UKUBAR KISHIYATA 1-END

UKUBAR KISHIYATA Page 1 to 10

Story by *~UMMEE YUSUF~*

   (Maman Yusuf)

✍✍✍✍✍✍✍

GOLDEN PEN WRITER’S ASSOCIATION

✍✍✍✍✍✍✍

*~part nine~*

Dai-dai wani rugujajjen tsohon gida tace ya tsaya,tsayawa yayi ya juyo gaba 1 ya zuba mata ido.

” Nagode Allah ya saka da alkhairi” tace a hankali kaman bata so kuma ba tare da ta d’ago ta kalle shi ba.

Kamin ya samu abin fad’a har ta bud’e murfin motan ta fita.

A sukuwane ya fito shima saboda yana da burin koda sunanta ne ya sani.

Wani wawan birik yaja ya tsaya ganin wani d’an dattijo ya fito daga gida da buta da tabarma a hannun shi.

D’an rusunawa tayi ta gaishe da tsohon sannan ta shige ciki, ganin yanayinta yasa tsohon kallon A’ameen cikin tuhuma yace ” bawan Allah meye had’inka da ‘yata har zaka d’auko ta a mota?”

Har kasa Al’ameen ya durkusa ya gaishe shi,a taikaice ya amsa yana jiran yaji amsan tambayan shi.

” Baba wallahi nima a hanya na samu wasu yara suna kokarin hi mata rashin mutunci,shine na tsaya na raba su kuma tsoron karsu k’ara biyota yasa na kawota gida”. Yace cikin ladabi.

” toh-toh madallah d’an samari Allah yayi albarka nagode kaji?”wannan tsohon yace masa cikin jin dad’i.

Sallama yayi masa sannan ya shiga motan shi yayi gaba.shi kuma wannan tsohon ya shimfid’a tabarman shi tare da fara alwala.

Da sallama ta shiga cikin gida Umma tana ganinta ta bar kwashe tuwo da take a bakin murhu tace ” AMIRA me ya same ki na ganki haka ga yanda idonki da fuakanki suka kumbura?”

Share gutun hawaye da ya gangaro mata tayi sannan tace ” wallahi Umma wasu ne ina dawowa a hanya dan sunyi min magana naki kulasu shine suka tare min hanya da kyar wani bawan Allah ya shiga tsakanin mu suka barni.shine ma ya kawo ni har kofar gida dan karsu kara biyoni”.

Umma tana tafa hannu tare da salati tace ” kema Amira ba kya ji bance ki daina bin wannan layin ba,kuma daga yau kar in kara jin kin shiga motan wani dan duniyan nan yanzu ta zama abin tsoro”.

” kiyi hak’uri Umma insha Allah zan kiyaye”.Amira tace cikin maraicewa.

“Allah ya tsare gaba” Umma tace tare da cigaba da aikinta.

D’akinsu Amira ta shiga dan cire uniform,k’anwarta Fateema ta taso cikin sauri tace ” tab  Ameera ashe yau kin auni arziki”.

Murmushi Ameera tayi ” hmmm sis bari kawai da Allah bai kawo mutumin nan ba da ban san wani  hali zan kasance ba”.

Allah ya kiyaye  fateema tayi mata ta amsa tare da d’aukan buta zuwa toilet.

Mallam yawale shine maifin Ameera,da mahaifarsu Hadiza wacce suje kira da Umma dukkan su cikakkun ‘yan Kaduna ne.

Malam Yawale talakane bashi da komai illa gidan da yake ciki,shima gada yayi a wajan mahaifinsu shi k’anwarsa basira.itama tana aure a nan cikin garin kaduna da ‘ya’yanta.

Mallam Yawale ya kasance masani ne shi ta fannin adsinin islam dan yayi saukan alqur’ani tun yana shekara sha bakwai a duniya sannan yayi karatun litattafai da dama,dan haka kullum kullum kofar gidan shi cike yake da masu d’aukan karatu manya da kanana.

Malam ya bawa ‘yan matansa ilimi na boko da arabi ga kuma tarbiya da ya basu,kowa yana sha’awar su a anguwan su.

Al’ameen kuwa yana tafiya cikin motan shi zuwa gida amma hankalin shi gaba d’aya yana kan yarinyan da ya gani domin shi asalima yana son mace kamila gata tayi shigan mutunci wanda matan aure ma da dama basayi suna fito da tsaraicinsu a ganin su wayewa ce amma kuma b’atace babba Allah ka shirye mu baki d’aya ameen.

Da irin tune-tunen nan ya isa gida,sallama yayi ya shigo waiting palour,cikin ikon Allah yau ba taron mutane da ya saba gani kuma hakan ya d’anji sanyi a ranshi.

Kai tsaye main palour ya shiga ya samu Latifa da k’annenta suna kallo,tashi tayi cikin fara’a ta tare shi.sannu da zuwa k’annenta suka mishi sannan suka wuce part d’in su.

