UKUBAR KISHIYATA Page 1 to 10

Cikeda takaici Al’ameen ya fara magana yace ” wallahi bazanyi shiru ba yanzu zanje in nuna mata bokanta yayi kad’an dan bazata kwana min a gida ba.
Alhaji ne ya shiga tausan shi akan Sa’ad yana da gaskiya abi komai a sannu.
Kowa yayi na’am da shawaran Sa’ad tare da add’uan Allah ya tsare gaba.
Haka ya wuce office cikin k’unan rai tare da tsanan Latifa a ran shi.
[3/24, 6:47 AM] Ummee Yusuf: . ????♀????♀????♀????♀????♀????♀
*~UKUBAR KISHIYATA~*
????????????????????????
( its all about love and betrayal)
Story by *~UMMEE YUSUF~*
(Maman Yusuf)
????*~FAGEN MARUBUTA WRITERS ASSOCIATION~*????
*Gidsn zaman lafiya,aminci hadin kai da yardar juna insha Allah*????
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
Alhmdllh mama ta samu lafiya ina mika godiyata gare ku my fans kan addu’oin ku Allah ya bar kauna????????
*~part eight~*
Al’ameen yan zuwa office ya samu mutane da yawa masu son ganin shi ga aiki sun taru sunyi yawa,dan haka sake ranshi yayi ya cigaba da harkokin shi hankali kwance.
Bayan sati Sa’ad yaje har company Al’ameen inda tace yazo ya raka shi unguwa,barin aikin shi Al’smeen yayi ya bishi suka fita su 2 a motan Sa’ad.
A sabon gari gidan mallam nuhu yake,a kofar gidan Sa’ad ya tsaya suka shiga ciki wajan mallam.
Yana kishingid’e a palourn shi sukayi sallama,daga ciki mallam ya amsa ya basu izin shigowa.
Zubewa sukayi gaba 1suka kwashi gaisuwa a wajan mallam sannan Sa’ad ya nuna Al’ameen yace ga kanin shi da ya kab’awa magani kwanaki kuma Alhmdllh sauki ya samu shine suka zo godiya.
Gyran murya mallam yayi sannan ya tashi zaune shima yayiwa Allah godiya tare da basu wasu addu’oi da zasu rik’e saboda kariya.kuma yace kar suyi wasa da azkar na safe rana dare shima in mutum ya rik’e babban kariyace.
Godiya suka karayi mishi sannan suka bashi abin sadaka suka fito.
Yau Al’ameen ya dawo daga aiki da wuri,ya tarar da Latifa suna zaune a waiting palour tare da Salees da abokanen shi 2 suna hira.
Wani rirn bakin cikine ya tokare mishi zuciya.
Suna mishi sannu da zuwa amma ko kallonsu baiyi ba ya wuce part d’inshi a zuciye.
Zama yayi a bakin bed ya dafa kashi da hannaye 2,magana ya fara cikin bacin rai shi kaf’ai.
” i cant tolarete dis nonsence in my house,i have to do somting.wa yasan lokacin da ta d’auka ta tara min kartin banza a gida,sai kace ita kad’ai ce mai dangi……”
Ringing din wayarsa ce ta katse shi,ciro phone d’in yayi daga aljihu.sunan da ya gani yana yawo akan screen ya sa shi sauke ajiyan zuciya sannan yayi recieving.
” Salamu alaikum Hajiyata,barka da yamma”.
” Lafiya lau Al’ameen ya gida,ya naji muryanka wani iri hop dai kana lafiya?” Hajiya ta tambaye shi cikin kulawa.
Tana ji cikin wayan yana sauke ajiyar zuciya wato yana kokarin calming kansa yace ” Hajiya na gaji am fed about Latifa,gaskiya i cant take it any more.ace wai any time na shigo gida sai raina ya baci”.
” nasan akwai ciwo amma fa dole ne ka danne zuciyarka for some time muga abinda Allah zaiyi karka manta Alhajin kuma ya bada goyon baya kan hakan so pls ban yarda ka kula taba.zan samu Alhajin inji me ya kamata kayi next,kaji ko?” cewar Hajiya.
” naji kuma insha Allah zan kiyaye ” yace cikin sanyin murya.
” yauwa d’an albarka Allah ya tsare ka daga dukkan abin ki”.
” Ameen Hajiya nagode sai anjima” yace tare da ajiye wayan.
Latifa tana can wajan su Salees,Al’ameen yana shigewa ciki abokansa suka mike jiki na rawa akan suzo su wuce dan basu san hukuncin da d’auka ba akan su.
Salees ya kalle su ya murmushi yace ” kwantar dahankalin ku guys ba abinda zai faru”.
