UKUBAR KISHIYATA 1-END

UKUBAR KISHIYATA Page 11 to 20

“Ameen ameen a ina yarinyan take ne?”Alhaji ya tambaya.

“A can tudun wada take ‘yar gidan Mallam Yawale “.

” toh masha Allah zan sa a min bincike akanta gudun fad’awa gidan jiya,in har ba’a samu zamu je bayan k’wana 2″.

Hajiya ta gyra zama tace” Al’ameen abinda nake so da kai kar ka kuskura matarka taji labarin nan kasan halinta ba abinda ba zata iya aikatawa ba,saboda haka k rufe maganan har saikomai ya kammala sai ka gaya mata”.

Cikin gamsuwa da maganan Hajiyarsa Al’ameen yayi godiya sannan ya musu sallama da sunan zuwa office office ya wuce. 

A wani babban shopping mall Al’a.een ya tsaya ya saya mata waya iphone 7 pink colour,ya had’a da kayan ciye-ciye yayi hanyan gidan su Amira.

Parking yana neman d’an aiken da zai tura dan kira mishi ita.

Cikin sa’a yaga wata yarinya da tallan awara akanta.

Ba b’ata lokaci ya kirata tazo da gudunta ta ganin mai mota zai sayi awaranta.

“Na nawa zan baka”ta tambaya cike da jin dad’i.

Dariya yayi yace mata ” na nawa ne a ciki?”

” na 350 ne “ta amsa cikin gaggawa.

500 ya mik’a mata yace taje tayi sadaka kuma ta shiga gidan can ta k’ira mishi Ameera.

Karb’an kud’in tayi sannan ta ajiye roban ta ruga da gudu zuwa cikin gidan tayi sallama.

Fateema ce a tsakar gidan tana wanke-wanke ta amsa mata.

” wai wani mai mota yana kiran Ameera” tace tana haki.

” mai mota kuma” Fateema ta tambaya”

Kamin ta amsa Umma ta lek’o a dak’i tace ” je ki gani mana ko yaron nan ne ?”

Da sauri ta tashi tayi hanyan fita bayan ta zura hijabinta.

“Tana zuwa akace kuma banida cangi dan banyi ciniki ba tun d’azu na fito”.

Kallon tausayi yayiwa yarinyan yace ” jeki abinki ngode “.

Da murna ta d’auki robanta ta tafi.

Fateema tana lek’owa zaure suka had’a ido dashi murmushi tayi ta koma cikin gida da sauri.

“Umma shine yazo”

“Toh d’auki tabarma ki kai mishi zaure bai kamata su tsaya a waje ba yanzu tunda Abbanku ya amince dashi”.Umma tace mata.

Tabarman ta d’auka ta fita zauren dashi ta shimfid’a sannan ta fita zuwa insa yake tsaye.

Sallama tayi mishi ya amsa yana tambayanta mutanen gida.

Amsawa tayi da lafiya sannan ta.mishi iso cikin zaure.

Gaba tayi ya biyo bayanta har cikin zauren nan ya zauna kan tabarman ita kuma tayi cikin gida.

D’akinsu ta shiga ta tarar da Ameera tana k’wance ta lumshe ido kaman mai bacci sai da a zahiri ba baccin take ba tana dai tunanin ya zatayi in ta fita wajan shi dan bata tab’a tsayawa da wani namiji da sunan zance ba.

Tashinta Fateema ta farayi ta bud’e ido tana kallon Fateema tace “lafiya ina baccina zaki tashe ni?”

” sis nasan fa ba bacci kike ba u re just pretending tashi mai sonki yazo yana jiranki”.

” nifa Fateema bansan ya zanyi ba in na fita nifa kunya nake ji “tace kaman tayi kuka.

” kunya?haba sis sai kace a zamanin su Umma kike?tashi kiyi light make up kije dont keep him waiting”.

Kamin ta bata amsa Umma ta d’aga labulen d’akin tace ” zaman me kike Ameera tundazu kin bar bak’o yana jiranki?tashi ki wuce bana son shashanci”.

Tashi tayi tana tura baki tasa wani white long hijab d’inta sannan ta nufi zauren.

Tundaga bakin zauren take jin fitinannen kamshin turaren yana tashi sallama tayi mishi da sweet voice d’inta,amsawa yayi yana kallonta da murmushi akan fuskan shi.can gefe nesa dashi ta samu waje ta zauna kanta a k’asa.

Jin idanun shi akanta yasa ta d’ago suka had’a ido turo baki tayi tare da kallon gefe dan ta tsani yawan kallo.

” ina wuni “tace ba tare da ta kalle shi ba.

Kallonta kawai yake cikin shauk’in sinta dan turo bakin nan da tayi saida ya.jefa shi wani hali da k’yar ya tattaro natsuwa yace” rik’e gaisuwarki dan bazan amsa.ba,haba prety haka ake gaisuwa?” 

