ga wanda ya d’auki maganan serious ba saima ce mata da sukayi ta bar maganan tunda bai tashi auren ba.
Sa’ad ne kad’ai yayi shiru bai tanka ba sai da suka gama magana sannan ya bud’i baki ya cewa Hajiyar katsina ” karki damu zamu tafi gidana dashi zansa shi ya fahimta”.
” Oh ni ‘yasu yau naga abinda yafi karfina”.inji Hajiyar katsina tana girgiza kai cikin jimami dan tabbas taga alamu ‘yan gidan ba cikin haiyacinsu suke ba.
Hankalinta bai kwanta ba saida suka keb’e da Sa’ad ya fad’a mata abinda yake ranshi.nan itama tace ba Al’ameen kad’ai abin ya shafa ba harda sauran ‘yan uwansa da iyayensu.
Fita Sa’ad yayi bayan sallahn azahar,sai kusan la’asar ya dawo da wani jerry can cike da ruwan addu’a da yasha ganyen magarya.
Tambayansa Alhajinsu yayi z ruwan menene wannan?”
” Ruwan addu’ace ta kariya na kawo dukkan mu muyi amfani dashi”.ya amsa mishi a ladabce.
Ba b’ata lokaci mai aiki ta kawo cups,duk suka sha sannan yace musu ” mallam yace kullum zamu rinka sha har zuwa 7days dan haka daga yau duk wanda ya tashi tafiya office ya biyo yasha kafin ya wuce”.
Yayi hakan ne sabida shi tun kamin aurensu shi bai yarda da Latifa ba,bare ma da yaga yanda kaninshi ya birkice lokacin da yaji maganan aure,bayan b4 yayi aure bashi da wani buri da ya wuce ace yayi aure ya tara ya yara amma yanzu ko zancen baya so.
Ga Ahajin su yasan halin shi yana d’an zafi wani lokacin gashi yau Al’ameen yana fad’awa Hajiyarsa magana amma ko kallon banza bai mishi ba ga Hajiyarsu itama a baya bata da buri da ya wuce taga jinin autanta,sai gashi itama ta canza.
Addu’ansa 1ce Allah yada duk wani surkullen da tayi ya warware albarcin wannan addu’an.
Da daddare da zasu rabu sauda yajawa Al’ameen kunne kan yaja bakin shi kar ya bawa Latifa labarin ruwan addu’an da zasu rinka zuwa sha kullum.
Yau kwana uku kenan kullum Al’ameen da safe sai yaje yasha ruwan add’ua sannan ya wuce office.
Da wuri yau ya tashi a office ya dawo gida asual ya tarar da gidan cike da samari da ‘yan mata da samari ana ta hira,a karo na farko da yaji ba dad’i a zuciyarshi amma ya danne bai nuna ba ya wuce ciki bayan yayi wanka ya zauna ya fara aiki a system d’in shi.
Haka kawai ya rinka jin shi wani iri yau.
Latifa ce ta shigo ta zauna kusa dashi tace ” my ameen lafiya yau baka sauko kasa ba?”
” Lafiya lau ina wasu aiyuka ne shiyasa”.yace mata.
Kallonsa tayi tace ” abincin fa ?”
Yace ” naci a gidan ya Sa’ad kamin inzo”.
Shiru tayi tana mamakin yaushe har ya far zuwa gidan wasu ba tare daya gaya mata ba?
Kawar da zancen tayi a ranta tace ” toh ni zan sauka kasa sai ka fito”.
” Toh ” kawai yace ba tare da ya dube ta ba ya cigaba da aikinsa.
Saukowa tayi ta kyale shi.
Yau friday kuma yaune kwana 5 da fara shan ruwan addu’an,yana zuwa ya tarar da duk brodas dinsa suma sun zo.
Bayan sun gaisa kuma sunyi abinda ya kawo su Ai’ameen yace ” nifa Hajiya na kasa gane me Latifa take nufi dani,ta mayar min da kaman wani bariki kullum cikin tara min mutane take baya ga haka rabin danginta a.gidan suka tare”.
“Hajiya tayi caraf tace ” wannan shashanci ne bangane rabin dangin taba”.
Alhaji yace ”
Wanna ai zancen banza ne kuma laifinka ne kai ka sake mata”
Murmushi mai kayatarwa Sa’ad yayi tare da cewa “ALHAMDULLILAH Ala kulli halin”.
Alhaji ne ya kalle shi yace ” d’an uwanka yana cikin matsala abinda zaka ce kenan?”
” ba haka nake nufi ba”yace
” Toh me kake nufi?” Hajiya ta katse shi.
Nan ya kwashe komai ya fad’a musu sannan yace ” Alhamdullih sauki ya samu tunda har ka fara ganin laifinta saidai abinda nake so da kai ka bar maganan a zuciyarka ka cigaba da pretending har yanzu asirin bai bar ka ba dan bamu san iya lokacin da ta d’eba tana aikatawa ba in ba haka kayi ba ba zamu samu bakin zaren ba.