UKUBAR KISHIYATA Page 11 to 20

“Ameera….”ya k’irata da wani irin murya da baisan yana da ita ba.
Da k’yar Ameera ta iya amsawa da ummm dan bakin ta yayi mata nauyi jin yanda ya kira sunanta for d first time kuma in a in a special way.
“Bansan ta ina zan fara ba prety but all i knw is dat i totaly fall 4 u since d day met.shiyasa na kasa hak’uri har nazo wajan Abba da fargaban ko anyi miki miji,sai dai Alhamdullilah Abba ta tabbatar min da bai bada ke.so its only me in d field kenan?”
Shiru tayi mishi ba tare da tayi magana ba,but murmushine k’wance a fuskanta.
” y re u silent prety bani amsa mana ko sai nazo da kaina zaki bani amsan?”
A hankali ta bashi amsa da ” eh”.
” ok gani nan zuwa yanzu”.
Cikin sauri ta katse shi da cewa ” kasan karfe nawa ne yanzu?”
” koma karfe nawa ne i don’t care dole inzo inji amsata bcos i can’t wait till morning dan kona k’wanta bazan iya bacci ba”.
‘Yar dariya tayi tace ” yi hak’uri ba sai kazo ba”.
“Then” yace yana d’aga gira 1 kaman yana gabanta.
Still shiru tayi tana murmushi.
Canza topic d’in yayi na yanda zata saki jiki suyi hira.
” kina j.s.s 2 ko 3 a secondry school?”
Dariya tayi.dan tambayan dariya y ya bata
“Oh na d’ebo dayawa ko”
” na gama dis year ko Fateema tana s.s 2″.ta bashi amsa tana dariya.
” woah ashe da babban yarinya nake magana wat abt islamiya?”ya kara jeho mata da tambaya.
” hmmm mun kusa had’a haddan mu ”
” afuwan yaah mu’allima” yace yana sassauta murya.
Nan ma dariya ta rink’ayi,kaman wasa sai gashi cikin dabara ya sa ta saki jiki suka sha hiran su har kusan 1:30am sannan ya hak’ura ya k’yaleta dan tayi bacci ba dan ya gaji ba.
Yana ajiye wayan ya kalli wall clock dake manne a jikin bangon d’akin,tsiririn tsaki yaja a ranshi yana mita kana da mata amma ba kada maraba da gauro.
Ameera sai juyi take tana murmushi ita kad’ai ta kasa bacci sai wani nishad’i take a ranta tana mamakin dama haka so yake?da k’yar ta samu bacci ya d’auke .
After 2 days Alhaji Mudassir ya samu duk wani information da yake son ya samu akan Ameera kuma ya gamsu sosa dan haka ba b’ata lokaci ya k’ira Al’ameen yace ya sanar da ita zasu je gidansu gobe da yamma.
Cikin tsananin farinciki ya k’ira ta a lokacin suna d’aki ita da Fateema tana tayata drawing d’in heart da aka basu assignment a makaranta.
Murmushine ya sub’uce mata ganin kiran hrt beat d’inta dan yanzu ta sake dashi suna shan hiran su yanda ya kamata amma fa a waya.
D’agawa tayi tare da sallama,amsawa yayi cikke da nishad’i dan ji yake kaman har an d’aura auren.
“Guess wat”
” i’m not gud at guessing just fad’a min nima in taya ka farinciki da alama abin farinciki ne ya samu” ta bashi amsa.
“Hakane kince u re nit gud at guessing but gashi kuwa har kinyi”.
“Hmmmm ta muryarka na gane kana cikin nishad’i yau”.
“Ba kad’an ba kuwa ki sanar da Abba gobe Alhajina zasu zo gidanku”.
Sassauta murya ya k’arayi yace sunga na fara zaucewa akanki shi zasu taimaka su kawo min ke dan kar in ida zauc……”.
Katse wayar tayi tana murmushi dan wani lokacin kunya yake bata.
Zungure ta Fateema tayi ta juyo da sauri suka sa dariya.
” kin fad’a dayawa sis ” Fatema tace tana dariya.
” Fateema kenan ba zaki gane ba a yanzu har sai kema Allah ya had’aki da real love d’inki,kinga yanzu je ki fad’awa Umma yace gobe Alhajin shi zasu zo wajan Abba”.
Cikin tsananin murna Fateema ta rungumeta sannan.ta sake ta ta fita da.gudu zuwa tsakar gida tana kiran Umma.
Fitowa Umma tayi daga d’aki har tana tuntub’e saboda rud’ewa.
Clashing tayi da Fateema tana washe baki,cikin fad’a Umma ta fara mata fad’a.
