UKUBAR KISHIYATA Page 11 to 20

Ko kulata baiyi ba ya wuce up stairs abinshi.
Da saurinta ta tashi tabi shi part d’inshi.
Jikinta har rawa yake saboda tsabar masufa da yake cinta.
Banko k’ofanta tayi da karfin gaske wanda har yasa shi d’an razana.
A fusace yace ” meye hakane Lateefa,wani irin rashin hankali ne wannan?”
” eh lalle Al’ameen dole kace banida hankali,meye nufinka na gyara wancan part d’in harda canza kayan da suke ciki?” tace tana huci.
” aure zanyi ” yace a takaice a lokacin da ya nufi hanyan bathroom.
Da gudu Lateefa tasha gaban shi ” what did u jst saida,aure or wat?”
” eh ko haramun ne?” ya jeho mata tambaya yanakallon cikin idonta.
K’walan shi taci a masifance tace ” wallahi baka isa ba ni kake gayawa zakayi aure?
Fizge hannunta yayi daga jikin rigan shi ya shige bathroom ya barta a tsaye sai huci take kaman maciji.
Da gudu ta fito tayi part d’inta wayanta ta d’auka ta fara dialing number Aina’u.
Ringing 2kawai yayi Aina’u tayi recieving tana ” Hajiya ya akayi ne?”
” Aina’u ba lafiya”tace murya na rawa.
” Subhanallah meya far najiki haka?”
“Komai ya warware Aina’u wai yau ni Al’ameen yake cewa zaiyi aure?”
A kid’ime Aina’u tace ” uban shima yayi kad’an,shi Al’ameen d’in ne har ya bud’i ya gaya miki zaiyi aure?”
“duk yanda za’ayi gobe kizo muje wajan boka dan insan halin da nake ciki.dan Allah kizo da wuri Aina’u kinji?”tace cikin marairaicewa.
Cikin rarrashi Aina’u tace ” karki damu besty zan zo da wuri ai bamu gata zama ba dole mu koma ki k’wantar da hankalinki kema ai kin san aikin boka kaman kaifin wuk’a yake”.
Sai alokacin ta samu sauk’e wani ajiyan zuciya dan ta san tabbas aikin boka ba wasa nan tace ” shikenan sai kin zo goben”.
10am a gidan Lateefa yayiwa Aina’u.
Lateefa dama tun 8 ta gama shiryawa ta zauna jiran Aina’u yau ba baccin safe.
Ba b’ata lokaci suka kama hanya zuwa wajan boka.
Suna isowa wajan boka tun kamin suyi mishi bayani ya daka musu tsawa yace ” auren nan ba makawa sai anyi shi,sai dai zan taimaka miki ya zamti ta zama hoto a gidan balle ta kai gahaihuwa da kike tsoro.karki damu ki k’wantar da hankalinki in anyi auran da wata 1 sai ki dawo komai zai tafi dai-dai kaman yanda kike buk’ata”.
Zuciyar Lateefa ta d’anyi sanyi akan bayanan boka,sai dai bata so ace anyi auren ba amma Aina’u tayi warning d’inta tun farko akan cewa ba ‘yi mishi musu dan haka ta tsuke bakinta tayi shiru badan taso ba.
Kud’i suka kawo mai yawa suka bashi tare da yi mishi sallama suka fita.
Akan hanyarsu ta dawowa Lateefa tace ” Aina’u inba dan kin hanani yiwa bokan nan musu ba,gaskiya banso ayi auren nan ba.saboda a ganina in an d’aura komai zai iya faruwa”.
” besty some time ki n cika surutu,ki hak’ura mana tunda yace komai zai tafi dai-dai kaman yanda kik so.kinsan akwai wata k’awar k’wata datavtab’a yiwa boka musu,,hmmmm kinga abinda ya same ta?”
A d’an tsorace Lateefa ta juyo ta tambaya ” meya same ta besty?”
“Hmmm wallahi sai data zama kare ya fita daraja,ta zama abin k’tama cikin mutane.ke in short uwarta ma saida ta guje ta saboda wasu kuraje da suka fito mata duk jikinta ga wani da take,hankalunta ma saida ya zama ba dai-dai ba”.
Wani irin yawu Lateefa ta had’iye tare da cewa ” kice nayi babban sa’a”.
” offcourse yes sai ki kiyaye sosai”.
A haka suka iso gida,Aina’u itama ta wuce gidansu bayan Lateefa tayi mata sha tara na arziki kaman yanda ta saba.
Yau saturday kuma a yaune duban jama ‘a suka shaida d’aurin auren Al’ameen da amaryan shi Ameera .