Bayan yayi wanka ya fito sanye da jallabiya fari kal,dinning ya wuce cikin jagorancin Latifa yaci abinci sannan suka dawo palour suka zaune kallo.

Suna cikin kallo Latifa ta tashi ta shiga part d’inta,jimawa kad’an ta fito da wasu files a hannunta ta zauna kusa dashi.

Mik’o mishi tayi tace ” gashi yi signing a nan” 

Karb’a yayi yana jujjuyawa yace ” what for?”

Kin kula shi tayi ta cigaba da kallonta hankali kwance.

Ganin haka yasa  ya bud’e ya fara karantawa……

“Ai ba sai ka karanta ba, taimako nake sonyi kasan ‘ya’yanGwaggona na can garin mu basuda aikin yi shiyasa”.

Kallonta kawai yake yandatak koro bayani tare da maimaita a ranshi 50 millions!!!.kuttt toh wai wani tsawon lokaci ta d’auka tana cutansa?coz da alamu ba yau ta fara ba.

Murmushin takaici ya mata yace ” good my Lateefa,taimako abune mai kyau amma ki bari zan samu contract na 100 millions next month sai in baki kinga sai kiyi yanda kike so kin huta da kad’an-kad’an daga nan ki taimakawa duk wanda kika ga yana bukatan taimako”.

Washe baki tayi cikin murna tace ” gaskiyane my Ameen hakan yayi min sosai zan jira zuwa next month d’in”.

Tashi tayi cikin sauri tayi hanyan part d’inta.

Shi kuma kallon takaici ya.bita.dashi a ranshi yana aiyana matakin da ya kamata ya d’auka a kanta kamin next month d’in.daga nan shima ya mik’e zuwa part d’insa.

Kallon system d’in shi yake kaman mai neman wani abu amma a zahiri a shi yake kallo ba yarinyan d’azun yake tunani kuma ba abunda yake so kaman kallon fuskan yarinyan.

Rufe system d’in yayi ganin ya kasa tab’uka komai,kwanciya yayi flat akan gadon shi yana wasi-wasi  yaushe rabon da ya kalli mace a matsayinta na mace har ya manta amma yau yar yarinya k’arama da ko fuskanta bai kalla ba bare ya san sunanta ta hana shi bacci.

Daga baya ya yanke hukunci gobe zai koma gidansu ya tambayi koda sunan tane.

[3/24, 6:47 AM] Ummee Yusuf: . ????‍♀????‍♀????‍♀????‍♀????‍♀????‍♀

  *~UKUBAR KISHIYATA~*

????????????????????????

  ( its all about love and betrayal)

Story by *~UMMEE YUSUF~*

   (Maman Yusuf)

✍✍✍✍✍✍✍

GOLDEN PEN WRITER’S ASSOCIATION

✍✍✍✍✍✍✍

*~part ten~*

Da washe gari Al’ameen da wuri ya shirya ya fito cikin wani shadda light blue wanda ya k’ara fito da k’yansa.

Ko kallon dining area da yake cike da kayan break fast baiyi ba yayi ficewarsa.saboda ya matsu ya kalli fuskan yaruyan nan dan jiya ko baccin kirki bai samu ba.

Latifa kuwa ko tashi ba tayi ba daga bacci.

Musa driver yana ganin fitowan shi ya taso cikin sauri ya bud’e mishi owner seat ya shiga ya zauna.

Duk’awa yayi ya gaishe shi sannan shima ya bud’e driver seat ya shiga ya zauna tare da yiwa motan key suka fita a gidan.

Al’ameen ne yace ” ammm musa mu fara zuwa tudun wada kafin mu wuce office”.

” toh ranka ya dade” musa yace cikin girmamawa.

Nuna mishi hanya ya fara har suka iso k’ofar gidan mallam Yawale,nan yace mishi ya tsaya anan

Brick Musa yaja ya tsaya tare da mamakin meye mai gidansa zaiyina wannan rugujajjen gidan.

Fitowa Al’ameen yayi daga cikin motan ya jingina da jikin motan yana kallon gidan.

Ganin haka yasa Musa daga motan shima ko akwai wani abinda zaiyiwa mai gidan nashi.

Shi kuwa Al’amewn tunani yake ya zaiyi yaga yarinyan da ko sunanta bai sani ba.

Wani almajiri ya gani ya fito daga cikin gidan da k’wanon baran shi a hannu,

kiran shi Al’ameen yayi,nan ya taho da gudun shi.

Al’ameen yace ” kasan mutanen cikin gidan nan ne?”

” a’a nima bara na shiga yi kuma ban samu komai ba” almajirin ya amsa mishi.

“Da ka shiga kaga wata yarinya a cikin gidan ” Al’ameen ya kara jeho mishi tambaya.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button