Latifa kuwa dariya take sosai harda rik’e ciki tace ” wai me ya tsorata ku haka?kun d’auka dan ya ganku ne yayi haka,ina ganin a office ne wani ya tab’a shi saboda haka kusha zaman ku”.
D’ayan hanyan waje yayi yace ” no lets get going tunda ya dawo,just kema ki bishi kar yayi suspecting wani abu”.
Salees mik’ewa yayi yace ” yeah hakane baby kije kawai mu zamu wuce sai munyi waya,but pls kisan yanda zakiyi yayi signig documents d’in”.
” dont worry kai ma kasan wannan yafi komai sauki ” tace tana tashi danyi masa good bye hug,a lokacin abokanen saless har sun tsufa a mota.
Da fara’anta ta shigo part d’in Al’ameen tana ” waue ya tab’a min my Ameen ne ya shigo ba fara’a haka?”
D’an murmushi ya kakalo yace ” bana jin dad’i ne kuma ga ciwon kai da nake ji”.
” eyyah sorry let me get u drugs cikin first aid box”.
Paracetamol ta ballo mishi guda 2 ta kawo had’e da bottle water.
Ba musu ya karba ya sha dan da gaske yake jin ciwon kan saboda bacin rai da suka saka shi.
Driving yake a hankali shi kad’ai a mota sakamakon ya aik8 drivern shi bai dawo da wuri ba,ya kama hanyan gida.
Yamma tayi lis a lokacin pass 5 ne,ya biyo ta tudun wada gun wani frnd d’insa da sukayi karatu tare a anguwan.
Kamin ya isa gidan abokin nashi ya hango wasu samari sun kai 6 sun sa wata yarinya a tsakiya,sai faman kuka ,rok’o da magiya take musu akan su bata hanya ta tafi amma sai wani dariyan mugunta suke mata.
Parking motan shi yayi ya fito ya nufi inda suke,a lokacin har har daya daga cikinsu ya kama hijabinta yana ja.
Uniform ne a jikinta na islamiya kuma hijabin har kasa.
Al’ameen yana zuwa yace musu ” ya dai,me ta muku ne haka?ku bata hanya ta wuce mana”.
1 ne ya juyo ya bashi amsa ga kayan maye a hannunsa yace ” kai dallah ina ruwanka damu,ko kanwarkace?”
” eh kanwata ce ku kyaleta ta wuce”
Wani d’an dogon cikin su yace” nd so wat in karwar kace,yau sai mun tafi da ita dan rainin wayon nata yayi yawa”.
Al’ameen ganin ba zasu saurare shi ba gashi kafa ya d’auke saboda irin tsukukun lungu ne.
Hannu yasa a aljihu ya kwaso duk kud’in dake ciki wanda shima baisan adadin suba ya mik’awa dogon yace ” ga wannan ku sha ruwa da shi pls ku kyaleta ta tafi”.
Kusan wawa suka dakawa hannun shi,suna ihun murna tare da jinjina mishi harda kirari.nan suka dubi yariyan da yanzu har ta durkushe a wajan tana kuka.
Wani mai katon kan cikin su yace mata ” ke wallahi kinci arzikin oga,badan shiba da yau sai kin yabawa aya zakinta.kuzo muje yau akwai hawa network dan yau ni service zan hauma ba network ba”.
Haka suka tafi suna ta iface-ifacen da suratansu har suka sha wani coner.
Al’ameeen zubawa yarinyan ido yayi for some seconds yajhna kallonta duk da ko tafin hannunta baya waje ko ina na jikinta a lullub’e suke sai shasshekar kukanta yake tashi.
Lumshe ido yayi ya bud’e yace ” meye ya had’aki da wa’yan kuma?”
Cikin kukan ta bashi amsa tace ” wallahi ban musu komai ba,sun ce in tsaya in saurare su dan…..da…..”kuka yaci karfinta ra kasa karasawa.
” ya isa haka tashi in karasa dake gida saboda kar in tafi su kara dawo kinsan wa’yan nan ba hankali ne dasu ba”.yace still idon shi kanta.
A sanyaye ta mik’e tsaye kanta a kas’a tana share hawaye,ganin haka shima ya juya ya nufi mota.
Bin bayansa tayi har zuwa inda yayi parking motan shi,bud’e mata front seat yayi ta shiga ta zauna.shima ya zagaya ya shiga yaja suka bar wajan.
Driving yake yana satan kallonta amma taki d’ago da kanta bare ya samu daman kallon fuskanta.
[3/24, 6:47 AM] Ummee Yusuf: . ????♀????♀????♀????♀????♀????♀
*~UKUBAR KISHIYATA~*
????????????????????????
( its all about love and betrayal)