Toh koya zaman nasu zai kasance?
[3/24, 6:47 AM] Ummee Yusuf: https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
????♀????♀????♀????♀????♀????♀
*~UKUBAR KISHIYATA~*
????????????????????????
(Its all about love and betrayal)
Story by *~UMMEE YUSUF~*
(Maman yusuf)
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION????????????~*
*~❄We beare’s of soon golden We writer’s assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen xBe hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*
*~part fifteen ~*
Al’ameen bakin shi yaki rufuwa saboda farinciki,yanda yake rawan kai sai ka zaci auren na farko ne wannan.
Bangaren amarya ameera ma hakan take tana can cikin ‘yan tsiraru frnds d’inta na makaranta sai cousin sisters d’inta da suka zazzo sai shewa ke tashi a d’akin da suke taro.
Lateefa kuwa tunda suka dawo daga wajan boka hankalinta ya gaza k’wanciya,more especially yau.dan tunda ta tashi gabanta yake ta fad’uwa saboda haka take kunshe a can cikin bedroom d’inta ko palour ta kasa fitowa.
Amarya tasha nasihohi daga wajan Ummanta da Abbanta kan zamanta kewar aure tsakanin ta da mijinta da abokiyar zamanta,sai kuka take kaman ranta ya fita.
Da aka zo fita da ita da k’yar aka b’anb’areta daga jikin Fateema aka sata a mota.nan abokanen ango suke sanar da ‘yan matan akwai dinner da za’ayi before akai amarya gidanta.
Nan ‘yan mata suka hau shiri ciikin farinciki.
Ameera sai kuka take a cikin mota ji take a cikin ranta zata ta hak’ura da auren,ta koma ga Ummanta.
Ido kawai ya zuba mata yana kallon yanda take kukan kuma ga dukkan alamu bata san yana cikin motan ba.
Hannu ya kai ya kamo hannunta na dama,a firgice ta juyo ganin angonta ne yasa ta k’ara sautin kukanta.
Jawo ta yayi ya rungume yana sauk’e ajiyar heart saboda kullum suka had’u ba k’aramin yaki da zuciyar shi yake wajan kar ya tab’ata ba.
Mutsu mutsu ta fara nason k’wace kanta amma ta kasa.
D’ago kai tayi suka had’a ido ko wannensu ido ya canza yayi jawur dashi Ameera nata na kukan da tasha ne Al’ameen kuma na tsaban fitina ce.
Kallon d’an k’aramin lips d’inta da yake bala’in k’wad’ayi yake,ganin tak’i barin kukan yasa ya had’e bakinsu ya kama tsotsa kaman ya cire su.
Motance ta tsaya a bakin wani lafiyayen beauty saloon amma Al’ameen gaba daya baisan ma inda suke ba har ya fara fita hayyacin shi.
Gyaran murya da bilal abokin shi yayi shi ya dawo dashi hayyacin shi ya tuna ashe fa a mota suke kuma basu kad’ai bane.
Da k’yar ya sake ta yana maida numfashi tare da zuba mata ido yana murmushi,wasu special feelings yake ji akan yariyan nan shi kan shi bai san adadin son da yake mata ba.
Ameera kuwa wannan abinda ya faru tsakanin su yasa wani irin kunyar shi ta gama rufeta sai sunne kai take tana blushing dan tunda take hakan bai tab’a faruwa da ita ba.
Leken fuskanta yake yana murmushi yace ” woah my prety bride ashe dama kukan bana gaske bane na in…….. ko?
Bata san lokacin da ta zaro ido waje tana kallon shi jin wannan sharrin da ya mata.
Dariya Al’ameen ya k’yalk’yale dashi tare da hure mata ido yace ” haba mana prety ko irin kunyan nan na amare babu kika tsare ango da ido haka?”
Rasa abinyi tayi ganin kome tayi sai ya musu negetive fassara.
Shi kuma he was enjoying every part of the time they spend together but na yau is diffrent ji yake kaman su dawwama haka just d 2 of them.
Gyara mata lullubi yayi shima ya gyara rigan shi sannan ya bud’e motan suka fito zuwa cikin saloon d’in.
Nan ya barta bayan yayi musu bayanin to do there very best amarya ce,sannan suka wuce shi da bilal dan suje su shirya kamin a gama mata.
Kasa gane Ameera nayi saboda yanda ta canza completely cikin wani material golden colour ga havy make up data sha.kanta yasha gyara amma an yafa mata wani hadadden net a kai,poss da high hills duk white tayi bala’in k’yau ta fito a amaryarta sak.