Hak’uri ta bata tare da fad’a mata sakon Al’ameen.
” Allah sarki ameera ita kunya ya hanata fad’a sai ke ko uwar rawan kai”.
Komawa tayi daki tana dariya.
Alhaji sun cika alkawari sun zo neman auren d’an autan shi tare da jama’rshi.
Sun samu tarba mai k’yau wajan mallam Yawale da mutanen shi.nan akasa sa ranan aure 3weeks kacal bisa umarnin Al’ameen.
Mallam Yawale yaso a k’ara mishi lokaci saboda yanayin rayuwa amma Alhaji mudassir yace su basa bukatan komai daga gare shi dan su .ata suka nema kuma an basu shikenan.
Nan taro ya watse kowa cike da farinciki more especially Al’ameen da yake jk kaman ya zuba ruwa a k’asa ya sha.
[3/24, 6:47 AM] Ummee Yusuf: . ????♀????♀????♀????♀????♀????♀
*~UKUBAR KISHIYATA~*
????????????????????????
( its all about love and betrayal)
Story by *~UMMEE YUSUF~*
(Maman Yusuf)
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION????????????~*
*~❄We beare’s of soon golden We writer’s assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*
*~part fourteen~*
Lateefa tana can tana budurinta hankali k’wance bata san wainar da ake toyawa ba dan ko kad’an Al’ameen bai nuna mata wata alama ba.
Ana saura 2weeks biki,aka kawo kayan lefe na gani na fad’a.akwati set 2 masu k’yau da tsada kuma fad’an kayan cikin b’ata lokaci ne.
‘Yan uwan Abba da Umma abin ya basu mamaki dan basu tab’a ganin lefe haka ba.
A wannan lokacin kuma wani irin soyayya da shak’uwace ta shiga tsakanin Ameera da Al’ameen dan kullum sai yazo da safe ya ganta before ya wuce office,haka ma da yamma sai yazo sun sha hiransu sannan zai wuce gida.
At night ma suna manne a waya sai sun kusan raba dare suna yi sai dai in Lateefa ta shigo ne ba zasuyi ba.
Ana saura 1 week biki Al’ameen ya har ya gama gyara gida duk da gidan da k’yansa amma hakan bai hana shi yiba more especially part d’in amarya yafi ko ina shan gyara.
Tun ana saura 2 weeks musamman yayi ordern kayan funutres daga italy kayan kitchen kuma daga dubai.
Ameera amarya itama tasha gyara ciki da waje dan kullum Umma cikin yi mata d’ure-d’ure take.
‘Yar gwaggonta basira kuma itace ta d’auki nauyin gyaran fata da kamshin jiki,cikin lokaci kad’an ta canza fatanta yayi wani irin k’yau abinka da farin fata har wani shek’i taje ga kamshi da jikinta yake na musamman.
Duk irin gyaran da ake a gidanta Lateefa bata kawo komai a ranta ba saboda tasan abinda ta taka.
Ana saura 1 week kayan da Al’ameen yayi oder suka iso.
Lateefa da k’annenta suna zaune a palour suna hira suka ga aka fara shigowa da kaya nik’i-nik’i.
Cikin tashin hankali Fa’iza tace ” Aunty wai meye yake faruwa ne naga anata shigowa da kaya ?”
Shamsiya tayi carab tace ” ko dai Ya Al’ameen ne zaiyi aure?”
Zabura Lateefa tayi daga kishingid’en da take tare da yayimo wata uwar ashar ta d’ura sannan tace ” ke daina irin wannan maganan a cikin gidan nan,yama isa yace zaiyi aure a gidan nan”.
Fa’iza ta girgiza kai tace ” Aunty maganan Shamsiya fa abin dubawa ne,ki tuna how many days akayi ana gyara a gidan nan ga kuma kayan da yanzu ake shigowa dasu ma sun isa shaida”.
Jiki a sanyaye take binsu da kallo can tace ” amma fa kunsa jikina yayi sanyi but bari ya dawo ya same ni,wallahi in dai da gaske auren zaiyi wallahi Allah ya d’ebo ruwan dafa kanshi.
nan fa suka rinka masifa ita da k’annenta kaman zasu ari baki.
5pm dai dai Al’ameen ya dawo gida bayan ya biya wajan Ameeransa suka sha hiransu,dan haka ran shi fari kal ya shigo gidan rik’e da brief case d’inshi.
Sallama yayi ya shigo su Fa’iza ne kad’ai suka amsa sallaman banda Latifa da sai cika take tana batsewa ga wata uwar harara da take wurga mishi.