Satan kallon shi tayi ta gefen ido taga har yanzu idon shi akanta,kara turo bakin tayi cikin ranta ta mitan yana bata kunya.cike da shagwab’a tace ” toh ya akeyi ?”

Ya Salam yace a ranshi dan yanda yarinyan take sashi rasa natsuwa.

Mik’ewa yayi ta ajiye shopping bag d’in a gabanta yace toh shi kenan tunda na lura kunyata kike ji ga waya nan a ciki ki sakata a charge zan kira ki anjima maybe zaki fi sakewamu gaisa sosai ta wayan”.

Tana nan zaune ya juya yace ” saina kira prety na wuce office”.

Har yasa kai zai fita yaji muryanta a bayan shi tace ” nagode Allah ya kiyaye”.

Juyowa yayi ya fasa fitan yana kallonta saboda yanda yaji dad’in addu’an data mishi har cikin ranshi dan duk tsawon zaman shi da Lateefa bata tab’a mishi addu’a dan yayi mata wani abu ko dan zai fita ba.amma yau gashi ‘yar k’aramar yarinya tayi mishi nan yaji ta k’ara samun waje na musamman a zuciyar shi.

” Ameen prety nima nagode ” yace sannan yasa kai ya fice.

[3/24, 6:47 AM] Ummee Yusuf: . ????‍♀????‍♀????‍♀????‍♀????‍♀????‍♀

  *~UKUBAR KISHIYATA~*

????????????????????????

  ( its all about love and betrayal)

Story by *~UMMEE YUSUF~*

   (Maman Yusuf)

✍✍✍✍✍✍✍

GOLDEN PEN WRITER’S ASSOCIATION

✍✍✍✍✍✍✍

*~part thirteen~*

Saida taga fitan shi sannan ta tashi tare da nannad’e tabarman ta shiga cikin gida bakinta d’auke da sallama.

Jingine tabarman tayi a jikin bango sannan tazo ta mik’awa Umma shopping bag d’in a hannunta.

” shi baya gajiya da hidimane?” Umma tace lokacin da take bud’e bag d’in.

Ihu Fateema tayi had’e da salle sai gata a gaban Umma ,cikin tsananin murna take magana ” lah sis iphone 7 nefa”.

Harara Umma ta banka mata tace ” ke ko Fateema ba zaki natsu bako?”

Komawa tayi ta zauna tana “kiyi hak’uri Umma na daina”.

Mik’awa Ameera ledan wayan Umma tayi,aiko kamin ta karb’a har Fateema ta rigata.

Rik’e baki Umma tayi ta bita da ido tana “Allah ya shirya min ke Fateema”.

” Ameeeen Ummana” ta amsa daga ciki tana dariya.

Kiranta Umma ta k’arayi ta basu kayan ciye-ciye da Al’ameen ya kawo.

Zama sukayi dirshan a d’aki suna cin kayan ciye-ciyen Fateema tana taya ta oprating wayan dan duk gidan basu da waya sai Abbansu da yake da k’aramar tecno.

 Fateema ta fita sanin kan waya dan tana karb’an na frnds d’inta a school.tsab’anin Ameera bata da karambani shiyasa bata wani iya kan waya sosai ba balle wannan mai tsadan.

Saida sukayi mai isarsu sannan ta jona ta a charging suka fito tsakar gida dan taya Umma aiki.

Kusan 11pm Ameera ta kasa bacci sai latse-latsen wayarta take.

Wani irin zabura tayi jin ringing d’in wayan saura kiris ya tsub’uce a hannunta.

Tsayawa tayi tana kallo kaman ba karta d’auka.

Saida ya kusan tsinkewa sannan ta d’aga cikin sanyin muryarta tace ” Assalamu alaikum”.

Wani irin sanyine ya ziyarci shi wanda ya haddasa mishi sauke ajiyan zuciya har tana jiwo shi ta cikin wayan.

“Wa alaikis salam my prety,me kike yi har yanzu bakiyi bacci ba?”

” na fara bacci ringing wayan ya tashe ni ”

A rud’e yace ” Ya Salam i’m soo sorry pls ki koma baccinki kinji?”

Dariyama ya bata ganing yanda ya wani rud’e dan tace tana bacci ne ya tashe ta.

 Jikin shine ya mutu murus jin dariyarta kunnen shi,how he wish a gaban shi tayi baisan halin da zai shiga ba bcos yarinyan nan komai nata daban yake.

Shi baisan wani irin so yakewa yarinyan nan ba dan abinda yake ji akanta bai tab’a jin ko quatern haka akan matar shi Lateefa ba balle wata macen.

“Wasa fa nake maka banyi bacci ba ” ya sake jin muryanta ta katse mishi zancen zuci da yake.”keko hmmmmm’ ina Fateema?”

“Gata nan tana bacci”ta bashi amsa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button